Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 26

“Ku Juyo Gare Ni”

“Ku Juyo Gare Ni”

“Ku juyo gare ni, ni kuwa zan koma gare ku.”​—MAL. 3:7.

WAƘA TA 102 “Mu Taimaki Marasa Ƙarfi”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Yaya Jehobah yake ji idan tunkiyarsa ta koma gare shi?

KAMAR yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, Jehobah ya kamanta kansa da makiyaya da ke kula da kowanne tumakinsa. Kuma yana neman waɗanda suka bijire. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa da suka bijire cewa: “Ku juyo gare ni, ni kuwa zan koma gare ku.” Mun san cewa yana jin hakan har ila domin ya ce: “Ba na canjawa.” (Mal. 3:​6, 7) Yesu ya ce Jehobah da kuma mala’iku suna farin ciki sosai sa’ad da ko da mutum ɗaya ne da ya bijire ya koma ga Jehobah.​—Luk. 15:​10, 32.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Bari mu tattauna kwatanci uku da Yesu ya yi game da yadda za mu taimaka wa waɗanda suka bijire. Za mu tattauna wasu halaye da muke bukatar mu kasance da su don mu iya taimaka wa tumakin Jehobah su komo gare shi. Kuma za mu ga dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu taimaka wa waɗanda suka bijire su komo ga Jehobah.

KA NEMI KUƊIN DA YA ƁACE

3-4. Me ya sa matar da aka ambata a Luka 15:​8-10 ta nemi kuɗin da ya ɓace?

3 Muna bukatar mu sa ƙwazo don mu nemi waɗanda suke so su komo ga Jehobah. A kwatancin Yesu da ke littafin Luka, ya yi magana game da wata mata da ta ɓatar da kuɗi. Abu mai muhimmanci a wannan kwatanci shi ne yadda matar ta nemi kuɗin.​—Karanta Luka 15:​8-10.

4 Yesu ya kwatanta yadda matar ta ji sa’ad da ta sami kuɗin da ta ɓatar. A zamanin Yesu, iyaye sukan ba ’yarsu tsabar kuɗi guda goma a ranar da ta yi aure. Wataƙila matar ta daraja kuɗin ne domin yana cikin waɗanda iyayenta suka ba ta. Matar ta ɗauka cewa kuɗin ya faɗi a ƙasa. Saboda haka, sai ta kunna fitila kuma ta nemi kuɗin, amma ba ta samu ba. Fitilar ba ta da haske sosai, don haka, ba ta sami kuɗin azurfar ba. A ƙarshe, sai ta share gidan gabaki ɗaya. Bayan ta gama share gidan, sai ta ga kuɗin a cikin shara yana ƙyalli. Ta yi farin cikin samun kuɗin! Sai ta kira abokanta da maƙwabtanta don su taya ta murna.

5. Me ya sa yake da wuya mu nemi waɗanda suka bijire?

5 Kamar yadda kwatancin Yesu ya nuna, muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu sami kuɗin da ya ɓace. Hakazalika, muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu nemi waɗanda suka bijire. Wataƙila ya ɗau shekaru da yawa da suka daina halartan taro da fita wa’azi. Ƙila sun ƙaura zuwa wani wuri da ’yan’uwa ba su san su ba. Amma muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa waɗannan ’yan’uwan suna so su komo ga Jehobah. Suna so su sake bauta wa Jehobah tare da bayinsa, amma suna bukatar taimakonmu.

6. Ta yaya kowa a ikilisiya zai taimaka don a nemi waɗanda suka bijire?

6 Wane ne zai iya taimaka wa waɗanda suka daina fita wa’azi da halartan taro? Duk masu shela a ikilisiya za su iya taimaka wa don a nemi waɗanda suka bijire, har da dattawa da majagaba da kuma dangin ’yan’uwan da suka bijire. Shin akwai wani abokinka ko dangin da ya bijire? Ka taɓa haɗuwa da wani da ya bijire a lokacin da kake wa’azi gida-gida ko kuma a wurin da jama’a suke? Ka bayyana wa mutumin cewa idan zai so wani ya ziyarce shi, za ka ba dattawan ikilisiyarku adireshinsa ko kuma lambar wayarsa.

