Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 23

‘Ku Lura Don Kada Wani Ya Kama Hankalinku’!

‘Ku Lura Don Kada Wani Ya Kama Hankalinku’!

“Ku lura fa, kada wani ya kama hankalinku ta wurin ilimin duniyar nan da kuma ilimin ruɗu na banza, waɗanda suka fito daga wurin al’adar ’yan Adam.”​—KOL. 2:8.

WAƘA TA 96 Kalmar Allah Tana da Tamani

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda Kolosiyawa 2:​4, 8 suka nuna, ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya rinjaye mu?

SHAIƊAN yana so mu daina bauta wa Jehobah. Don ya cim ma manufarsa, yana ƙoƙari ya canja ra’ayinmu ta wajen sa mu kasance da ra’ayinsa. Ƙari ga haka, yana ƙoƙari ya rinjaye mu ko kuma ya ruɗe mu mu bi shi ta wurin yin amfani da abubuwan da muke sha’awa.​—Karanta Kolosiyawa 2:​4, 8.

2-3. (a) Me ya sa ya kamata mu saurari gargaɗin da ke Kolosiyawa 2:8? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Da gaske ne cewa Shaiɗan zai iya yaudarar mu? Ƙwarai kuwa! Ku tuna cewa shafaffun Kiristoci ne Bulus ya rubuta wa gargaɗin da ke Kolosiyawa 2:​8, ba mutanen da ba sa bauta wa Allah ba. (Kol. 1:​2, 5) Idan waɗannan Kiristocin ba su yi hattara ba, Shaiɗan zai yaudare su kuma zai fi yin nasara a kanmu idan ba mu yi hattara ba. (1 Kor. 10:12) Me ya sa? Domin an jefo Shaiɗan duniya, kuma yana ƙoƙari ya yaudari bayin Allah masu aminci. (R. Yar. 12:​9, 12, 17) Ban da haka ma, muna zama a zamanin da halin mugaye da masu ruɗu yake “ƙara muni.”​—2 Tim. 3:​1, 13.

3 A wannan talifin, za mu tattauna yadda Shaiɗan yake amfani da “ruɗu na banza” don ya rinjaye mu. Za mu ga ‘dabaru’ uku da yake amfani da su. (Afis. 6:11) Sa’an nan a talifi na gaba, za mu bincika yadda za mu kāre kanmu don kada Shaiɗan ya rinjaye mu. Amma, bari mu fara tattauna darasin da za mu iya koya daga yadda Shaiɗan ya yaudari Isra’ilawa bayan da suka shiga Ƙasar Alkawari.

AN RINJAYE SU SU BAUTA WA GUNKI

4-6. Kamar yadda Maimaitawar Shari’a 11:​10-15 suka nuna, waɗanne sabbin hanyoyin yin noma ne Isra’ilawa suka bukaci su koya sa’ad da suka koma Ƙasar Alkawari?

4 Shaiɗan ya rinjayi Isra’ilawa su bauta wa gunki. Ta yaya ya yi hakan? Ya san suna bukatar abinci, sai ya yi ƙoƙari ya yi amfani da wannan damar don ya sa su yi nufinsa. Sa’ad da Isra’ilawa suka shiga Ƙasar Alkawari, sun bukaci su canja yadda suke noma. A lokacin da suke Masar, suna noma da ruwan da ke kogin Nilu, amma babu babban kogi a Ƙasar Alkawari. Saboda haka, Isra’ilawa za su bukaci ruwan sama da kuma raɓa don yin noma. (Karanta Maimaitawar Shari’a 11:​10-15; Isha. 18:​4, 5) Don haka, suna bukatar su koyi sabbin hanyoyin yin noma. Hakan ba zai yi musu sauƙi ba domin yawancin su da suka iya noma sun riga sun mutu a jeji.

Ta yaya Shaiɗan ya canja ra’ayin manoma Isra’ilawa? (Ka duba sakin layi na 4-6) *

5 Jehobah ya bayyana wa mutanensa cewa yanayinsu ya canja. Sai ya daɗa yi musu wannan gargaɗin da kamar ba shi da alaƙa da batun noma cewa: “Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku har ku juya ku bauta wa waɗansu alloli ku yi musu sujada.” (M. Sha. 11:​16, 17) Me ya sa Jehobah ya yi musu gargaɗi game da bauta wa allolin ƙarya sa’ad da yake magana a kan koyon sabbin hanyoyin yin noma?

