Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 26

Ka Taimaka wa Mutane Su Jimre da Matsaloli

Ka Taimaka wa Mutane Su Jimre da Matsaloli

“Dukanku ku haɗa hankalinku ya zama ɗaya. Kuna jin tausayin juna, kuna kuma ƙaunar ’yan’uwa, kuna nuna halin taimakon juna ba tare da ɗaga kai ba.”​—1 BIT. 3:8.

WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah, Allah mai ƙauna?

JEHOBAH yana ƙaunar mu sosai. (Yoh. 3:16) Muna son mu yi koyi da Ubanmu mai ƙauna, don haka, muna ‘jin tausayin juna, muna ƙaunar ’yan’uwa, [kuma] muna nuna halin taimakon juna’ musamman ma ga “ ’yan’uwanmu cikin Almasihu.” (1 Bit. 3:8; Gal. 6:10) Idan ’yan’uwanmu suna fuskantar matsaloli muna son mu taimaka musu.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Dukan bayin Jehobah za su fuskanci matsaloli. (Mar. 10:​29, 30) Za mu fuskanci matsaloli sosai da yake ƙarshen wannan zamanin ya yi kusa. Ta yaya za mu taimaka wa juna? Bari mu tattauna abin da za mu iya koya daga labarin Lutu da Ayuba da kuma Naomi. Ban da haka, za mu tattauna wasu matsalolin da ’yan’uwanmu suke fuskanta a yau, kuma za mu ga yadda za mu iya taimaka musu su jimre.

KA ZAMA MAI HAƘURI

3. Kamar yadda 2 Bitrus 2:​7, 8 suka nuna, wace shawara marar kyau ce Lutu ya yanke, kuma wane sakamako hakan ya kawo?

3 Lutu ya yanke shawarar da ba ta dace ba sa’ad da ya zaɓi ya zauna a Saduma tare da mutane masu lalata sosai. (Karanta 2 Bitrus 2:​7, 8.) Akwai arziki sosai a ƙasar, amma Lutu ya fuskanci matsaloli da yawa a Saduma. (Far. 13:​8-13; 14:12) Wataƙila matarsa tana son birnin ko kuma mazaunan birnin, kuma hakan ya sa ta yi wa Jehobah rashin biyayya. Ta mutu sa’ad da Allah ya sa aka yi ruwan wuta da ƙibiritu a yankin. ’Ya’yan Lutu kuma fa? Mazan da suka yi musu alkawarin za su aure su sun mutu a Saduma. Lutu ya yi hasarar dukiyarsa da gidansa kuma matarsa ta mutu. (Far. 19:​12-14, 17, 26) Sa’ad da Lutu yake cikin wannan matsalar, Jehobah ya yi fushi ne? A’a.

Jehobah ya tura mala’iku su ceci Lutu da iyalinsa don yana jin tausayin su (Ka duba sakin layi na 4)

4. Ta yaya Jehobah ya yi haƙuri da Lutu? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

4 Duk da cewa Lutu ya zaɓi ya zauna a Saduma, Jehobah ya tausaya masa kuma ya tura mala’iku su cece shi da iyalinsa. Amma maimakon su bi umurnin mala’ikun kuma su bar Saduma, sun “yi ta jan jiki.” Sai mala’ikun suka kama hannunsa da kuma iyalinsa suka taimaka musu su bar birnin. (Far. 19:​15, 16) Bayan haka, mala’ikun suka umurce su su gudu zuwa kan tuddai. Amma maimakon su bi umurnin Jehobah, Lutu ya roƙi Jehobah ya bar shi ya je wani gari da ke kusa da wurin. (Far. 19:​17-20) Jehobah ya yi haƙuri da Lutu kuma ya yarda ya je garin. Daga baya, Lutu ya soma tsoron zama a garin kuma ya koma kan tuddai da zama, wurin da tun da farko Jehobah ya ce ya je. (Far. 19:30) Jehobah ya yi haƙuri da Lutu sosai! Ta yaya za mu yi koyi da shi?

5-6. Ta yaya za mu bi shawarar da ke 1 Tasalonikawa 5:14 yayin da muke yin koyi da Allah?

5 Kamar Lutu, wani a ikilisiya yana iya tsai da shawarar da ta jawo masa matsaloli sosai. Idan hakan ya faru, mene ne za mu yi? Wataƙila za mu so mu gaya masa cewa yana girban abin da ya shuka. Babu shakka, hakan gaskiya ne. (Gal. 6:7) Amma, zai fi kyau mu taimaka masa kamar yadda Jehobah ya taimaka wa Lutu. Ta yaya?

