Ka Bar Dokokin Allah da Kuma Ka’idodinsa Su Ja-gorance Ka
“Ƙa’idodinka su ne tunanina.”—ZAB. 119:99.
1. Wane abu ne ya sa ’yan Adam suka fi dabbobi?
LAMIRIN da Allah ya ba ’yan Adam yana cikin abubuwan da ya sa ’yan Adam suka fi dabbobi. Wannan abu ne da Allah ya ba ’yan Adam tun lokacin da ya halicce su. Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka ƙarya dokar Allah, sai suka ɓoye kansu. Me ya sa? Domin lamirinsu ya dame su.
2. Me ya sa za mu iya kwatanta lamirinmu da sitiyarin? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
2 Za a iya kwatanta mutanen da ba a horar da lamirinsu ba da jirgin ruwan da sitiyarin ɗinsa ya lalace. Tuƙa jirgin da sitiyarin ɗinsa ya lalace yana da hatsari sosai domin iska za ta iya nitsar da shi. Sitiyarin mai kyau zai iya taimaka wa matuƙin jirgi ya kiyaye hatsari. Za a iya kwatanta lamirinmu da sitiyarin. Lamirinmu shi ne abin da ke cikin zuciyarmu da ke gaya mana abu mai kyau da marar kyau. Amma idan muna so lamirinmu ya riƙa taimaka mana, dole ne mu horar da shi sosai.
3. Wane sakamako za mu samu idan ba mu horar da lamirinmu sosai ba?
3 Idan mutum bai horar da lamirinsa sosai ba, ba zai 1 Tim. 4:1, 2) Irin wannan lamirin zai iya sa mu ɗauka cewa “mugunta” abin kirki ne. (Isha. 5:20) Yesu ya gargaɗi mabiyansa cewa: “Babu shakka lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku zai yi tsammani yana yin aikin Allah ne.” (Yoh. 16:2) Tunanin da mutanen da suka kashe almajiri Istifanus suka yi ke nan. (A. M. 6:8, 12; 7:54-60) Mutane da yawa sun daɗe suna kashe-kashe kuma suna yin wasu munanan ayyuka da sunan suna yi ne don Allah. Amma irin waɗannan ayyukan sun saɓa wa dokokin Allah. (Fit. 20:13) Babu shakka, lamirinsu bai taimaka musu su yi abu mai kyau ba.
gargaɗar da shi idan yana so ya yi abu marar kyau ba. (4. Ta yaya za mu iya horar da lamirinmu don ya riƙa gargaɗar da mu?
4 Mene ne za mu yi don mu tabbatar da cewa lamirinmu yana gargaɗar da mu? Dokoki da kuma ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna da “amfani wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma horarwa cikin adalci.” (2 Tim. 3:16) Saboda haka, yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai da yin bimbini a kan abin da ke cikinsa da kuma yin amfani da darasin zai taimaka mana. Hakan zai sa lamirinmu ya riƙa motsa mu mu yi abubuwan da Jehobah yake so. Yanzu bari mu tattauna yadda dokokin Jehobah da kuma ƙa’idodinsa za su iya taimaka mana mu horar da lamirinmu.
KA BAR DOKOKIN ALLAH SU HORAR DA KAI
5, 6. Ta yaya muke amfana daga bin dokokin Allah?
5 Idan muna son dokokin Allah su taimaka mana, ba karanta Littafi Mai Tsarki kaɗai za mu riƙa yi ba. Dole ne mu ƙaunace dokokin Allah kuma mu daraja su. Kalmar Allah ta ce: “Ku ƙi mugunta, ku so abu mai kyau.” (Amos 5:15) Amma ta yaya za mu iya yin hakan? Ya kamata mu riƙa ɗaukan abubuwa yadda Jehobah yake ɗaukan su. Alal misali: A ce kana fama da rashin barci. Sai ka je asibiti kuma likita ya gaya maka irin abincin da za ka riƙa ci da irin motsa jikin da za ka riƙa yi. Ƙari ga haka, ya gaya maka cewa ka daina yin wasu abubuwan da ka saba yi. Sa’ad da ka dawo gida, sai ka yi su kuma ka lura cewa sun taimaka maka! Babu shakka, za ka yi farin ciki sosai domin likitan ya taimaka maka ka magance matsalarka.
6 Hakazalika, Mahaliccinmu ya ba mu dokokin da za su kāre mu daga fuskantar sakamako marar kyau na yin zunubi kuma za su sa mu kyautata rayuwarmu. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu riƙa yin ƙarya da zamba da sata da lalata da mugunta da kuma sihiri. (Karanta Karin Magana 6:16-19; R. Yar. 21:8) Idan mun lura cewa muna amfana sosai daga bin dokokin Jehobah, hakan zai motsa mu mu ƙaunace shi da kuma dokokinsa.
