Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Tuna?

Ka Tuna?

Shin ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:

Waɗanne abubuwa huɗu ne za mu iya yi don mu kyautata yadda muke waƙa?

Zai dace mu riƙe littafin da kyau kuma mu ɗaga kanmu. Ya kamata mu riƙa jan numfashi sosai. Ƙari ga haka, za mu riƙa rera waƙa da kyau idan muka buɗe bakinmu kuma muka yi waƙar da babbar murya.​—w17.11, shafi na 5.

Me ya kamata ya burge mu game da wuraren da biranen mafaka suke a Isra’ila da kuma hanyoyin shiga biranen?

Akwai biranen mafaka shida a ko’ina a ƙasar da kuma hanyoyi masu kyau na shiga biranen. Shi ya sa mutum zai iya shiga biranen da sauƙi ba tare da ɓata lokaci ba.​—w17.11, shafi na 14.

Me ya sa tanadin fansa da Allah ya yi ta wurin Yesu ya fi kowace kyauta da aka ba mu?

Kyautar ta biya muradinmu na yin rayuwa har abada, kuma ta biya bukatarmu don mu iya samun ’yanci daga zunubi da kuma mutuwa. Ko da ’yan Adam masu zunubi ne, Allah ya yi wannan tanadin don yana ƙaunar su sosai.​—wp17.6, shafuffuka na 6-7.

Ta yaya littafin Zabura 118:22 ya nuna lokacin da za a ta da Yesu daga matattu?

Wasu ba su yarda cewa Yesu ne Almasihu kuma an kashe shi ba. Wajibi ne a ta da shi daga mutuwa kafin ya zama “kan kusurwa.”​—w17.12, shafuffuka na 9-10.

Shin waɗanda Almasihu ya fito daga zuriyarsu a Isra’ila ta dā ’ya’yan fari ne kawai?

Zuriyar da Yesu ya fito daga ciki ta ƙunshi ’yan fari da waɗanda ba ’yan fari ba. Dauda ba ɗan farin Jesse ba ne, duk da haka, Almasihu ya fito daga zuriyarsa.​—w17.12, shafuffuka na 14-15.

Waɗanne ƙa’idodi game da kiwon lafiya ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

A Dokar da aka ba da ta hannun Musa, ana ware mutanen da ke ɗauke da wasu irin cututtuka kuma an ce mutane su yi wanka idan sun taɓa gawa. Dokar ta ce mutum ya tona rami idan zai yi bayan gida. Ƙari ga haka, dokar Allah ta ce a yi wa yaro kaciya a rana ta takwas da haihuwa. Hakan yana da kyau don rauni yana saurin warkewa bayan mako ɗaya da haihuwar yaro.​—wp18.1, shafi na 7.

Me ya sa ya dace Kirista ya riƙa ƙaunar kansa?

Ya kamata mu riƙa ƙaunar maƙwabcinmu kamar kanmu. (Mar. 12:31) Ya kamata maza su “ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu.” (Afis. 5:28) Hakika, bai kamata mu so kanmu fiye da kima ba.​—w18.01, shafi na 23.

Me zai taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?

Muna bukatar mu riƙa nazarin Kalmar Allah kuma mu yi bimbini a kan abin da muka karanta. Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa amfani da abin da muka koya. Wajibi ne mu nemi taimakon ruhu mai tsarki kuma mu amince da taimakon mutane.​—w18.02, shafi na 26.

Me ya sa ilimin taurari da dūba ba za su sa mu san abin da zai faru a nan gaba ba?

Da akwai dalilai da yawa, amma ainihin dalilin shi ne domin Littafi Mai Tsarki ya hana mu yin waɗannan abubuwan.​—wp18.2, shafuffuka na 4-5.

Yaya ya kamata mu ɗauki gayyatar cin abinci?

Idan wani ya gayyace mu gidansa kuma mun yarda, kada mu ƙi zuwa ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba. (Zab. 15:4) Babu shakka, mutumin da ya kira mu gidansa ya riga ya yi shirye-shirye sosai.​—w18.03, shafi na 18.

Waɗanne darussa ne dattawa za su iya koya daga Timoti?

Timoti ya damu da mutane kuma bautarsa ga Jehobah ce ta fi muhimmanci a gare shi. Ƙari ga haka, ya kasance da ƙwazo a hidimarsa kuma ya yi amfani da abin da ya koya. Ya ci gaba da horar da kansa kuma ya nemi taimakon ruhun Jehobah. Ya kamata dattawa da sauran ’yan’uwa su bi misalinsa.​—w18.04, shafuffuka na 13-14.