6 Jehobah ya tura mala’ikun ba kawai don su yi wa Lutu kashedi ba amma don su taimaka masa ya bar Saduma kafin a halaka birnin. Hakazalika, muna bukatar mu yi wa ɗan’uwanmu kashedi idan muka ga cewa zai sa kansa cikin matsala. Ban da haka, za mu bukaci taimaka masa. Ko da bai bi shawarar da muka ba shi nan take ba, muna bukatar mu yi haƙuri da shi. Mu yi koyi da mala’iku biyun nan. Maimakon mu fid da rai kuma mu ƙyale shi, zai dace mu taimaka masa ta furucinmu da ayyukanmu. (1 Yoh. 3:18) Mu taimaka masa ya yi amfani da shawarar da muka ba shi.​—Karanta 1 Tasalonikawa 5:14.

7. Ta yaya za mu yi koyi da yadda Jehobah ya ɗauki Lutu?

7 Jehobah bai mai da hankali ga ajizancin Lutu ba. A maimakon haka, ya hure manzo Bitrus ya rubuta cewa Lutu mutum mai adalci ne. Muna farin ciki sosai cewa Jehobah ba ya mai da hankali ga kura-kurenmu! (Zab. 130:3) Za mu iya yin koyi da yadda Jehobah ya ɗauki Lutu kuwa? Idan muka mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwanmu, hakan zai taimaka mana mu riƙa haƙuri da su. Zai fi kasance musu da sauƙi su riƙa bin shawarar da muka ba su.

KA ZAMA MAI JUYAYI

8. Mene ne tausayi zai motsa mu mu yi?

8 Ayuba bai sha wahala saboda shawarar da ya tsai da kamar Lutu ba. Duk da haka, ya fuskanci matsaloli sosai. Ya yi hasarar dukiyarsa, da matsayinsa a yankinsu kuma ya yi rashin lafiya. Mafi muni ma, yaransa sun mutu. Ƙari ga haka, abokan Ayuba uku sun zarge shi. Wane dalili ne ya sa abokansa uku suka ƙi tausaya masa? Ba su fahimci ainihin abin da ke faruwa da Ayuba ba. Saboda haka, sun yanke shawara ba tare da samun cikakken bayani ba kuma suka shari’anta Ayuba. Ta yaya za mu guji yin irin wannan kuskuren? Muna bukatar mu sani cewa Jehobah ne ya san gaskiyar yanayin da mutum ke ciki. Mu saurari wanda ke cikin matsalar da kyau. Mu yi ƙoƙarin fahimtar yadda yake ji. Ta yin hakan ne za mu nuna cewa muna tausaya wa ’yan’uwanmu.

9. Mene ne jin tausayi zai hana mu yi, kuma me ya sa?

9 Tausayi zai hana mu yaɗa gulma game da matsalar da ’yan’uwanmu ke fuskanta. Mai gulma yana raba ’yan’uwa maimakon sa su kasance da haɗin kai. (K. Mag. 20:19; Rom. 14:19) Mai gulma ba mutumin kirki ba ne, amma marar tunani ne, kuma kalamansa suna iya jawo wa mutumin da ke cikin matsala baƙin ciki. (K. Mag. 12:18; Afis. 4:​31, 32) Zai fi kyau idan muka mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwanmu kuma muka yi ƙoƙarin taimaka musu su jimre da matsaloli!

Ka saurara da kyau idan wani ɗan’uwa ya soma yin maganganun da ba su dace ba, sai ka ta’azantar da shi a lokacin da ya dace (Ka duba sakin layi na 10-11) *

10. Mene ne abin da ke Ayuba 6:​2, 3 ya koya mana?

10 Karanta Ayuba 6:​2, 3A wasu lokuta, Ayuba ya yi “saurin magana,” wato ya yi maganganun da ba su dace ba. Amma daga baya ya yi da-na-sani don abubuwan da ya faɗa. (Ayu. 42:6) Kamar Ayuba, a yau mutumin da ke fuskantar matsaloli yana iya soma yin maganganun da daga baya zai yi da-na-sani. Mene ne za mu yi? Maimakon hakan ya ɓata mana rai, ya kamata mu tausaya wa mutumin. Mu tuna cewa ba nufin Jehobah ba ne mu riƙa fuskantar matsaloli ba. Saboda haka, muna iya fahimtar dalilin da ya sa bawan Jehobah zai iya yin maganganun da ba su dace ba sa’ad da yake fuskantar matsaloli. Ko da sun faɗi abin da bai dace ba game da Jehobah ko kuma game da mu, kada hakan ya ɓata mana rai da sauri ko kuma mu shari’anta su.​—K. Mag. 19:11.

