Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Da Ya Sami Tagomashin Allah

Da Ya Sami Tagomashin Allah

MUNA bauta wa Jehobah kuma muna son tagomashinsa, ko ba haka ba? Amma wane irin mutum ne Jehobah zai nuna masa tagomashi kuma ya albarkace shi? Akwai wasu mutane da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki da Allah ya amince da su ko da sun taɓa yin zunubi mai tsanani. Amma akwai wasu da suke da halaye masu kyau da Allah bai amince da su ba. Saboda haka, muna iya yin wannan tambayar, “Mene ne Jehobah yake bukata daga kowannenmu?” Labarin wani sarkin Yahuda mai suna Rehobowam zai iya taimaka mana mu san amsar.

BAI BI SHAWARA MAI KYAU BA

Mahaifin Rehobowam shi ne Sulemanu wanda ya yi sarauta shekara 40 a Isra’ila. (1 Sar. 11:42) Sulemanu ya rasu a shekara ta 997 kafin haihuwar Yesu. Bayan haka, sai Rehobowam ya nufi arewa daga Urushalima zuwa birnin Shekem don a naɗa shi sarki. (2 Tar. 10:1) Shin ya ji tsoron zama sarki ne? An san sarki Sulemanu da hikima sosai. Ba da daɗewa ba, Rehobowam zai bukaci ya nuna cewa yana da hikimar magance matsaloli masu wuya.

Babu shakka, Rehobowam ya lura cewa mazaunan ƙasar Isra’ila suna fushi sosai. Ba da daɗewa ba, sai mazaunan ƙasar suka tura wasu mutane zuwa wurin Sarki. Suka ce: “Babanka ya sa mana gungumen da ya danne mu sosai. Yanzu idan ka sauƙaƙa mana ayyukan nan da suka danne mu sosai, da abubuwa masu nauyin da ya saka a kanmu, to, za mu yi maka hidima.”​—2 Tar. 10:​3, 4.

Rehobowam yana da shawara mai wuya da zai tsai da. Idan ya yi abin da mutanen suka ce, shi da iyalinsa za su daina moran wasu abubuwan da suka saba. Amma idan bai yarda ba, mutanen za su iya yin tawaye. Wace shawara ce sarkin zai yanke? Sabon sarkin ya fara neman shawarar maza tsofaffi da suke ba Sulemanu shawara. Bayan haka, ya nemi shawara daga wurin tsararsa. Rehobowam ya bi shawarar tsararsa, kuma ya yanke shawarar wahalar da mutanen. Ya ce: “Zan ƙara danne ku, babana ya dūke ku da bulala, amma ni zan hore ku da bulala mai haƙoran ƙarfe.”​—2 Tar. 10:​6-14.

Akwai darasin da za mu iya koya daga wannan labarin? Ƙwarai kuwa. Yana da kyau mu riƙa bin shawarar Kiristoci da suka daɗe suna bauta wa Jehobah. Da yake sun daɗe suna bauta wa Jehobah, za su iya taimaka mana mu yanke shawara mai kyau.​—Ayu. 12:12.

“SUKA YI BIYAYYA DA MAGANAR YAHWEH”

Sa’ad da Rehobowam ya ga cewa mutanen sun yi tawaye, sai ya shirya sojojinsa don su yaƙe su. Amma Jehobah ya yi amfani da annabi Shemaya wajen yi masa gargaɗi. Ya ce: “Kada ku fāɗa wa ’yan’uwanku Isra’ilawa da yaƙi. Bari kowane mutum ya koma gidansa, gama wannan abu daga wurina ne.”​—1 Sar. 12:​21-24. *

Ya kasance wa Rehobowam da sauƙi kuwa ya yi biyayya ga Jehobah? Yaya mutanen za su ɗauki Rehobowam da ya ce zai hore su da “bulala mai haƙoran ƙarfe” amma yanzu bai ɗauki mataki ba? (Ka gwada da 2 Tarihi 13:7.) Duk da haka, sarkin da sojojinsa sun yi “biyayya da maganar Yahweh, suka koma gidajensu bisa ga umarnin Yahweh.”

Wane darasi ne hakan zai iya koya mana? Ya kamata mu riƙa yin biyayya ga Allah ko da yin hakan zai sa mutane su yi mana ba’a. Yin biyayya ga Jehobah yana sa ya yi mana albarka kuma ya nuna mana tagomashi.​—M. Sha. 28:2.

Shin Jehobah ya albarkaci Rehobowam domin ya yi masa biyayya? Rehobowam ya fasa zuwa yaƙin amma ya mai da hankali wajen gina birane a ƙabilu biyu da ya mallaka, wato Yahuda da Benyamin. Ya ƙara wa birane da yawa “ƙarfi sosai.” (2 Tar. 11:​5-12) Abu mafi muhimmanci shi ne ya ɗan jima yana kiyaye dokokin Jehobah. Sa’ad da mazaunan ƙabilu goma na Isra’ila waɗanda Yerobowam ne sarkinsu suka soma bautar gumaka, da yawa cikin mutanen sun ‘goyi bayan Rehobowam’ ta wajen zuwa yin bauta a Urushalima. (2 Tar. 11:​16, 17) Kiyaye dokokin Jehobah ya kyautata sarautarsa.