6 Jehobah ya san cewa Isra’ilawa za su so su koyi sabbin hanyoyin yin noma daga mutanen da ke kewaye da su da ke bauta wa allolin ƙarya. Hakika, maƙwabtan Isra’ilawa sun iya noma sosai, kuma mutanen Allah za su iya koyon abubuwan da za su taimaka musu daga wurinsu. Amma suna iya yaudarar su. Ta yaya za su yi hakan? Manoma a ƙasar Kan’ana suna bauta wa Ba’al, kuma hakan ya shafi ra’ayinsu sosai. Sun gaskata cewa Ba’al ne mahaliccin sarari sama kuma shi ne yake sa a yi ruwan sama. Jehobah ba ya son irin wannan koyarwar ƙarya ta yaudari mutanensa. Amma, a kai a kai Isra’ilawa sun zaɓi su bauta wa Ba’al. (L. Ƙid. 25:​3, 5; Alƙa. 2:13; 1 Sar. 18:18) Yanzu ku lura da yadda Shaiɗan ya rinjayi Isra’ilawa.

DABARU UKU DA SHAIƊAN YA YI AMFANI DA SU

7. Ta yaya aka jarraba Isra’ilawa sa’ad da suka shiga Ƙasar Alkawari?

7 Ga dabara ta farko da Shaiɗan ya yi amfani da ita. Ya san cewa Isra’ilawa suna so a yi ruwan sama don su sami abinci, sai ya yi amfani da wannan sha’awar don ya rinjaye su. Ba a ruwan sama sosai a Ƙasar Alkawari daga ƙarshen watan Afrilu zuwa Satumba a kowace shekara. Don Isra’ilawa su sami amfanin gona, sun dogara da ruwan sama da ke somawa a watan Oktoba. Shaiɗan ya yaudare su su gaskata cewa idan suna so su sami ci gaba, wajibi ne su bi al’adun maƙwabtansu. Maƙwabtansu sun gaskata cewa suna bukatar su yi wasu bukukuwa don su sa allolinsu su kawo musu ruwan sama. Isra’ilawan da ba su da bangaskiya ga Jehobah sun gaskata cewa idan suka yi hakan, ba za a yi fari na dogon lokaci ba. Shi ya sa suka yi wasu bukukuwa ga Ba’al.

8. Wace dabara ta biyu ce Shaiɗan ya yi amfani da ita? Ka bayyana.

8 Shaiɗan ya yi amfani da dabara ta biyu don ya rinjayi Isra’ilawa. Ya yi amfani da sha’awoyin yin lalata. Al’ummai da ke wurin suna bauta wa allolin ƙarya ta wajen yin ayyukan lalata masu ban ƙyama. Hakan ya ƙunshi mata da maza da ke karuwanci a haikali. Ƙari ga haka, yin luwaɗi da wasu ayyukan lalata ba laifi ba ne a gare su! (M. Sha. 23:​17, 18; 1 Sar. 14:24) Waɗannan al’umman, sun gaskata cewa yin waɗannan bukukuwa yana ƙarfafa allolinsu su sa gonakinsu su ba da amfani sosai. Isra’ilawa da yawa sun yi sha’awar ayyukan lalata da waɗannan al’ummai suke yi. Saboda haka, suka zaɓi su bauta wa allolin ƙarya. Hakika, Shaiɗan ya rinjaye su sosai.

9. Kamar yadda Hosiya 2:​16, 17 suka nuna, ta yaya Shaiɗan ya sa Isra’ilawa suka mance da ra’ayin Jehobah?

9 Shaiɗan ya yi amfani da dabara ta uku. Ya sa Isra’ilawa su manta da ra’ayin Jehobah. A zamanin annabi Irmiya, Jehobah ya ce annabawan ƙarya sun sa bayinsa sun manta da sunansa saboda “Ba’al.” (Irm. 23:27) Wataƙila, mutanen Allah sun daina yin amfani da sunan Jehobah, sun sauya shi da suna Ba’al, wanda yake nufin “Mai Shi” ko “Ubangiji.” Hakan ya sa ya yi wa Isra’ilawa wuya su san bambancin da ke tsakanin Jehobah da Ba’al. Shi ya sa suke haɗa bautar Ba’al da na Jehobah.​—Karanta Hosiya 2:​16, 17.