7. Yaya za mu amfana idan muna karanta labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki?
7 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan mutane da yawa da suka karya dokokin Allah da za mu iya koyan darussa daga labarinsu. Misalansu za su taimaka mana mu guji yin irin kurakuren da suka yi. Littafin Karin Magana 1:5 ya ce: “Bari mai hikima ya ji ya ƙara karɓar koyarwa.” Babu shakka, muna amfana sosai idan muka karanta labaran mutanen da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi bimbini a kan su. Alal misali, ka yi la’akari da baƙin cikin da Sarki Dauda ya yi sa’ad da ya yi zina da Bath-sheba. (2 Sam. 12:7-14) Yayin da muke karanta da kuma yin bimbini a kan wannan labarin, za mu iya yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Mene ne ya kamata Sarki Dauda ya yi don ya guji yin zina? Mene ne zan yi idan hakan ya faru da ni? Shin zan yi zina kamar Dauda ko kuwa zan gudu kamar Yusufu?’ (Far. 39:11-15) Idan mun yi tunani sosai a kan sakamako marar kyau na yin zunubi, za mu sami ƙarfin ƙin “mugunta.”
8, 9. (a) Ta yaya lamirinmu yake taimaka mana? (b) Ta yaya ƙa’idodin Jehobah suke horar da lamirinmu?
8 Wataƙila mun janye gabaki ɗaya daga yin abubuwan da Jehobah ba ya so. Amma me ya kamata mu yi idan muna so mu yanke shawara a kan wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki bai yi magana a kansu ba? Ta yaya za mu iya sanin abin da Allah yake so? Idan mun horar da lamirinmu, hakan zai taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau.
9 Da yake Jehobah yana ƙaunar mu, ya ba mu ƙa’idodin da za su ja-goranci lamirinmu. Jehobah da kansa ya ce: “Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya koya muku domin amfanin kanku, wanda ya nuna muku hanyar da za ku bi.” (Isha. 48:17, 18) Idan muna bimbini sosai a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muka bari su ratsa zukatanmu, za mu iya horar da lamirinmu. Hakan zai taimaka mana mu riƙa yanke shawarwari masu kyau.
KA BAR ƘA’IDODIN ALLAH SU JA-GORANCE KA
10. Yaya muke amfana daga ƙa’idodi, kuma ta yaya Yesu ya yi amfani da su a koyarwarsa?
10 Ƙa’idodi suna taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Idan muna so mu fahimci ma’anar ƙa’ida, wajibi ne mu fahimci ra’ayin Allah da kuma dalilan da suka sa ya kafa wasu dokoki. Sa’ad da Yesu yake duniya, ya koya wa almajiransa wasu ƙa’idodin da za su taimaka musu su san sakamakon yin wasu ayyuka. Alal misali, ya gaya musu cewa riƙe mutum a zuciya zai iya jawo kisa kuma yin sha’awar banza zai iya jawo zina. (Mat. 5:21, 22, 27, 28) Idan muka bar ƙa’idodin Jehobah su ja-gorance mu, lamirinmu zai riƙa motsa mu mu yi zaɓin da ke faranta wa Jehobah rai.—1 Kor. 10:31.
11. Ta yaya lamirinmu zai iya bambanta da na wasu?
11 Idan Kiristoci biyu suka yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen horar da lamirinsu, za su iya yanke shawarwarin da suka bambanta. Ka yi la’akari da batun shan giya. Littafi Mai Tsarki bai haramta shan giya ba. Amma ya ce kada shan giya ya zama mana jiki ko kuma mu riƙa yin maye da ita. (K. Mag. 20:1; 1 Tim. 3:8) Shin hakan yana nufin cewa Kirista zai iya shan giya a duk lokacin da ya ga dama? A’a. Ko da lamirinsa bai dame shi, ya kamata ya yi la’akari da na wasu.
12. Ta yaya abin da ke Romawa 14:21 zai motsa mu mu guji yin abin da zai shafi ’yan’uwanmu?
12 Manzo Bulus ya ce ya kamata mu riƙa yin la’akari da lamirin wasu. Ya ce: “Ya fi kyau kada ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko ka aikata kowane irin abu idan zai sa ɗan’uwanka ya faɗi.” (Rom. 14:21) Saboda haka, ko da yake Littafi Mai Tsarki bai haramta shan giya ba, amma zai dace mu janye daga yin haka idan zai sa ’yan’uwanmu tuntuɓe. A dā, wasu ’yan’uwa suna maye da giya amma da suka koyi gaskiya, sai suka ƙuduri niyya cewa ba za su sake shan giya ba. Babu shakka, ba za mu so mu sa ’yan’uwanmu su koma gidan jiya ba! (1 Kor. 6:9, 10) Saboda haka, idan mun gayyato ’yan’uwa gidanmu, ba zai dace mu taƙura musu su sha giya ba idan ba sa so.
13. Ta yaya Timoti ya kafa misali mai kyau don mutane su saurari wa’azinsa?
A. M. 16:3; 1 Kor. 9:19-23) Saboda haka, kana a shirye ka yi sadaukarwa domin ka taimaka wa wasu?
13 Sa’ad da Timoti yake matashi, ya yarda a yi masa kaciya ko da yake hakan yana da zafi sosai. Ya yi hakan domin yana so Yahudawa su saurari wa’azin da zai yi musu. Timoti yana da irin halin manzo Bulus. (“MU CI GABA” DA MANYANTA
14, 15. (a) Me ya kamata mu yi don mu nuna cewa muna samun ci gaba? (b) Ta yaya Kiristocin da suka manyanta suke sha’ani da mutane?