11. Ta yaya dattawa za su yi koyi da Elihu sa’ad da suke ba da shawara?

11 A wasu lokuta, mutumin da ke fuskantar matsaloli yana bukatar a yi masa gargaɗi ko kuma horo. (Gal. 6:1) Ta yaya dattawa za su yi hakan? Zai dace su yi koyi da Elihu wanda ya saurari Ayuba don yana tausaya masa. (Ayu. 33:​6, 7) Bayan Elihu ya fahimci ra’ayin Ayuba da kyau, sai ya ba shi shawara. Dattawan da ke bin misalin Elihu za su yi ƙoƙari su fahimci yanayin mutumin da ke fuskantar matsaloli kuma su saurare shi da kyau. Bayan haka, idan suka ba shi shawara, yana iya ratsa zuciyarsa.

KA TA’AZANTAR DA MUTANE

12. Ta yaya mutuwar mijin Naomi da yaranta biyu ya shafe ta?

12 Naomi mace ce mai aminci da ke ƙaunar Jehobah. Amma bayan mijinta da kuma yaranta biyu suka mutu, ta so ta canja sunanta daga Naomi zuwa “Mara” da ke nufin “ɗaci.” (Rut 1:​3, 5, 20, 21) Rut surkuwar Naomi ta kasance tare da ita sa’ad da take fuskantar matsalolin nan. Rut ta biya bukatun Naomi, kuma ta ta’azantar da ita. Ta nuna ƙaunarta ga Naomi kuma ta goyi bayanta ta kalmominta masu ban-ƙarfafa.​—Rut 1:​16, 17.

13. Me ya sa waɗanda mijinsu ko matarsu ta rasu suke bukatar taimakonmu?

13 Idan miji ko kuma matar wani a ikilisiya ta mutu, ɗan’uwan zai bukaci taimakonmu sosai. Muna iya kwatanta ma’aurata da bishiyoyi guda biyu da suka yi girma kusa da juna. Da shigewar lokaci, jijiyoyinsu za su haɗe. Idan aka sare ɗaya, zai shafi ɗayan bishiyar sosai. Hakazalika, idan miji ko matar wani ta rasu, hakan yana iya sa mutumin baƙin ciki na dogon lokaci. Wata mai suna Paula * da mijinta ya rasu, ta ce: “Rayuwata ta canja sosai, kuma hakan ya sa na ji kamar ban da taimako. Na yi rashin aminina. Nakan tattauna kome da mijina. Yana farin ciki idan ina farin ciki kuma yana taimaka mini sa’ad da nake fuskantar matsaloli. A koyaushe yana saurara ta idan ina so in gaya masa abin da ke damuna. Na ji kamar an raba ni waje biyu.”

Ta yaya za mu taimaka ma waɗanda mijinsu ko matarsu ta rasu? (Ka duba sakin layi na 14-15) *

14-15. Ta yaya za mu ta’azantar da wanda matarsa ko mijinta ya rasu?

14 Ta yaya za mu ta’azantar da wanda matarsa ko mijinta ya rasu? Abu mafi muhimmanci shi ne mu tattauna da shi ko ita ko da yin hakan ba zai yi mana sauƙi ba, ko kuma ba mu san abin da za mu ce ba. Paula da aka ambata ɗazu, ta ce: “Na fahimci cewa sa’ad da wani ya mutu, mutane suna tsoro kada su faɗi abin da zai daɗa jawo baƙin ciki. Amma ƙin yin magana ne ya fi sa mutum baƙin ciki.” Mutumin da yake makoki ba ya bukatar mu faɗa masa abin a-zo-a-gani. Paula ta ce: “Ina godiya sa’ad da abokaina suka ce mini: ‘Yaya haƙuri?’ ”

15 Wani mai suna William da matarsa ta rasu shekaru da suka shige, ya ce: “Ina farin ciki sa’ad da mutane suka ba da labarin matata. Yana nuna cewa mutane sun ƙaunace ta, sun daraja ta kuma hakan yana taimaka mini sosai. Furucinsu na ƙarfafa ni sosai don matata tana da daraja sosai a gare ni.” Wata mai suna Bianca da mijinta ya rasu ta ce: “Ina samun ƙarfafa sosai sa’ad da wasu suka yi addu’a tare da ni kuma suka karanta mini nassi ɗaya ko biyu. Ban da haka, ina samun ƙarfafa sa’ad da suka faɗi wani abu game da mijina da kuma sa’ad da suka saurare ni idan ina magana game da shi.”