DABARUN SHAIƊAN A YAU

10. Wace dabara ce Shaiɗan yake yin amfani da ita a yau?

10 Shaiɗan yana amfani da irin waɗannan dabarun a yau. Yana rinjayar mutane ta wajen yin amfani da abubuwan da suke sha’awa da ɗaukaka lalata da kuma sa mutane su manta da ra’ayin Jehobah. Za mu fara tattauna yadda Shaiɗan yake sa mutane su mance da ra’ayin Jehobah.

11. Ta yaya Shaiɗan yake sa mutane su manta da ra’ayin Jehobah?

11 Shaiɗan yana sa mutane su manta da ra’ayin Jehobah. Bayan mutuwar manzannin Yesu, wasu da suke da’awa su Kiristoci ne sun soma yaɗa koyarwar ƙarya. (A. M. 20:​29, 30; 2 Tas. 2:3) Waɗannan ’yan ridda suka soma hana mutane sanin cewa Jehobah ne Allah na gaskiya. Alal misali, sun cire sunan Allah a nasu Littafi Mai Tsarki kuma sun sauya shi da “Ubangiji.” Ta yin hakan, sun sa ya yi wa mutane wuya su ga yadda Jehobah ya bambanta da sauran “iyayengiji” da aka ambata a Nassosi. (1 Kor. 8:5) Suna kiran Jehobah da kuma Yesu “Ubangiji.” Hakan yana sa ya yi wuya a san cewa Jehobah da Ɗansa sun bambanta. (Yoh. 17:3) Hakan ne ya sa aka soma koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya, kuma wannan koyarwar ba ta cikin Kalmar Allah. Saboda haka, mutane da yawa sun gaskata cewa ba zai yiwu a san Allah ba. Hakan muguwar ƙarya ce sosai!​—A. M. 17:27.

Ta yaya Shaiɗan ya yi amfani da addinin ƙarya don ya ɗaukaka sha’awoyin lalata? (Ka duba sakin layi na 12) *

12. Mene ne addinan ƙarya suke ɗaukakawa, kuma mene ne sakamakon hakan kamar yadda aka bayyana a Romawa 1:​28-31?

12 Shaiɗan yana amfani da sha’awar mutane na yin lalata. A zamanin Isra’ilawa, Shaiɗan ya yi amfani da addinin ƙarya don ya ɗaukaka yin lalata. Hakan yake yi a yau. Addinan ƙarya sun amince da lalata kuma suna ɗaukaka wannan halin. Saboda haka, mutane da yawa da suke da’awa suna bauta wa Allah sun daina bin ƙa’idodinsa game da ɗabi’a. A wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta zuwa ga Romawa, ya nuna sakamakon ɗaukaka yin lalata. (Karanta Romawa 1:​28-31.) Dukan ayyukan lalata, har da luwaɗi suna cikin ayyukan “da bai kamata a yi ba.” (Rom. 1:​24-27, 32; R. Yar. 2:20) Yana da muhimmanci mu bi koyarwar da ke cikin Littafi Mai Tsarki!

13. Wace dabara ce kuma Shaiɗan yake amfani da ita?

13 Shaiɗan yana yin amfani da abubuwan da mutane suke sha’awa. Mukan so mu koyi sana’ar da za ta taimaka mana mu biya bukatunmu da na iyalanmu. (1 Tim. 5:8) Sau da yawa, mukan koyi wannan sana’ar a makaranta idan muka yi ƙoƙari sosai. Amma wajibi ne mu yi hattara. Domin a ƙasashe da yawa, ɗalibai suna koyon sana’a mai kyau a makarantu, amma duk da haka, ana koya musu hikimar mutanen duniya. Ana ƙarfafa ɗalibai su yi shakkar wanzuwar Allah kuma su daina amincewa da Littafi Mai Tsarki. Kuma ana koya musu cewa ’yan Adam sun soma wanzuwa ta juyin halitta. (Rom. 1:​21-23) Irin wannan koyarwar ta saɓa wa “hikimar Allah.”​—1 Kor. 1:​19-21; 3:​18-20.