7. Me ka koya daga furucin wani dattijo mai suna Thomas?

7 Waɗanne matakai ne dattawa za su iya ɗauka don su nemi waɗanda suke so su komo ga Jehobah? Ka yi la’akari da labarin wani dattijo mai suna Thomas * da ke zama a ƙasar Sifen, kuma ya taimaka wa mutane fiye da 40 su komo ga Jehobah. Thomas ya ce: “Da farko, ina tambayar ’yan’uwa cewa ko sun san wuraren da waɗanda suka bijire suke da zama. Ko kuma in tambaye su ko sun san wasu da suka daina halartan taro. Yawancin ’yan’uwa a ikilisiya suna farin cikin taimakawa domin hakan yana ba su damar saka hannu a wannan aikin. Daga baya, idan na ziyarci waɗanda suka bijire, ina tambayar su yadda yaransu da kuma iyalinsu suke. Wasu da suka bijire suna kawo yaransu taro a dā kuma wataƙila yaran masu shela ne a lokacin. Su ma suna bukatar taimako.”

KA TAIMAKA WA TUMAKIN JEHOBAH SU KOMO GARE SHI

8. A kwatancin mubazzarin ɗa da ke Luka 15:​17-24, ta yaya mahaifin ya bi da ɗansa?

8 Waɗanne halaye ne muke bukatar mu kasance da su idan muna so mu taimaka wa waɗanda suke so su komo ga Jehobah? Ka yi la’akari da wasu darussa da za mu iya koya daga kwatancin mubazzarin ɗa da Yesu ya ba da. (Karanta Luka 15:​17-24.) Yesu ya bayyana cewa daga baya yaron ya dawo hankalinsa kuma ya koma gida. Mahaifin ya ruga a guje don ya marabci ɗan kuma ya tabbatar masa da cewa yana ƙaunar sa. Zuciyar yaron ta dame shi don abin da ya yi, kuma yana ganin cewa bai cancanci Uban ya marabce shi ba. Mahaifin ya tausaya wa ɗan domin ya gaya masa abin da ke zuciyarsa. Mahaifin ya ɗauki mataki don ya tabbatar wa yaron da cewa ya marabce shi a matsayin ɗansa da yake ƙauna ba ma’aikaci ba. Don ya nuna cewa yana ƙaunar ɗansa kuma ya marabce shi, mahaifin ya shirya a yi liyafa kuma ya ba wa yaron da ya dawo tufafi mai kyau.

9. Waɗanne halaye ne muke bukata don mu iya taimaka wa waɗanda suka bijire? (Ka duba akwatin nan “ Taimako Don Waɗanda Suke So Su Dawo.”)

9 Jehobah yana kamar mahaifi na wannan kwatancin. Yana ƙaunar ’yan’uwa maza da mata da suka bijire kuma suke so su komo gare shi. Ta yin koyi da Jehobah, za mu iya taimaka musu su komo gare shi. Don mu taimaka musu, muna bukatar haƙuri da tausayi da nuna jinƙai da kuma ƙauna. Me ya sa muke bukatar waɗannan halayen, kuma ta yaya za mu yi hakan?

10. Me ya sa muke bukatar haƙuri sa’ad da muke taimaka wa wani ya kusaci Jehobah?

10 Muna bukatar haƙuri domin wanda ya bijire yana bukatar lokaci don ya sake ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Mutane da yawa da suka bijire sun ce dattawa da kuma wasu a ikilisiya sun ziyarce su sau da yawa kafin su komo ga Jehobah. Wata ’yar’uwa mai suna Nancy da ke kudu maso gabashin Asiya ta ce: “Wata ƙawata na kud da kud a ikilisiya ta taimaka mini sosai. Tana ƙauna ta kamar yayarta. Ta tuna mini abubuwa masu kyau da muka yi tare a dā. Ta saurare ni sosai sa’ad da nake gaya mata abin da ke zuciyata kuma takan ba ni shawara. Ta nuna cewa ita abokiyar kirki ce kuma tana a shirye ta taimaka mini a kowane lokaci.”

