TALIFIN NAZARI NA 25
Ka Dogara ga Jehobah Sa’ad da Kake Cikin Damuwa
“Damuwa a zuciya takan hana mutum sakewa.”—K. MAG. 12:25.
WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Me ya sa wajibi ne mu bi gargaɗin Yesu?
A ANNABCIN da Yesu ya yi game da kwanaki na ƙarshe, ya ce: “Ku zauna a shirye fa. Kada ku bar . . . damuwar rayuwar duniya su ɗauki hankalinku.” (Luk. 21:34) Ya kamata mu bi wannan gargaɗin. Me ya sa? Domin a yau, muna fuskantar irin matsalolin da sauran ʼyan Adam suke fuskanta.
2. Waɗanne matsaloli ne ’yan’uwanmu suke fuskanta?
2 A wasu lokuta, muna fuskantar matsaloli dabam-dabam a lokaci ɗaya. Alal misali, akwai wani Mashaidi mai suna John * da ke fama da ciwon multiple sclerosis, wato ciwon garkuwan jiki. Ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da matarsa ta bar shi bayan sun yi shekara 19 da aure. Bayan haka, yaransa mata biyu suka daina bauta wa Jehobah. Wasu ma’aurata masu suna Bob da Linda sun fuskanci wasu matsaloli dabam. An sallame su daga aiki, kuma aka kore su daga gida don ba su iya biyan kuɗin haya ba. Ƙari ga haka, likita ya binciko cewa Linda tana da ciwon zuciya da zai iya kashe ta. Ban da haka, tana da wata cuta da ke kashe garkuwar jikinta.
3. Mene ne littafin Filibiyawa 4:6, 7 ya gaya mana game da Jehobah?
3 Muna da tabbaci cewa Mahaliccinmu Jehobah mai ƙaunar mu ya san yadda muke ji sa’ad da muke fama da matsaloli. Kuma yana so ya taimaka mana mu jimre. (Karanta Filibiyawa 4:6, 7.) Kalmar Allah tana ɗauke da misalai da yawa da suka nuna matsalolin da bayin Jehobah suka jimre. Ƙari ga haka, ya bayyana yadda Jehobah ya taimaka musu su jimre da waɗannan matsalolin. Bari mu tattauna wasu cikin misalan.
“ILIYA MUTUM NE KAMAR MU”
4. Waɗanne ƙalubale ne Iliya ya fuskanta, kuma yaya ya ji game da Jehobah?
4 Iliya ya bauta wa Jehobah a mawuyacin lokaci kuma ya fuskanci ƙalubale sosai. Sarki Ahab yana cikin sarakuna marasa aminci na Isra’ila kuma ya auri Jezebel, wata muguwa mai bauta wa Ba’al. Su biyu sun ɗaukaka bautar Ba’al a ƙasar kuma suka kashe annabawan Jehobah da yawa, amma Iliya ya tsira. Sa’ad da ake fari a ƙasar, Iliya bai mutu ba don ya dogara ga Jehobah. (1 Sar. 17:2-4, 14-16) Ƙari ga haka, Iliya ya dogara ga Jehobah sa’ad da ya yi adawa da annabawa da kuma masu bauta wa Ba’al. Sai ya gargaɗi Isra’ilawa su bauta wa Jehobah. (1 Sar. 18:21-24, 36-38) Iliya yana da tabbaci sosai cewa Jehobah yana taimaka masa a waɗannan mawuyacin lokaci.
5-6. Kamar yadda yake a littafin 1 Sarakuna 19:1-4, yaya Iliya ya ji, kuma yaya Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar sa?