14. Wane ra’ayi ne hikimar mutanen duniya take ɗaukakawa?

14 Mutane da suke bin hikimar wannan duniya ba sa amincewa da ƙa’idodin Jehobah amma suna ƙin su. Hikimar wannan duniyar ba ta ƙarfafa mutane su kasance da halayen da ruhun Allah ke sa mu koya, amma tana sa mu koyi “ayyukan” jiki. (Gal. 5:​19-23) Tana ƙarfafa mutane su zama masu fahariya, kuma hakan yana sa su zama “masu sonkansu.” (2 Tim. 3:​2-4) Allah ba ya so bayinsa su kasance da waɗannan halayen, maimakon haka, yana so su zama masu tawali’u. (2 Sam. 22:28) Wasu Kiristoci da suka je jami’a sun soma tunani kamar mutanen duniya maimakon kasancewa da ra’ayin Allah. Bari mu tattauna abin da zai faru idan ba mu mai da hankali ba.

Ta yaya hikimar mutanen duniya za ta iya shafan ra’ayinmu? (Ka duba sakin layi na 14-16) *

15-16. Mene ne ka koya daga abin da ya faru da wata ’yar’uwa?

15 Wata ’yar’uwa da ta yi shekara fiye da 15 tana hidima ta cikakken lokaci ta ce: “A matsayina na Mashaidiya da ta yi baftisma, na karanta da kuma ji labarin haɗarurruka da ke tattare da zuwa jami’a, amma ban saurara ba. Ina ganin wannan gargaɗin bai shafe ni ba.” Waɗanne matsaloli ne ta fuskanta? Ta ce: “Na ba da lokacina da duk kuzarina don yin karatu, har ba ni da lokacin yin addu’a. Hakan ya sa nakan gaji ainun kuma ba na iya yi wa mutane wa’azi. Gajiya takan sa ba na shirya taro da kyau. Na daina zuwa makarantar sa’ad da na gane cewa hakan yana shafan dangantakata da Jehobah.”

16 Ta yaya wannan makarantar ta shafi ra’ayinta? Ta ce: “Ina jin kunyar faɗa cewa makarantar ta koya mini mai da hankali ga kurakuran mutane, musamman na ’yan’uwa. Ta sa in riƙa ganin ya kamata su riƙa yin abubuwa kamar kamiltattu, kuma ta sa in riƙa ware kaina. Ya ɗau lokaci sosai kafin in daina yin hakan. Hakan ya koya min cewa ya dace mu riƙa saurarar gargaɗin da Jehobah yake ba mu ta ƙungiyarsa. Jehobah ya san ni sosai fiye da yadda na san kaina. Da a ce na saurari Jehobah da ban shiga cikin waɗannan matsalolin ba!”

17. (a) Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Ya kamata mu guji barin “ilimin duniyar nan da kuma ilimin ruɗu na banza” na Shaiɗan su rinjaye mu. Kada mu bar Shaiɗan ya yaudare mu da dabarunsa. (1 Kor. 3:18; 2 Kor. 2:11) Ban da haka, bai kamata mu bar Shaiɗan ya sa mu manta da Jehobah da yadda yake so mu bauta masa ba. Ya kamata mu bi ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a. Kuma kada mu bar Shaiɗan ya sa mu ƙi bin shawarar Jehobah. Amma, mene ne za mu yi idan muka lura cewa ra’ayin mutanen wannan duniyar yana shafan mu? A talifi na gaba, za mu koya yadda Kalmar Allah za ta taimaka mana mu kawar da halaye da kuma tunani masu wuyan bari.​—2 Kor. 10:​4, 5.

WAƘA TA 49 Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah

^ sakin layi na 5 Shaiɗan ya iya yaudarar mutane sosai. Ya yaudari mutane da yawa har suna ganin suna da ’yanci, amma sun riga sun zama bayinsa. A wannan talifin, za mu bincika dabaru da dama da Shaiɗan yake amfani da su don ya yaudari mutane.

^ sakin layi na 48 BAYANI A KAN HOTO: An jarraba Isra’ilawa da suke cuɗanya da Kan’anawa su bauta wa Ba’al kuma su yi lalata.

^ sakin layi na 51 BAYANI A KAN HOTO: An nuna wani fosta a coci da ya nuna cewa sun amince da luwaɗi.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Wata matashiya tana makarantar jami’a. Ita da abokan ajinsu sun bi ra’ayin malamansu cewa kimiyya da fasaha za su magance dukan matsalolin ’yan Adam. Bayan haka, a Majami’ar Mulki ba ta jin daɗin abin da ake jawabi a kai ba kuma ta ɓata fuska.