11. Me ya sa muke bukatar mu ji tausayin waɗanda aka ɓata musu rai?

11 Idan aka ɓata wa mutum rai, zai yi masa zafi kamar an ji masa rauni. Jin tausayin sa yana kamar magani da zai iya sa mutumin ya warke. Wasu da suka bijire suna fushi domin abin da wani a ikilisiya ya yi musu shekaru da yawa da suka shige. Saboda haka, ba sa so su komo ga Jehobah domin suna ganin an yi musu rashin adalci. Suna bukatar wanda zai saurare su kuma ya fahimci yadda suke ji. (Yaƙ. 1:19) Wata ’yar’uwa mai suna María da ta taɓa bijirewa ta ce: “Na bukaci wanda zai saurare ni, ya ƙarfafa ni, ya kuma taimaka mini.”

12. Ka kwatanta yadda ƙaunar Jehobah yake jawo waɗanda suka bijire.

12 A Littafi Mai Tsarki, an kwatanta ƙauna da Jehobah yake yi wa mutanensa da igiya. Ta yaya ƙaunar Allah ta yi kama da igiya? Ka yi la’akari da wannan misalin: A ce ka faɗi a cikin teku. Ruwan yana da zurfi sosai da kuma sanyi. Kana nitsewa, sai wani daga cikin jirgin ruwa ya jefo maka abin da zai taimaka maka domin kada ka nitse. Ka yi farin ciki sosai! Amma duk da haka, kana bukatar taimako don ka tsira. Kana bukata mutanen da ke jirgin su jefo maka igiyar da za ka riƙe don su fitar da kai daga tekun zuwa jirgin ruwan. Jehobah ya ce game da Isra’ilawan da suka bijire: “Na jawo su wurina da igiyoyin alheri, na ɗaure su da ƙauna.” (Hos. 11:4) Haka ma Allah yake ji a yau game da waɗanda suka bijire kuma suke fama da matsaloli. Yana so su san cewa yana ƙaunar su kuma yana so ya jawo su kusa da shi. Jehobah yana iya yin amfani da kai don ya nuna musu cewa yana ƙaunar su.

13. Ta yaya labarin Pablo ya nuna cewa ƙaunar mu za ta iya taimaka wa mutanen da suka bijire?

13 Yana da muhimmanci mu tabbatar wa waɗanda suka bijire cewa Jehobah da kuma mu muna ƙaunar su. Wani mai suna Pablo da aka ambata a talifin da ya gabata ya yi fiye da shekara 30 ba ya bauta wa Jehobah. Ya ce: “Wata rana da na fita daga gida, na haɗu da wata ’yar’uwa tsohuwa mai alheri. Ta nuna tana ƙauna ta kuma ta yi mini magana da ya ratsa zuciyata. Sai na soma zub da hawaye kamar yaro ƙarami. Na gaya mata cewa kamar dai Jehobah ne ya aiko ta ta yi mini magana. A wannan lokacin ne na yanke shawarar komawa ga Jehobah.”

KU TAIMAKA WA MARASA ƘARFI

14. Kamar yadda kwatancin da ke Luka 15:​4, 5 ta nuna, mene ne makiyayin ya yi sa’ad da ya sami tunkiyar da ta ɓata?

14 Muna bukatar mu riƙa taimaka da kuma ƙarfafa waɗanda suka bijire. Kamar mubazzarin ɗa a kwatancin Yesu, zuciyarsu tana iya damunsu na dogon lokaci. Da yake suna duniyar Shaiɗan, babu shakka ba su da dangantaka da Jehobah kamar dā. Muna bukatar mu taimaka musu su ƙarfafa bangaskiyarsu ga Jehobah. A kwatancin tumaki da Yesu ya ba da, ya bayyana yadda makiyayin ya ɗora tunkiyar a kafaɗarsa kuma ya kai ta wurin garken. Makiyayin ya yi amfani da lokaci da kuzari sosai don ya nemi tunkiyar. Amma ya san cewa tunkiyar tana bukatar taimako. Ba ta da ƙarfin yin tafiya zuwa wurin da sauran tumakin suke, don haka, sai ya ɗauke ta.​—Karanta Luka 15:​4, 5.

