Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah Yana Karfafa Mu Sa’ad da Muke Cikin Matsala

Jehobah Yana Karfafa Mu Sa’ad da Muke Cikin Matsala

“Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.”​—2 KOR. 1:​3, 4.

WAƘOƘI: 38, 56

1, 2. Ta yaya Jehobah yake ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar matsaloli, kuma wane tabbaci ne ya ba mu a cikin Kalmarsa?

WANI matashi yana tunani a kan abin da aka faɗa a littafin 1 Korintiyawa 7:28 cewa: Waɗanda suka yi aure “za su sha wahala a cikin jiki.” Sai ya tambayi Stephen wani dattijo magidanci: “Mece ce wannan ‘wahalar,’ kuma yaya zan bi da ita idan na yi aure?” Kafin Stephen ya amsa wannan tambayar, sai ya gaya wa matashin ya bincika wani abu da manzo Bulus ya rubuta cewa Jehobah ne “Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.”​—2 Kor. 1:​3, 4.

2 Hakika, Jehobah Uba ne mai ƙauna kuma yana ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Wataƙila Allah ya taimaka maka kuma ya ja-gorance ka ta wurin Kalmarsa. Muna da tabbaci cewa yana son ya taimaka mana kamar yadda ya yi wa bayinsa a dā.​—Karanta Irmiya 29:​11, 12.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

3 Za mu iya jimre matsalolin da muke fuskanta idan muka gano dalilan da suka sa muke shan wahala. Kuma hakan yake da wahalar da ma’aurata suke fuskanta. To, waɗanne abubuwa ne za su iya jawo ‘wahala a cikin jiki’ da Bulus ya ambata? Waɗanne misalai na dā da kuma na zamaninmu ne za su iya ƙarfafa mu? Idan muka bincika amsoshin waɗannan tambayoyin, za mu san abubuwan da za mu yi don mu jimre sa’ad da muke shan wahala.

WAHALAR DA MA’AURATA SUKE SHA

4, 5. Waɗanne abubuwa ne suke jawo “wahala” a aure?

4 Sa’ad da Allah ya halicci mutane kuma yake ɗaura aure na farko, ya ce: ‘Mutum za ya rabu da ubansa da uwarsa, ya manne wa matarsa, za su zama nama ɗaya kuma.’ (Far. 2:24) Duk da haka, da yake mu ajizai ne, idan muka yi aure kuma muka sami iyali, muna iya fuskantar matsaloli sosai. (Rom. 3:23) Alal misali, yarinya takan yi wa iyayenta biyayya idan ba ta yi aure ba. Amma Allah ya ce idan ta yi aure, miji ne zai zama shugabanta, shi ya sa ya kamata ta bi ja-gorancin mijinta maimakon iyayenta. (1 Kor. 11:3) Kuma da farko idan mutumi ya yi aure, yi wa matarsa ja-goranci zai yi masa wuya. Haka ma yake da matar, yi wa mijinta biyayya maimakon iyayenta zai iya yi mata wuya. Ƙari ga haka, suna iya samun saɓani da surukai kuma hakan zai iya jawo musu matsala.

5 Ma’aurata sukan yi alhini sosai sa’ad da suka gane cewa za su sami yaro. Ko da yake ma’aurata suna farin ciki game da hakan, amma sukan damu da batutuwan da suka shafi jinya da za su iya tasowa a lokacin haihuwa ko kuma bayan hakan. Ƙari ga haka, sun san za su riƙa kashe kuɗi sosai. Kuma suna bukatar su yi wasu canje-canje sa’ad da aka haifi yaron. Ban da haka ma, yanzu matar za ta riƙa kula da jaririn fiye da mijinta. Shi ya sa maigida zai iya ganin matarsa ba ta kula da shi don ta shagala wajen kula da yaronsu. Kuma yanzu ya sami ƙarin aiki a iyali, don shi ne zai ɗauki nauyin biyan bukatun matar da kuma jaririn.