5 Karanta 1 Sarakuna 19:1-4. Amma, Iliya ya ji tsoro sa’ad da Sarauniya Jezebel ta ce za ta kashe shi. Sai ya guda zuwa yankin Beer-sheba. Ya yi sanyin gwiwa sosai har ya ce ya gwammace ya mutu. Me ya sa Iliya ya ji hakan? Iliya ajizi ne kuma “mutum ne kamar mu.” (Yaƙ. 5:17) Wataƙila ya gaji ainun don matsalolin da yake ciki. Mai yiwuwa, Iliya yana ganin cewa duk ƙoƙarce-ƙoƙarcen da yake yi don ya ɗaukaka bauta ta gaskiya bai da amfani. Ƙari ga haka, wataƙila yana ganin babu abin da ya canja a Isra’ila kuma shi kaɗai ne har ila yake bauta wa Jehobah. (1 Sar. 18:3, 4, 13; 19:10, 14) Mai yiwuwa, muna mamaki cewa wannan annabi mai aminci ya yi sanyin gwiwa. Amma Jehobah ya fahimci yadda Iliya yake ji.
6 Jehobah bai tsauta wa Iliya ba don ya faɗi yadda yake ji. Maimakon haka, ya ƙarfafa shi. (1 Sar. 19:5-7) Daga baya, Jehobah ya daidaita ra’ayin Iliya a hankali ta wajen nuna masa ikonsa mai ban al’ajabi. Sai Jehobah ya gaya masa cewa har ila da akwai mutane 7,000 a Isra’ila da ba su bauta wa Ba’al ba. (1 Sar. 19:11-18) Ta wajen ba Iliya waɗannan misalan, Jehobah ya nuna masa cewa yana ƙaunar sa.
YADDA JEHOBAH ZAI TAIMAKA MANA
7. Ta yaya yadda Jehobah ya taimaka wa Iliya ya ƙarfafa mu?
7 Kana fama da wata matsala ne? Sanin cewa Jehobah ya fahimci yadda Iliya yake ji ya ƙarfafa mu sosai! Hakan ya tabbatar mana da cewa Jehobah ya san matsalolin da muke fama da su. Ya san kasawarmu, kuma ya san tunaninmu da yadda muke ji. (Zab. 103:14; 139:3, 4) Idan muka dogara ga Jehobah kamar Iliya, Jehobah zai taimaka mana mu jimre da matsalolinmu.—Zab. 55:22.
8. Ta yaya Jehobah zai taimaka maka ka jimre da matsaloli?
8 Baƙin ciki zai sa ka riƙa tunani cewa ba za ka taɓa fita daga cikin matsala ba, kuma hakan zai sa ka yi sanyin gwiwa. Idan hakan ya faru, ka tuna cewa Jehobah zai taimaka maka ka jimre. Ta yaya zai taimaka maka? Allah ya ce mu riƙa gaya masa matsalolinmu da kuma yadda muke ji. Kuma zai amsa addu’o’inmu na neman taimako. (Zab. 5:3; 1 Bit. 5:7) Saboda haka, ka riƙa gaya wa Jehobah matsalolinka. Ko da ba zai yi magana da kai kamar yadda ya yi da Iliya ba, zai yi magana da kai ta wajen Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa. Labaran da ka karanta a Littafi Mai Tsarki za su ƙarfafa ka kuma su sa ka kasance da bege. Ƙari ga haka, ’yan’uwa za su ƙarfafa ka.—Rom. 15:4; Ibran. 10:24, 25.
9. Ta yaya abokinmu zai iya taimaka mana?
9 Jehobah ya gaya wa Iliya ya ba Elisha wasu ayyuka. Ta hakan, ya ba Iliya abokin kirki da zai taimaka masa ya jimre sa’ad da ya yi sanyin gwiwa. Hakazalika, idan muka gaya wa abokinmu yadda muke ji, zai taimaka mana mu jimre da matsalolinmu. (2 Sar. 2:2; K. Mag. 17:17) Me za ka yi idan kana ganin ba ka da wanda za ka iya gaya wa matsalolinka da yadda kake ji? Ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka maka ka sami Kirista da ya manyanta da zai ƙarfafa ka.
