Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Mulkina Ba Na Duniya Ba Ne’

‘Mulkina Ba Na Duniya Ba Ne’

“Wannan . . . shi ne kuma dalilin da na shigo duniya, domin in ba da shaida ga gaskiya.”​—YOH. 18:37.

WAƘOƘI: 15, 74

1, 2. (a) Mene ne yake raba kan mutane a duniyar nan? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?

WATA ’yar’uwa a kudancin Turai da take tunawa da abin da ya faru da ita a dā, ta ce: “Tun da aka haife ni, abin da nake gani shi ne rashin adalci. Saboda haka, sai na soma adawa da gwamnatin ƙasar. Har ma na zama budurwar wani ɗan ta’adda.” A dā, wani ɗan’uwa a kudancin Afirka ma ya yi tsammanin cewa jawo tashin hankali ba wani laifi ba ne. Ya ce: “Ina ganin cewa yarenmu ya fi na wasu kyau. Saboda haka, sai na shiga siyasa. An koya mana mu riƙa kashe mutanen da ba sa jam’iyyarmu da mashi ko da yarenmu ɗaya ne da su. Wata ’yar’uwa kuma da take zama a yankin Turai na tsakiya ta ce: “A dā, ina nuna bambanci sosai kuma na ƙi jinin mutanen da ba ’yan ƙasarmu ba ne ko kuma mutanen da ke bin wani addini.”

2 A yau, mutane da yawa suna da irin ra’ayin waɗannan mutanen da muka ambata. Ƙungiyoyin siyasa da yawa suna yin amfani da tashin hankali don su sami ’yanci. Mutane suna yawan yin faɗa saboda siyasa. Ƙari ga haka, a ƙasashe da yawa, an tsani baƙi. Hakan ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Ya ce a waɗannan kwanaki na ƙarshe, mutane za su zama “masu riƙe juna a zuciya.” (2 Tim. 3:​1, 3) Ta yaya Kiristoci za su kasance da haɗin kai duk da cewa mutane a duniya ba su hakan? Yin koyi da yadda Yesu ya bi da yanayi a zamaninsa zai taimaka mana. Yanzu, za mu tattauna batutuwa uku: Me ya sa Yesu ya ƙi saka hannu a yin adawa? Ta yaya ya nuna cewa bai kamata bayin Allah su saka hannu a siyasa ba? Kuma ta yaya Yesu ya nuna cewa bai kamata mu riƙa yin faɗa ba?

RA’AYIN YESU GAME DA NEMAN ’YANCI

3, 4. (a) Mene ne Yahudawa suke tsammani a zamanin Yesu? (b) Ta yaya ra’ayin ya shafi almajiran Yesu?

3 Yahudawa da yawa da Yesu ya yi musu wa’azi sun so su sami ’yanci daga Romawa. Saboda haka, wasu Yahudawa ’yan adawa suka soma fifita wannan ra’ayin. Da yawa cikinsu sun goyi bayan wani Yahuda Bagalile. Yahuda Bagalile wani annabin ƙarya ne da ya yaudari mutane da yawa a ƙarni na farko. Wani ɗan tarihi mai suna Josephus ya ce Yahuda Bagalile ya “sa mutanen su yi adawa da gwamnatin Roma kuma ya ce duk Bayahuden da ya biya haraji matsoraci ne.” A sakamakon haka, Romawa suka kashe Yahuda. (A. M. 5:37) Wasu masu tsattsauran ra’ayi sun ma soma tayar da hankulan mutane don su cim ma burinsu.

4 Ban da waɗannan mutanen, Yahudawa da yawa sun yi ɗokin zuwan Almasihu. Sun yi tsammanin cewa idan Almasihu ya zo, zai ’yantar da su daga hannun Romawa kuma ya sa Isra’ila ta sake zama ƙasa mai albarka sosai. (Luk. 2:38; 3:15) Da yawa cikinsu sun yi zato cewa Almasihu zai kafa mulki a ƙasar Isra’ila kuma hakan zai sa Yahudawa da yawa da ke zama a wasu ƙasashe su dawo ƙasarsu. Har Yohanna Mai Baftisma ya tambayi Yesu cewa: “Kai ne wanda zai zo, ko mu sa ido ga wani?” (Mat. 11:​2, 3) Wataƙila Yohanna yana so ya san ko akwai wani da zai zo ya biya dukan bukatunsu. Daga baya, almajiran Yesu guda biyu sun tambayi Yesu sa’ad da za su garin Imwasu cewa sun yi zato Yesu ne zai ’yantar da su daga hannun Romawa. (Karanta Luka 24:21.) Jim kaɗan bayan haka, almajiran Yesu sun tambaye shi cewa: “Ubangiji, yanzu ne za ka mayar wa Isra’ila mulki?”​—A. M. 1:6.