6-8. Ta yaya rashin haihuwa zai sa ma’aurata damuwa?

6 Wasu ma’aurata suna fuskantar wata matsala dabam. Suna so su haifi yara, amma ba za su iya yin hakan ba. Idan matar ba ta yi juna biyu ba, hakan yana iya sa ta damuwa sosai. Amma aure ko kuma haifan yara ba ya kawar da alhini, duk da haka, idan ma’aurata suna neman yara amma ba su samu ba, hakan yana iya jawo wa ma’aurata “wahala a cikin jiki.” (Mis. 13:12) A zamanin dā, abin kunya ne a ce mace ba ta haihuwa. Rahila matar Yakubu ta yi baƙin ciki sosai don yayarta tana haifan yara amma ita ba ta iya yin hakan ba. (Far. 30:​1, 2) A ƙasar da al’adar mutanen ita ce haifan yara da yawa, ana yawan tambayar masu wa’azi a ƙasashen waje dalilin da ya sa ba su da yara. Duk da bayani da masu wa’azin suke ba su da basira, sukan ce musu, “Kada ku damu, za mu yi muku addu’a!”

7 Alal misali, wata ’yar’uwa a Ingila tana so ta haihu, amma ba ta iya yin hakan ba. Da ta ga ta wuce shekarun haihuwa, ta ce ta yi baƙin ciki sosai. Me ya sa? Don ta gane cewa ba za ta iya haihuwa ba a wannan zamanin. Ita da mijinta suka tsai da shawarar su ɗauki riƙon yaro. Duk da haka, ta ce: “Har ila, nakan yi baƙin ciki, don na san cewa ba ni na haife shi ba.”

8 Littafi Mai Tsarki ya ce mace “za ta tsira ta wurin haifan ya’ya.” (1 Tim. 2:15) Amma hakan ba ya nufin cewa haifan yaro ko kuma samun yara zai sa mutum ya samu rai na har abada. Maimakon haka, yana nufin cewa idan mace tana kula da yara tare da wasu aikace-aikacen gida, hakan zai taimaka mata ta guji yin gulma da saka baki a abin da bai shafe ta ba. (1 Tim. 5:13) Amma duk da haka, tana iya fuskantar wasu matsaloli a aurenta da kuma a iyalinta.

Ta yaya mutum zai jimre da rasuwar abokinsa ko kuma wani a cikin iyali? (Ka duba sakin layi na 9, 12)

9. Ta yaya rasuwar mata ko miji ya fi sa ma’aurata baƙin ciki?

9 Sa’ad da ake magana game da wahala da ke tattare da aure, ba a yawan tunawa da mutuwar aboki ko abokiyar aure. Hakika, rasuwar miji ko mata ne ya fi sa ma’aurata baƙin ciki. Don wannan abu ne da mijin ko matar ba za su yi tsammanin za su fuskanta a wannan zamanin ba. Amma Kiristoci sun gaskata da alkawarin da Yesu ya yi cewa za a ta da waɗanda suka mutu. (Yoh. 5:​28, 29) Ta yaya wannan begen yake taimaka ma waɗanda aka yi musu rasuwa? Kasancewa da begen yana ƙarfafa su sosai. Kuma wannan wata hanya ce da Ubanmu yake amfani da Kalmarsa don ya ƙarfafa da kuma taimaka ma waɗanda suke shan wahala. Bari mu bincika yadda wasu bayin Allah suka ji da kuma amfana daga irin ƙarfafar da Jehobah yake musu.