10. Ta yaya labarin Iliya ya sa mu kasance da bege, kuma ta yaya abin da ke littafin Ishaya 40:28, 29 zai taimaka mana?
10 Iliya ya jimre da matsalolinsa kuma ya bauta wa Jehobah da aminci shekaru da yawa don Jehobah ya taimaka masa. Labarin Iliya ya sa mu kasance da bege. A wasu lokatai, mukan fuskanci matsalolin da suke sa mu sanyin gwiwa sosai. Duk da haka, idan muka dogara ga Jehobah, zai ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta masa.—Karanta Ishaya 40:28, 29.
HANNATU DA DAUDA DA WANI MARUBUCIN ZABURA SUN DOGARA GA JEHOBAH
11-13. Ta yaya matsaloli suka shafi Hannatu da Dauda da wani marubucin Zabura?
11 Akwai mutanen da aka ambata a Littafi Mai Tsarki da suka fuskanci matsaloli sosai. Alal misali, Hannatu ta yi baƙin ciki 1 Sam. 1:2, 6) Matsalolin Hannatu sun sa ta ɓacin rai har ta yi ta kuka kuma ba ta iya cin abinci ba.—1 Sam. 1:7, 10.
domin ba ta iya haihuwa ba kuma kishiyarta takan yi mata dariya da kuma wulaƙanci. (12 Akwai lokacin da matsaloli suka yi wa Sarki Dauda yawa. Ka yi tunanin irin matsalolin da ya fuskanta. Dauda ya yi baƙin ciki sosai domin ya yi kura-kurai da yawa. (Zab. 40:12) Absalom, ɗan da Dauda yake ƙauna ya yi masa tawaye, kuma hakan ya sa aka kashe Absalom. (2 Sam. 15:13, 14; 18:33) Ƙari ga haka, ɗaya cikin aminan Dauda ya ci amanarsa. (2 Sam. 16:23–17:2; Zab. 55:12-14) Zabura da yawa da Dauda ya rubuta sun kwatanta yadda ya yi sanyin gwiwa da kuma yadda ya dogara sosai ga Jehobah.—Zab. 38:5-10; 94:17-19.
13 Daga baya, wani marubucin zabura ya soma kishin salon rayuwar mugaye. Wataƙila ya fito ne daga iyalin Asaph Ba-lawi, kuma yana hidima a “Wuri Mai Tsarki na Allah.” Wannan marubucin zabura ya fuskanci matsaloli sosai, kuma hakan ya sa shi baƙin ciki da kuma rashin gamsuwa. Ya sa ya soma tunanin cewa ba zai sami albarka ba idan yana bauta wa Allah.—Zab. 73:2-5, 7, 12-14, 16, 17, 21.
14-15. Me muka koya daga misalai guda uku da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da neman taimako daga Jehobah?
14 Waɗannan bayin Jehobah da muka ambata sun dogara ga Jehobah. Sun gaya wa Jehobah matsalolinsu a addu’a. Sun gaya masa kai tsaye abubuwan da ke sa su baƙin ciki. Kuma ba su daina zuwa wuraren ibada don su bauta wa Jehobah ba.—1 Sam. 1:9, 10; Zab. 55:22; 73:17; 122:1.
15 Jehobah ya amsa addu’arsu don ya tausaya musu. Hannatu ta sami kwanciyar 1 Sam. 1:18) Dauda ya ce: “Mai adalci yakan sami wahaloli da yawa, amma Yahweh yakan kuɓutar da shi daga cikinsu duka.” (Zab. 34:19) Kuma daga baya, Asaph ya ga cewa Jehobah yana ‘riƙe shi a hannun damansa’ kuma yana ba shi shawara mai kyau. Ya ce: “A gare ni, yana da kyau a yi kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Yahweh wurin ɓuyana.” (Zab. 73:23, 24, 28) Me muka koya daga waɗannan misalan? A wasu lokuta, mukan fuskanci matsaloli masu tsanani da za su iya sa mu sanyin gwiwa. Amma za mu iya jimrewa idan muka yi bimbini a kan yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa. Kuma mu dogara a gare shi ta wurin yin addu’a da kuma bin umurninsa.—Zab. 143:1, 4-8.
hankali. (ZA KA YI NASARA IDAN KA DOGARA GA JEHOBAH
16-17. (a) Me ya sa bai kamata mu riƙa ware kanmu ba? (b) Ta yaya za mu sami ƙarfafa?