15. Ta yaya za mu taimaka wa waɗanda suke so su komo ga Jehobah? (Ka duba akwatin nan “ Kayan Aiki Mai Kyau.”)

15 Muna bukatar mu yi amfani da lokacinmu da kuma kuzarinmu don mu taimaka wa waɗanda suka bijire su magance matsalar da ke hana su komowa ga Jehobah. Ruhun Jehobah da Kalmarsa da kuma littattafan ƙungiyar Jehobah, za su iya taimaka musu su sake ƙulla dangantaka da shi. (Rom. 15:1) Me zai taimaka mana mu yi hakan? Wani dattijo da ya manyanta ya ce: “Yawancin mutanen da suka bijire suna bukatar a sake yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su sa’ad da suke so su komo ga Jehobah.” * Saboda haka, idan dattawa suka ce ka yi nazari da ɗaya cikin mutanen, ka amince da hakan da hannu biyu-biyu. Dattijon ya daɗa da cewa: “Ya kamata mai shelan da zai gudanar da nazarin ya zama mai fara’a don ya yi wa ɗalibin sauƙi ya furta yadda yake ji.”

ANA FARIN CIKI A SAMA DA DUNIYA

16. Ta yaya muka san cewa mala’iku suna taimaka mana?

16 Da akwai misalai da yawa da suka nuna cewa mala’iku suna taimaka mana mu nemi mutanen da suka daina fita wa’azi da halartan taro da suke so su komo ga Jehobah. (R. Yar. 14:6) Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Silvio daga ƙasar Ecuador da ya daina fita wa’azi da halartan taro ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya dawo ƙungiyarsa. A lokacin da yake addu’ar, dattawa biyu sun ƙwanƙwasa ƙofarsa. Sa’ad da suka ziyarce shi sun yi farin cikin soma taimaka masa ya komo ga Jehobah.

17. Yaya za mu ji idan mun taimaka wa mutanen da suka bijire?

17 Za mu yi farin ciki sosai idan muka taimaka wa mutanen da suka bijire su komo ga Jehobah. Wani majagaba mai suna Salvador da yake taimaka wa mutanen da suka bijire ya ce: “A wasu lokuta, ina zub da hawaye don farin ciki. Ina farin ciki cewa na yi aiki tare da Jehobah wajen taimaka wa ɗaya cikin tumakinsa ya komo gare shi.”​—A. M. 20:35.

18. Idan ka daina cuɗanya da mutanen Jehobah, wane tabbaci ne kake da shi?

18 Idan ka daina cuɗanya da bayin Jehobah, ka kasance da tabbaci cewa har yanzu, Jehobah yana ƙaunar ka kuma yana so ka komo gare shi. Kana bukatar ka ɗau wasu matakai don ka komo ga Jehobah. Kamar mahaifi a kwatancin Yesu, Jehobah yana jira ka komo gare shi kuma zai marabce ka sosai.

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

^ sakin layi na 5 Jehobah yana so mutanen da suka daina fita wa’azi da halartan taro su komo gare shi. Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi don mu ƙarfafa waɗanda suke so su “juyo” ga Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya taimaka musu.

^ sakin layi na 7 An canja wasu sunaye.

^ sakin layi na 15 Za a iya taimaka wa wasu da suka bijire, ta wajen yin nazarin wasu sassan littafin nan Ku Ci Gaba da Ƙaunar Allah. Wasu sun amfana daga littafin nan Ka Kusaci Jehovah. Kwamitin Hidima na Ikilisiya ne zai yanke shawara a kan wanda ya cancanci ya gudanar da nazarin.

^ sakin layi na 68 BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ’yan’uwa uku suna taimaka ma wani da yake so ya komo ga Jehobah. Sun yi hakan ta wajen kiransa a waya, da tabbatar masa da cewa Jehobah yana ƙaunar sa da kuma saurarar sa yayin da yake faɗin abin da ke zuciyarsa.