YADDA AKE ƘARFAFA MU SA’AD DA MUKE SHAN WAHALA

10. Ta yaya Hannatu ta sami ƙarfafa sa’ad da take cikin matsala? (Ka duba hoton da ke shafi na 4.)

10 Hannatu matar Elkanah da yake ƙauna ta fuskanci wata irin matsala, ba ta samu haihuwa ba amma kishiyarta Peninnah tana haihuwa. (Karanta 1 Sama’ila 1:​4-7.) Don haka, kishiyar Hannatu tana mata ba’a kowace “shekara” kuma hakan ya sa Hannatu baƙin ciki da kuma damuwa sosai. Sai ta “jima tana addu’a a gaban Ubangiji,” don ya ƙarfafa ta. Shin tana son Jehobah ya biya mata bukatarta ne? Babu shakka, ta so hakan. Ban da haka ma, “fuskarta ba ta ƙara nuna baƙin ciki ba.” (1 Sam. 1:​12, 17, 18) Me ya sa? Ta gaskata cewa Jehobah zai iya sa ta haihu ko kuma ya ƙarfafa ta.

11. Ta yaya addu’a za ta iya ƙarfafa mu?

11 Saboda mu ajizai ne kuma muna rayuwa a duniyar da Shaiɗan yake mulki, za mu fuskanci matsaloli da kuma wahala. (1 Yoh. 5:19) Amma za mu yi farin ciki idan muka sani cewa Jehobah ‘Allah ne na dukan ta’aziyya’! Hanya ɗaya da za mu iya samun ƙarfafa idan muna cikin matsala ita ce ta wurin yin addu’a. Hannatu ta yi addu’a sosai ga Jehobah. Saboda haka, mu ma idan muna fuskantar matsaloli, muna bukatar mu faɗa wa Jehobah yadda muke ji, kuma mu roƙe shi sosai mu bayyana masa abin da ke zuciyarmu.​—Filib. 4:​6, 7.

12. Me ya taimaka wa gwauruwa Hannatu ta riƙa farin ciki duk da matsalarta?

12 Za mu iya samun ƙarfafa ko da muna baƙin ciki sosai don ba mu haifi yara ba ko kuma don wani da muke ƙauna ya rasu. A zamanin Yesu, mijin annabiya Hannatu ya rasu bayan shekara bakwai da aurensu. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki bai ambata ko suna da yara ba. Shin me Hannatu ta yi duk da cewa shekararta 84 ne? Littafin Luka 2:37 ya ce: “Ba ta rabuwa da haikali, tana sujada tare da azumi da addu’o’i dare da rana.” Hakika, bautar Jehobah da Hannatu take yi ne ya sa ta samu ƙarfafa kuma ta kasance da farin ciki.

13. Ka ba da misalin yadda abokan gaske za su iya ƙarfafa wasu ko da dangin mutumin ba su yi hakan ba.

13 Idan muna yin tarayya da ’yan’uwanmu Kiristoci, za mu sami abokai na gaske. (Mis. 18:24) Wata ’yar’uwar mai suna Paula ta faɗi yadda ta ji sa’ad da take ’yar shekara biyar da mahaifiyarta ta daina bauta wa Jehobah. Samun ƙarfin gwiwa a wannan yanayin bai kasance mata da sauƙi ba. Amma wata ’yar’uwa majagaba mai suna Ann, a ikilisiyarsu ta nuna cewa ta damu da ita kuma hakan ya ƙarfafa ta. Paula ta ce: “Duk da cewa Ann ba dangina ba ce, ta taimaka min sosai in ci gaba da ibada.” Paula ta ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Kuma tana farin ciki domin mahaifiyarta ta dawo kuma suna bauta wa Jehobah tare. Ann ma ta yi farin ciki domin ta zama kamar uwa ga Paula.

14. Wace albarka ce waɗanda suke ƙarfafa mutane suke samu?

14 Idan muka nuna cewa mun damu da wasu, hakan zai taimaka mana mu rage baƙin ciki da muke yi. ’Yan’uwa mata masu aure da marasa aure sun ga cewa suna farin ciki sosai idan suna wa’azi game da Mulkin Allah. Muradinsu shi ne su ɗaukaka Allah ta yin nufinsa. Wasu suna ganin cewa yin wa’azi magani ne. Hakika, dukanmu muna sa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai idan muna ƙaunar waɗanda suke yankinmu da waɗanda suke cikin ikilisiya. (Filib. 2:⁠4) Manzo Bulus ya kafa mana misali mai kyau a wannan batun don ya zama kamar mahaifiya ga ’yan’uwa da ke ikilisiyar Tasalonika. Ƙari ga haka, ya zama kamar mahaifi a gare su don ya koya musu game da Allah.​—Karanta 1 Tasalonikawa 2:​7, 11, 12.

