HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Yuni 2020

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 3-30 ga Agusta, 2020.

“A Kiyaye Sunanka da Tsarki”

Talifin Nazari na 23: 3-9 ga Agusta, 2020. Wane batu mai muhimmanci ne mutane da mala’iku suke fuskanta? Me ya sa batun yake da muhimmanci, kuma me matsayinmu a batun? Fahimtar amsoshin tambayoyin nan za su taimaka mana mu karfafa dangantakarmu da Jehobah.

‘Ka Ba Ni Zuciya Daya, Don In Girmama Sunanka’

Talifin Nazari na 24: 10-16 ga Agusta, 2020. A wannan talifin, za mu mai da hankali a kan addu’ar da Sarki Dauda ya yi da ke rubuce a littafin Zabura 86:​11, 12. Mene ne jin tsoron sunan nan Jehobah yake nufi? Me ya sa muke bukatar mu daraja wannan sunan? Ta yaya jin tsoron Allah zai taimaka mana mu guji yin abin da bai dace ba sa’ad da aka jarraba mu?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Halayen da aka ambata a Galatiyawa 5:​22, 23 su ne kaɗai halayen da ruhun Allah yake sa mu kasance da su?

‘Ni da Kaina Zan Nemi Tumakina’

Talifin Nazari na 25: 17-23 ga Agusta, 2020. Me ya sa wasu da suka yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah suka daina hakan? Yaya Allah yake ji game da su? Za a ba da amsoshin wadannan tambayoyin a wannan talifin. Za a kuma tattauna darasi da muka koya daga yadda Jehobah ya taimaka wa mutane a zamanin dā da suka daina bauta masa na dan lokaci.

“Ku Juyo Gare Ni”

Talifin Nazari na 26: 24-30 ga Agusta, 2020. Jehobah yana so mutanen da suka daina fita wa’azi da halartan taro su komo gare shi. Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi don mu karfafa wadanda suke so su “juyo” ga Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya taimaka musu.