REHOBOWAM YA YI ZUNUBI KUMA YA TUBA

Sa’ad da Rehobowam ya yi ƙarfi sosai, ya yi wani abu mai ban mamaki. Ya soma bauta wa allolin ƙarya! Me ya sa? Shin mahaifiyarsa wadda Ba-ammoniya ce ta rinjaye shi? (1 Sar. 14:21) Ba mu sani ba, amma al’ummar ta bi misalinsa. Saboda haka, Jehobah ya ƙyale sarkin Masar mai suna Shishak ya ci birane da yawa a Yahuda da yaƙi duk da yake Rehobowam ya ƙara musu ƙarfi sosai!​—1 Sar. 14:​22-24; 2 Tar. 12:​1-4.

Yanayi ya yi tsanani sosai sa’ad da Shishak ya isa Urushalima inda karagar Rehobowam take. Sai annabi Shemaya ya idar da saƙon Allah ga Rehobowam da hakimansa. Ya ce: “Kun yashe ni, domin haka ni ma ina yashe ku ina bashe ku a hannun Shishak.” Wane mataki ne Rehobowam ya ɗauka don wannan saƙon? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sarki da shugabannin Isra’ila suka ƙasƙantar da kansu suka tuba suka ce, ‘Yahweh ya yi abin da yake daidai.’ ” Hakan ya sa Jehobah ya kāre Rehobowam da kuma Urushalima.​—2 Tar. 12:​5-7, 12.

Bayan haka, Rehobowam ya ci gaba da yin sarauta a kan mazaunan kudancin ƙasar. Kafin Rehobowam ya mutu, ya rarraba wa ’ya’yansa kyaututtuka. Da alama cewa ya yi hakan ne don kada su yi tawaye da ɗan’uwansu Abijah wanda zai gāji mulkin. (2 Tar. 11:​21-23) Hakan ya nuna cewa Rehobowam ya ƙara yin hikima sosai fiye da yadda ya yi sa’ad da ya soma sarauta.

SHI MUTUMI NE MAI AMINCI KO MARAR AMINCI?

Duk da yake Rehobowam ya ƙoƙarta don ya yi abu mai kyau, amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya aikata mugunta gama bai sa zuciyarsa ga neman Yahweh ba.”​—2 Tar. 12:14.

Rehobowam bai ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah ba kamar Sarki Dauda

Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Rehobowam? Rehobowam ya yi biyayya ga Jehobah a wasu lokuta kuma ya ɗan taimaka wa bayin Allah. Amma bai kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah ba kuma bai ƙuduri niyyar faranta masa rai ba. Hakan ya sa ya yi zunubi kuma ya bauta wa gumaka. Kana iya yin tunani cewa: ‘Sa’ad da Rehobowam ya yi biyayya ga Jehobah, ya yi hakan ne domin yana da-na-sani don kuskuren da ya yi ko domin wasu sun ce ya yi hakan?’ (2 Tar. 11:​3, 4; 12:6) Daga baya, ya soma yin abin da bai dace ba. Rehobowam bai yi koyi da kakansa Sarki Dauda ba! Babu shakka, Sarki Dauda ya yi kurakure, amma ya yi tuban gaske. Ya nuna ƙauna ga Jehobah kuma ya goyi bayan bauta ta gaskiya a dukan rayuwarsa.​—1 Sar. 14:8; Zab. 51:​1, 17; 63:1.

Za mu iya koyan darasi daga labarin Rehobowam. Muna bukatar mu yi wa iyalinmu tanadi kuma mu yi ƙwazo a hidimar Jehobah. Amma ba shi ke nan ba. Idan muna so mu sami tagomashin Jehobah, dole ne mu bauta masa a hanyar da yake so kuma mu ƙulla dangantaka mai kyau da shi.

Za mu iya yin hakan idan muna ƙaunar Jehobah sosai. Alal misali, idan muka kunna wuta kuma ba ma son wutar da ta mutu, wajibi ne mu riƙa ƙara mata itace. Hakazalika, idan ba ma so ƙaunarmu ga Jehobah ta yi sanyi, wajibi ne mu riƙa yin nazarin Kalmar Allah a kai a kai, mu yi bimbini a kan abin da muka karanta kuma mu riƙa yin addu’a. (Zab. 1:2; Rom. 12:12) Idan mun yi haka, ƙaunarmu ga Jehobah za ta motsa mu mu riƙa faranta masa rai kuma za ta motsa mu mu tuba idan mun yi zunubi. Hakan zai sa mu riƙa goyon bayan bauta ta gaskiya kuma mu guji bin misalin Rehobowam.​—Yahu. 20, 21.

^ sakin layi na 9 Jehobah ya riga ya faɗa cewa za a raba mulkin kashi biyu domin Sulemanu ya yi rashin aminci.​—1 Sar. 11:31.