ƘARFAFAR DA MUKE SAMU A IYALI

15. Su waye suke da hakkin koya wa yara game da Jehobah?

15 Wani batu da ya kamata mu yi la’akari da shi shi ne yadda muke ƙarfafa da kuma taimaka wa iyalai. A wani lokaci, ’yan’uwa sukan gaya wa masu shela da suke ibada sosai, su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da yaransu ƙanana. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce koyar da yara hakkin iyaye ne. (Mis. 23:22; Afis. 6:​1-4) Ko da yake a wasu lokatai suna iya neman taimakon wasu ’yan’uwa, duk da haka, iyaye ne ya kamata su koyar da yaransu. Kuma yana da muhimmanci su riƙa tattaunawa sosai da iyalinsu.

16. Mene ne ya kamata mu riƙa tunawa idan muna nazari da yara?

16 Idan iyaye suka tsai da shawara wani ya riƙa nazari da yaransu, bai kamata wanda yake nazari da su ya ɗauki hakkin iyayen ba. A wasu lokatai, ana gaya ma wani Mashaidi ya yi nazari da yaran da iyayensu ba Shaidu ba. Ya kamata Mashaidin ya tuna cewa ko da yake yana nazari da yaran, ba shi ba ne ya haife su. Ƙari ga haka, idan yana nazari da su, zai fi dacewa ya yi hakan a gidansu ko ya tafi tare da wani Mashaidi da ya manyanta ko kuma su yi nazarin a wurin da mutane suke. Don kada wani ya ce suna yin abin da bai dace ba. Ana fatar cewa da shigewar lokaci, iyayen za su cika hakkin da Allah ya ba su na koya wa yaransu game da Jehobah.

17. Ta yaya yara za su iya ƙarfafa iyalansu?

17 Yara ko matasa da suke ƙaunar Allah za su iya ƙarfafa iyalinsu. Ta yaya za su iya yin hakan? Ta wurin yi wa iyayensu biyayya da kuma taimaka musu. Ƙari ga haka, idan yara suka ci gaba da bauta wa Jehobah, hakan zai ƙarfafa dukan iyalin. Kafin rigyawa, Lamek zuriyar Seth ya bauta wa Jehobah. Wannan mutumin ya gaya wa ɗansa Nuhu cewa: “Za ya ta’azantar da mu domin aikinmu da wahalar hannuwanmu, da ya fito daga ƙasa wadda Ubangiji ya la’anta.” Wannan annabcin ya cika sa’ad da Jehobah ya janye la’anan da ya yi wa ƙasar. (Far. 5:29; 8:21) Amma matasa da suka ɗauki bautar Jehobah da muhimmanci za su iya ƙarfafa iyalansu don dukansu su jimre matsalolin da suke fuskanta yanzu kuma su tsira wa abin da ya fi rigyawa.

18. Mene ne zai taimaka mana mu jimre duk da matsalolin da muke fuskanta?

18 Addu’a da kuma bimbini a kan labaran wasu mutane a Littafi Mai Tsarki da kuma tarayya da bayin Jehobah yana ƙarfafa miliyoyin mutane su iya jimre da matsalolin da suke fuskatanta. (Karanta Zabura 145:​18, 19.) Sanin cewa Jehobah yana shirye ya ƙarfafa mu a kowane lokaci zai taimaka mana mu jimre duk wani gwajin da muke fuskanta a yanzu da wanda za mu fuskanta a nan gaba.