5. (a) Me ya sa mutanen Galili suke so Yesu ya zama sarkinsu? (b) Ta yaya Yesu ya daidaita ra’ayinsu?

5 Babu shakka, Yahudawa suna so Yesu ya zama sarki don ya magance matsalolinsu. Wataƙila suna tunanin cewa Yesu zai zama sarki nagari domin ya iya magana sosai, yana warkar da marasa lafiya, kuma yana da ikon ciyar da masu jin yunwa. Bayan da Yesu ya ciyar da mutane wajen 5,000, ya lura cewa suna da wani maƙarƙashiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da Yesu ya gane mutanen suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan babban tudu shi kaɗai.” (Yoh. 6:​10-15) Washegari da Yesu ya sake haɗuwa da mutanen a tsallaken Tekun Galili, ya gaya musu ainihin abin da ya kawo shi duniya. Ya ce bai zo biyan bukatunsu na zahiri ba, amma don ya koya musu game da Mulkin Allah. Ya ce: “Kada ku yi wahalar aiki a kan neman abinci mai lalacewa, amma ku yi aiki a kan abincin da zai dawwama zuwa ga rai na har abada.”​—Yoh. 6:​25-27.

6. Ta yaya Yesu ya nuna sarai cewa bai zo yin siyasa a duniya ba? (Ka duba hoto na 1 da ke shafi na 3.)

6 Jim kaɗan kafin Yesu ya mutu, ya lura cewa wasu cikin mabiyansa suna tsammani cewa zai kafa mulki a Urushalima. Amma ya yi musu gyara ta wajen yi musu wani kwatanci. Kwatancin ya ce Yesu, wanda shi “wani babban mutum” ne zai tafi wani wuri kuma ya jima a wurin. (Luk. 19:​11-13, 15) Ƙari ga haka, sa’ad da Bilatus Ba-Bunti ya tambayi Yesu cewa: “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya gaya masa cewa babu ruwansa da siyasa. (Yoh. 18:33) Wataƙila Bilatus yana tsoro cewa Yesu zai jawo tashin hankali, wanda abu ne da suke fama da shi a lokacin. Yesu ya ce masa: “Mulkina ba . . . na duniya ba ne.” (Yoh. 18:36) Yesu ya ƙi saka hannu a siyasa domin shi sarkin Mulkin Allah ne. Ya gaya wa Bilatus cewa ya zo duniya ne domin ya “ba da shaida ga gaskiya.”​—Karanta Yohanna 18:37.

Kana mai da hankali ne a kan matsalolin duniya ko kuma a kan Mulkin Allah? (Ka duba sakin layi na 7)

7. Me ya sa ba shi da sauƙi mu guji goyon bayan siyasa har ma a zuciyarmu?

7 Yesu ya san abin da ya kawo shi duniya. Ya kamata mu ma mu san ainihin aikinmu domin hakan zai taimaka mana mu guji goyon bayan siyasa har ma a cikin zuciyarmu. Gaskiya ne cewa hakan bai da sauƙi. Wani mai kula mai ziyara ya ce: “Halayen mutane a yankinmu na daɗa muni. Mutane suna kishin ƙasarsu sosai kuma suna tsammani cewa yanayinsu zai gyaru idan wani nasu ya yi sarauta. Amma abin farin ciki ne cewa ’yan’uwa suna kāre haɗin kansu ta wajen mai da hankali ga yin wa’azi game da Mulkin Allah. Suna dogara ga Allah don ya cire rashin adalci da wasu matsalolin da muke fuskanta.”

YADDA YESU YA BI DA BATUTUWAN SIYASA

8. Wane rashin adalci ne Yahudawa suka fuskanta a zamanin Yesu?

8 Idan wasu suka ga ana rashin adalci, hakan na sa su daɗa saka hannu cikin siyasa. A zamanin Yesu, batun biyan haraji ya sa mutane da yawa su goyi bayan siyasa. Yahuda Bagalile da muka ambata ɗazu ya yi adawa domin Romawa sun yi kiɗaya don su tabbatar da cewa kowa yana biyan haraji. Mutanen da suke ƙarƙashin mulkin Roma har ma da mutanen da suka saurari Yesu suna biyan haraji sosai a zamanin. Alal misali, suna biyan haraji a kan filaye da gidaje da kuma wasu kayayyakin da suka mallaka. Ƙari ga haka, masu karɓan haraji suna cin hanci da rashawa sosai kuma hakan ya daɗa ɓata lamarin. A wasu lokuta, masu karɓan haraji suna ba hukumomi cin hanci don su sami wani matsayi. Bayan haka, sai su yi amfani da matsayin wajen yin arziki. Wani mai suna Zakka wanda shi babba ne cikin masu karɓan haraji ya azurta kansa da kuɗaɗen da ya karɓa daga wurin mutane. (Luk. 19:​2, 8) Babu shakka, abin da masu karɓan haraji da yawa suke yi ke nan a lokacin.