16. (a) Wane tanadi ne muke bukatar mu yi wa wanda matarsa ko mijinta ya rasu? (b) Kamar yadda Yaƙub 1:27 ya nuna, wane hakki ne muke da shi?

16 Kamar yadda Rut ta kasance tare da Naomi, muna bukatar mu ci gaba da taimaka ma wanda matarsa ko mijinta ya rasu. Paula da aka ambata ɗazu ta ce: “Sa’ad da mijina ya rasu, mutane da yawa sun zo taimaka mini da kuma ta’azantar da ni. Da shigewar lokaci, kowa ya koma ayyukansa, amma rayuwata ta canja sosai. Yana da kyau idan mutane suka fahimci cewa mutumin da aka yi masa rasuwa zai bukaci taimako na dogon lokaci.” Gaskiya ne cewa dukanmu mun bambanta. Ba ya yi ma wasu wuya su saba da yanayinsu. Amma wasu, a duk lokacin da suka yi wani abu da suke yi dā da mijinsu ko matarsu, hakan yana iya sa su baƙin ciki. Yadda mutane ke makoki ya bambanta sosai. Mu tuna cewa Jehobah ya ba mu gata da kuma hakkin kula da waɗanda mijinsu ko kuma matarsu ta rasu.​—Karanta Yaƙub 1:27.

17. Me ya sa waɗanda mijinsu ko matarsu ta bar su suke bukatar taimako?

17 Mutanen da mijinsu ko matarsu ta bar su suna fama da baƙin ciki sosai. Wata mai suna Joyce da mijinta ya bar ta ya auri wata ta ce: “Da a ce mijina mutuwa ya yi, da hakan bai yi mini zafi kamar kashe aurenmu ba. In ya mutu a sanadiyyar hatsari ko kuma rashin lafiya, zan san cewa ba zaɓinsa ba ne. Amma a wannan yanayin, mijina ne ya zaɓi ya yashe ni. Hakan ya sa na ji an wulaƙanta ni sosai.”

18. Mene ne za mu iya yi don mu taimaka wa mutanen da mijinsu ko matarsu ta bar su?

18 Idan muka nuna alheri ma waɗanda mijinsu ko matarsu ta bar su, hakan zai tabbatar musu da cewa muna ƙaunar su. Yanzu da suka kaɗaita ne suke bukatar abokan kirki. (K. Mag. 17:17) Ta yaya za ka nuna musu cewa kai abokinsu ne? Kana iya gayyatar su gidanka don cin abinci. Ban da haka, kana iya zuwa shaƙatawa da kuma wa’azi da su. Wani abu kuma da za mu iya yi shi ne gayyatar su don mu yi ibada ta iyali tare. Idan ka yi waɗanda abubuwan, za ka faranta wa Jehobah rai domin yana taimaka ma waɗanda suke baƙin ciki da kuma “matan da mazansu suka mutu.”​—Zab. 34:18; 68:5.

19. Kamar yadda 1 Bitrus 3:8 ta nuna, mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

19 Nan ba da daɗewa ba, a lokacin da duniya ta zama aljanna, za mu “manta da” dukan matsalolinmu. Muna ɗokin ganin lokacin da “ba za a sāke tunawa da abubuwan dā ba, tunaninsu ma ba zai zo wa mutane ba.” (Isha. 65:​16, 17) Kafin wannan lokacin, bari mu riƙa taimaka wa juna kuma mu nuna ta furucinmu da kuma ayyukanmu cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu.​—Karanta 1 Bitrus 3:8.

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

^ sakin layi na 5 Lutu da Ayuba da kuma Naomi sun bauta wa Jehobah da aminci, amma sun fuskanci matsaloli a rayuwarsu. A wannan talifin, za mu tattauna darussan da za mu koya daga labarinsu. Ƙari ga haka, za mu tattauna dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu zama masu haƙuri, mu riƙa nuna ƙauna kuma mu ta’azantar da ’yan’uwanmu sa’ad da suke fuskantar matsaloli.

^ sakin layi na 13 An canja wasu sunaye a wannan talifin.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa yana fushi kuma yana maganganun da ba su dace ba, amma dattijo ya saurare shi. Sa’ad da hankalin ɗan’uwan ya kwanta, dattijon ya ba shi shawara.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Wasu ma’aurata sun ziyarci wani ɗan’uwa da matarsa ba ta daɗe da rasuwa ba. Ɗan’uwan yana ba su labarin abubuwan da shi da mamacin suka yi tare.