14 Ya kamata dukanmu mu “ci gaba” da manyanta. Kada mu mai da hankali kawai a kan “koyarwar nan ta farko wadda muka karɓa game da Almasihu.” (Ibran. 6:1) Hakan ba ya faruwa a dare ɗaya kawai. Muna bukatar mu “ci gaba” ko kuma mu sa ƙwazo. Yin hakan yana nufin cewa iliminmu da kuma fahiminmu zai ƙaru. Shi ya sa ake yawan ƙarfafa mu cewa mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum. (Zab. 1:1-3) Ka kafa maƙasudin yin hakan kuwa? Yin hakan zai sa ka daɗa fahimtar dokokin Jehobah da ƙa’idodinsa da kuma Kalmarsa sosai.
15 Dokar da aka ba Kiristoci da ta fi muhimmanci ita ce dokar nuna ƙauna. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yoh. 13:35) Wani ɗan’uwan Yesu mai suna Yaƙub ya kira ƙaunar nan “koyarwa . . . ta mulkin Allah.” (Yaƙ. 2:8) Manzo Bulus ya ce: “Ƙauna ita ce cikawar Koyarwar.” (Rom. 13:10) Yadda ake ɗaukan nuna ƙauna da muhimmanci sosai ba abin mamaki ba ne domin Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Allah yana yin abubuwan da ke nuna cewa yana ƙauna. Yohanna ya ce: “Ga yadda Allah ya nuna mana ƙaunarsa. Ya aiko da makaɗaicin ɗansa zuwa cikin duniya domin mu sami rai ta wurinsa.” (1 Yoh. 4:9) Babu shakka, ƙaunar Allah ta motsa shi ya ɗauki mataki. Idan muna nuna ƙauna ga Jehobah da Yesu da kuma ’yan’uwanmu, muna nuna cewa mu Kiristoci ne da suka manyanta.—Mat. 22:37-39.
16. Me ya sa za mu daraja ƙa’idodi yayin da muke manyanta?
1 Kor. 15:33) Amma idan yaron ya soma manyanta, zai soma sanin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Hakan zai taimaka masa ya iya zaɓan abokan kirki. (Karanta 1 Korintiyawa 13:11; 14:20.) Idan mun ci gaba da yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, lamirinmu zai riƙa motsa mu mu yi abubuwan da za su faranta wa Allah rai.
16 Yayin da muke ci gaba da zama Kiristocin da suka manyanta, za mu daraja ƙa’idodi sosai. Me ya sa? Domin dokoki suna yawan shafan abu guda, amma ƙa’idodi suna shafan abubuwa da yawa. Alal misali, ƙaramin yaro bai san cewa abokan banza za su iya ɓata shi ba. Saboda haka, iyaye masu basira suna yawan kafa dokokin da za su kāre yaransu. (17. Me ya sa za mu iya cewa muna da abubuwan da muke bukata don mu iya yin zaɓi mai kyau?
17 Muna da abubuwa da yawa da za su iya taimaka mana mu faranta wa Jehobah rai. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da dokoki da kuma ƙa’idodin da suke Kalmar Allah. Idan muna amfani da su, za mu zama ‘cikakku, mu kasance a shirye kuma domin kowane irin kyakkyawan aiki.’ (2 Tim. 3:16, 17) Saboda haka, mu riƙa bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki domin mu “fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.” (Afis. 5:17) Mu riƙa yin amfani da kayan binciken da ƙungiyar Jehobah ta tanadar. Kayan bincike kamar su Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah da Watchtower LABURARE NA INTANE da kuma manhajar JW Library. An shirya waɗannan kayan binciken domin su taimaka mana sosai sa’ad da muke nazari mu kaɗai da kuma a matsayin iyali.
ZA MU AMFANA IDAN MUN HORAR DA LAMIRINMU
18. Wace albarka ce za mu samu idan muna bin dokokin Jehobah da kuma ƙa’idodinsa?
18 Za mu sami albarka idan muna bin dokokin Jehobah da kuma ƙa’idodinsa. Zabura 119:97-100 ta ce: “Ina misalin ƙaunata ga Koyarwarka! Dukan yini ita ce tunanina. Umarninka sun sa hikimata ya fi na abokan gābana, gama kullum dokokinka suna tare da ni. Na fi dukan malamaina ganewa, gama ƙa’idodinka su ne tunanina. Na fi tsofaffi fahimta, gama ina kiyaye ƙa’idodinka.” Idan muna keɓe lokaci don mu riƙa yin ‘tunani’ a kan dokokin Allah da kuma ƙa’idodinsa, hikimarmu da fahiminmu za su ƙaru. Ƙari ga haka, idan muna yin amfani da dokokin Allah da kuma ƙa’idodinsa wajen horar da lamirinmu, za mu “zama cikakkun mutane, mu kuma kai matsayi na dukan cikar Almasihu.”—Afis. 4:13.