9, 10. (a) Mene ne maƙiyan Yesu suka yi don su sa ya goyi bayan siyasa? (b) Mene ne muka koya daga amsar da Yesu ya ba su? (Ka duba hoto na 2 da ke shafi na 3.)

9 Maƙiyan Yesu sun nemi su sa shi ya saka baki a batun haraji. Sun yi masa tambaya game da harajin dinari ɗaya da mutane suke biyan Kaisar. (Karanta Matiyu 22:​16-18.) Yahudawa sun tsani biyan wannan harajin domin yana tuna musu cewa Romawa ne suke iko da su. “Mutanen Hirudus” da suka yi wannan tambayar sun yi zato cewa Yesu zai ce kada su biya harajin don su ce shi maƙiyin Kaisar ne. Amma idan Yesu ya ce su riƙa biyan harajin, mabiyansa za su iya daina bin sa.

10 Mene ne Yesu ya yi? Ya mai da hankali sosai don kada ya goyi bayan kowannensu. Ya ce: “Sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” (Mat. 22:21) Babu shakka, Yesu ya san cewa masu karɓan haraji suna cin hanci da rashawa sosai. Amma Yesu ba ya so kome ya raba hankalinsa daga abu mafi muhimmanci, wato Mulkin Allah da zai magance matsalolinmu. Ta yin hakan, ya kafa wa mabiyansa misali mai kyau. Ya kamata mu nisanta kanmu daga batutuwan siyasa, ko da muna ganin muna da hujjar yin hakan. Abin da muka saka a gaba shi ne biɗan Mulkin Allah da kuma adalcinsa. Saboda haka, bai kamata mu furta ra’ayinmu game da wani batun siyasa da ya taso ba.​—Mat. 6:33.

11. Ta yaya za mu iya yin amfani da burinmu na son adalci a hanyar da ta dace?

11 Shaidun Jehobah da yawa sun yi nasara wajen nisanta kansu daga batutuwan siyasa. Wata ’yar’uwa da ke Biritaniya ta ce: “Bayan da na karance ilimin zaman jama’a a makarantar jami’a, sai na soma kasancewa da tsattsauran ra’ayi. Na so in ƙwato wa baƙaƙen fata ’yancinsu domin ana danne hakkinsu. Ko da yake ina yawan yin mahawwara game da baƙaƙen fata kuma ina yin nasara, amma duk da haka, ba na farin ciki. Ban san cewa abin da ke sa mutane su nuna bambancin launin fata yana cikin zuciyarsu ba. Da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na fahimci cewa ni ce ke bukatar in fara cire wannan ƙiyayyar daga zuciyata. Wata ’yar’uwa farar fata ce ta taimaka mini in yi wannan canjin. A yanzu haka, ina hidimar majagaba a wata ikilisiyar da ake yaren kurame. Ina koyan yin cuɗanya da mutanen ƙabilu dabam-dabam.”

KA “MAI DA TAKOBINKA”

12. Wane irin ‘yisti’ ne Yesu ya gaya wa almajiransa su guje wa?

12 A zamanin Yesu, malaman addinai suna yawan goyon bayan siyasa. Littafin nan Daily Life in Palestine at the Time of Christ ya ce, addinan da Yahudawa suke bi yana kamar jam’iyyoyin siyasa. Shi ya sa Yesu ya ja kunnen almajiransa cewa: “Ku kula fa, kuma ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.” (Mar. 8:15) Wataƙila Hirudus da Yesu ya ambata a ayar yana nufin magoyan bayan Hirudus. Farisiyawa suna so Yahudawa su sami ’yanci daga hannun Romawa. Ƙari ga haka, a littafin Matiyu, Yesu ya gargaɗi almajiransa cewa su yi hankali da Sadukiyawa. Sadukiyawa suna so Romawa su ci gaba da mulki domin hakan yana sa su kasance da iko. Sadukiyawa da yawa suna da matsayi a mulkin Romawa. Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su yi hankali da ‘yisti’ ko kuma koyarwar mabiyan Hirudus da Farisiyawa da kuma Sadukiyawa. (Mat. 16:​6, 12) Yesu ya yi wannan gargaɗin jim kaɗan bayan mutanen sun so su naɗa shi sarki.

13, 14. (a) Ta yaya batun siyasa da addini yake jawo faɗa da rashin adalci? (b) Me ya sa bai kamata mu ɗauki mataki ba ko da muna fuskantar rashin adalci? (Ka duba hoto na 3 da ke shafi na 3.)