16 Waɗannan misalai uku sun koya mana wani darasi mai muhimmanci. Bai kamata mu ware kanmu daga Jehobah da kuma mutanensa ba. (K. Mag. 18:1) Nancy wadda ta yi baƙin ciki sosai sa’ad da mijinta ya bar ta, ta ce: “Da akwai kwanakin da ba na son in ga kowa ko kuma yin magana da kowa. Amma, yin hakan ya sa na daɗa baƙin ciki.” Amma Nancy ta magance wannan matsalar sa’ad da ta nemi hanyoyin taimaka ma waɗanda suke fuskantar matsaloli. Ta ce: “Na lura cewa mai da hankali ga taimaka ma waɗanda suke fuskantar matsaloli, ya sa na daina mai da hankali ga matsalolina.”
17 Mukan ƙarfafa kanmu ta wurin halartar taron ikilisiya. Idan muka halarci taro, muna ba Jehobah damar taimaka mana da kuma yi mana “ta’aziyya.” (Zab. 86:17) A wurin, Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki da Kalmarsa da kuma mutanensa don ya ƙarfafa mu. Muna kuma samun damar “ƙarfafa” juna a taro. (Rom. 1:11, 12) Wata ’yar’uwa mai suna Sophia ta ce: “Jehobah da kuma ’yan’uwanmu sun taimaka min in jimre. Taron ikilisiya ya fi muhimmanci a gare ni. Kuma na lura cewa na fi jimrewa sa’ad da na ƙara ƙwazo a hidima da kuma yin ayyukan ikilisiya.”
18. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana idan muka yi sanyin gwiwa?
18 Idan muna sanyin gwiwa, ya kamata mu tuna cewa Jehobah ya yi mana alkawari cewa a nan gaba, zai kawar da dukan abubuwan da ke sa mu baƙin ciki. Ban da haka, zai taimaka mana mu jimre da matsalolin da muke fama da su a yanzu. Jehobah yana sa mu iya jimrewa da dukan abubuwan da ke sa mu sanyin gwiwa da rashin bege.—Filib. 2:13.
19. Wane alkawari ne aka yi mana a Romawa 8:37-39?
19 Karanta Romawa 8:37-39. Manzo Bulus ya tabbatar mana da cewa babu abin da zai iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana. Ta yaya za mu iya taimaka wa ’yan’uwanmu da suke fama da matsaloli? A talifi na gaba, za mu tattauna yadda za mu yi koyi da Jehobah ta wajen tausaya wa ’yan’uwanmu. Za mu kuma koyi yadda za mu taimaka musu sa’ad da suke cikin matsala.
WAƘA TA 44 Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala
^ sakin layi na 5 Yawan damuwa na dogon lokaci zai iya shafanmu sosai. Ta yaya Jehobah zai iya taimaka mana? Za mu tattauna yadda Jehobah ya taimaka wa Iliya ya jimre sa’ad da yake baƙin ciki. Misalan wasu a cikin Littafi Mai Tsarki zai nuna mana abin da muke bukatar mu yi don mu sami taimakon Jehobah sa’ad da muke cikin damuwa.
^ sakin layi na 2 An canja wasu sunaye a wannan talifin.
^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Mala’ikan Jehobah ya ta da Iliya a hankali daga barci kuma ya ba shi abinci da ruwa.
^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: Wani marubucin zabura daga iyalin Asaph yana jin daɗin rubuta zabura da kuma rera waƙa tare da abokansa Lawiyawa.