13 Idan addinai suka goyi bayan siyasa, hakan yana yawan jawo faɗa. Yesu ya koya wa almajiransa cewa wajibi ne su nisanta kansu daga harkokin siyasa. Hakan yana cikin dalilan da suka sa manyan firistoci da Farisiyawa suka so su kashe Yesu. Suna tsoro cewa mutane za su daina goyon bayansu. Suka ce: “In fa muka ƙyale shi yana yin abubuwan nan, dukan mutane za su ba da gaskiya gare shi. Sa’an nan Romawa kuma za su zo su ƙwace ƙasarmu da kuma Haikalinmu!” (Yoh. 11:48) Saboda haka, Kayafa babban firist ya ja-goranci ƙullin da aka yi don a kashe Yesu.​—Yoh. 11:​49-53; 18:14.

14 Kayafa ya tura sojoji daddare su kama Yesu. Amma Yesu ya riga ya san cewa ana maƙarƙashiya don a kashe shi. Shi ya sa a lokacin da ya ci abincin dare na ƙarshe da almajiransa, ya gaya musu su ɗauki takuba biyu. Me ya sa? Domin zai yi amfani da takoban wajen koya musu darasi mai muhimmanci. (Luk. 22:​36-38) A daren, sai ’yan tawaye suka zo su kama Yesu. Hakan ya ɓata wa Bitrus rai sosai har ya zaro takobinsa ya soma faɗa. (Yoh. 18:10) Sai Yesu ya gaya wa Bitrus cewa: Ka “mai da takobinka, gama duk wanda ya ɗauki takobi, takobi ne zai kashe shi.” (Mat. 26:​52, 53) Wane darasi mai muhimmanci ne Yesu ya koya musu? Ya koya musu cewa su nisanta kansu daga harkokin duniya kuma ya yi addu’a a kan wannan batun a daren. (Karanta Yohanna 17:16.) Allah ne kaɗai yake da ikon magance duk wani rashin adalcin da muke fuskanta.

15, 16. (a) Ta yaya Kalmar Allah ta taimaka wa Kiristoci su guji yin faɗa? (b) Wane bambanci ne ke tsakanin bayin Jehobah da mutanen da ba bayinsa ba?

15 Darasin da ’yar’uwa daga kudancin Turai da muka ambata ɗazun ta koya ke nan. Ta ce: “Na koyi cewa yin faɗa ba ya ƙwato wa mutum hakkinsa. Mutanen da suke yin faɗa suna yawan mutuwa. Wasu kuma suna kasancewa da ɓacin rai. Na yi farin ciki sosai da na koya a Littafi Mai Tsarki cewa Allah ne kaɗai zai iya kawo adalci a duniyar nan. Na yi shekara 25 yanzu ina yin wa’azi game da wannan gaskiyar.” Ɗan’uwa daga kudancin Afirka da muka ambata ya yar da māshinsa. Amma yanzu, yana amfani da “takobin Ruhu,” wato Kalmar Allah yayin da yake yaɗa albishiri ga maƙwabtansa kome al’adarsu. (Afis. 6:17) Bayan ’yar’uwa daga Turai na tsakiya da muka ambata ɗazun ta zama Mashaidiyar Jehobah, ta auri wani ɗan’uwa daga ƙabilar da ta tsani a dā. Dukan waɗannan ’yan’uwa uku sun yi waɗannan canje-canje domin suna so su zama kamar Kristi.

16 Yin waɗannan canje-canjen na da muhimmanci sosai. Littafi Mai Tsarki ya kamanta ’yan Adam da kogin da ke hayaniya yana bala’i kullum. (Isha. 17:12; 57:​20, 21; R. Yar. 13:1) Batutuwan siyasa na sa mutane fushi, yana raba kansu kuma yana jawo faɗa. Amma mu muna zama cikin kwanciyar hankali da haɗin kai. Babu shakka, Jehobah yana yin farin ciki sosai idan ya ga yadda muke da haɗin kai a wannan duniyar da mutane ba sa haɗin kai.​—Karanta Zafaniya 3:17.

17. (a) A waɗanne hanyoyi uku ne za mu iya sa haɗin kanmu ya ci gaba? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 A wannan talifin, mun koya cewa za mu iya sa a kasance da haɗin kai a hanyoyi uku: (1) Idan mun dogara ga Mulkin Allah don ya cire rashin adalci, (2) idan mun ƙi goyon bayan siyasa, da kuma (3) idan mun ƙi saka hannu a tashin hankali. Amma a wasu lokuta, nuna bambanci yana iya jawo rabuwar kai. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu iya magance wannan matsalar yadda Kiristoci suka yi a ƙarni na farko.