Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mu Riƙa Bin Ja-goranci a Yau

Mu Riƙa Bin Ja-goranci a Yau

MUN gaskata cewa Jehobah yana wa mutanensa ja-goranci kuma yana tanadar da abin da suke bukata don su kusace shi a wannan ‘kwanaki na ƙarshe.’ (2 Tim. 3:1) Amma muna bukatar mu riƙa yi wa Jehobah biyayya. Muna iya kwatanta yanayinmu da na Isra’ilawa a jeji. Suna bukatar su ɗau mataki sa’ad da suka ji ƙarar kakaki da aka busa.

Jehobah ya gaya wa Musa ya ƙera kakaki biyu na azurfa don “a kira taron jama’a, ko kuma a yi shelar tashi daga zango.” (L. Ƙid. 10:2) Ya kamata firistocin su busa kakakin a hanyoyi dabam-dabam don mutanen su san abin da suke bukata su yi. (L. Ƙid. 10:​3-8) A yau, ana ba mutanen Allah umurni a hanyoyi dabam-dabam. Ka yi la’akari da waɗannan hanyoyi uku da suke tuna mana da busa kakaki a zamanin dā. Ana gayyatar mutanen Allah a yau zuwa manyan taro da kuma horar da dattawa. Ban da haka, ana canja tsarin da ake bi a dukan ikilisiyoyi.

GAYYATA ZUWA MANYAN TARO

Firistoci suna busa kakaki guda biyun sa’ad da Jehobah yake son “jama’a gaba ɗaya” su taru a ta gabas na mazaunin. (L. Ƙid. 10:3) Dukan ƙabilu da aka raba zuwa kashi huɗu da suka kafa tentunansu kusa da mazauni suna jin ƙarar kakakin. Waɗanda suke kusa da ƙofar shiga mazaunin za su zo nan da nan. Wasu suna da nisa, saboda haka za su bukaci ƙarin lokaci da ƙoƙartawa kafin su isa. Ko da mene ne yanayinsu, Jehobah yana so dukansu su zo taron kuma su amfana.

A yau, ba ma taro a mazauni, amma ana gayyatar mu zuwa taron da mutanen Allah suke yi. Hakan ya ƙunshi taron yanki da wasu taro na musamman. A waɗannan taro, ana koyar da mu da kuma ba mu umurni mai muhimmanci. Mutanen Jehobah suna samun koyarwa iri ɗaya a dukan ƙasashe. Saboda haka, dukan waɗanda suke halartan waɗannan taro suna cikin babban rukuni masu farin ciki. Wasu suna yin tafiya mai nisa sosai fiye da wasu. Amma dukan waɗanda suka halarci wannan taron sun ga cewa ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Waɗanda suke wurare masu nisa za su iya halartan waɗannan manyan taron kuwa? Da taimakon na’urori, mutane da yawa suna amfana daga waɗannan taro. Ban da haka, suna ɗauka cewa suna cikin waɗanda suka halarci waɗannan manyan taro. Alal misali, a lokacin da wani wakili daga hedkwatarmu ya ziyarci reshen ofishin da ke ƙasar Bini, ’yan’uwa da ke garin Arlit a Nijar sun saurari jawabinsa. ’Yan’uwa 21 da waɗanda suke son saƙonmu ne suka halarta. Ko da yake suna wuri mai nisa, suna tare da ’yan’uwansu a wannan babban taro da mutane 44,131 suka halarta. Wani ɗan’uwa ya rubuto: “Mun gode muku da dukan zuciyarmu cewa mun sami damar saurarar wannan taron ta na’ura. Hakan ya nuna cewa kuna tuna da mu kuma ya ratsa zuciyarmu.”

UMURNI GA DATTAWA

Sa’ad da firistoci suka busa kakaki ɗaya, “shugabanni ne” kawai za su taru a tantin taro. (L. Ƙid. 10:4) A wurin za a ba su umurni kuma Musa ya horar da su. Hakan zai taimaka musu su idar da ayyukansu. Idan kana cikin waɗannan shugabannin, babu shakka za ka yi iya ƙoƙarinka don ka halarci taron don ka amfana.

A yau, dattawa ba “shugabanni” ba ne, kuma ba sa iko a kan mutanen Allah. (1 Bit. 5:​1-3) Amma suna yin iya ƙoƙarinsu don su riƙa ƙarfafa su. Saboda haka, ba sa ɓata lokaci sa’ad da aka gayyace su samun ƙarin horarwa, kamar halartan Makarantar Hidima ta Mulki. A wannan makarantar, dattawa suna koyan yadda za su riƙa yin ayyukan ikilisiya da kyau. Hakan yana sa dattawa da kuma ’yan’uwa su kusaci Jehobah. Za ka amfana sosai ko da ba ka halarci kowanne cikin waɗannan makarantun ba don waɗanda suka je za su yi amfani da abin da suka koya su taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya.

SA’AD DA AKA CE MU YI CANJE-CANJE

A wani lokaci firistoci a Isra’ila suna busa kakaki don su ba da umurni. Ta hakan suna sanar cewa Jehobah yana so dukan mutane su ƙaura. (L. Ƙid. 10:​5, 6) Sa’ad da mutane suka tashi daga zango, suna yin hakan bisa tsari amma suna aiki tuƙuru don su cim ma wannan. A wasu lokuta, wataƙila wasu Isra’ilawa sun yi jinkirin ƙaura. Me ya sa?

Wataƙila wasu suna ganin ana yawan ba da umurnin ƙaura a kai a kai ba zato. Littafi Mai Tsarki ya ce: A “wani lokaci, ƙunshin girgijen zai tsaya daga yamma zuwa safe kawai.” A wani kuma zai yi ‘kwanaki biyu ne, ko wata ɗaya ne, ko shekara ɗaya.’ (L. Ƙid. 9:​21, 22) Sau nawa ne suke ƙaura? Littafin Ƙidaya sura 33 ya ambata wurare 40 da Isra’ilawa suka kafa zango.

A wasu lokuta, Isra’ilawa suna kafa zango a wuri mai inuwa. Yin hakan zai sa su yi farin ciki da yake suna “babban dajin nan mai ban tsoro.” (M. Sha. 1:19) Amma wasu za su iya tunani cewa sake ƙaura zai sa su koma wurin da ba za su ji daɗin zama ba.

Muddin kashi ɗaya suka soma ƙaura, sauran suna bukatar su yi haƙuri har sai lokacin su ya zo. Dukansu ne za su ji ƙarar kakakin ƙaura, amma ba dukansu ba ne za su ƙaura a lokaci ɗaya ba. Kakakin ba da umurni yana nuna cewa ya kamata zuriyar da suka yi zango a gabas, wato zuriyar Yahuda da Issakar da Zebulun su tashi. (L. Ƙid. 2:​3-7; 10:​5, 6) Bayan sun ƙaura, firistocin suna sake busa kakakin don su sanar da zuriya ta uku da suke ta kudu su ƙaura. Firistocin za su ci gaba da yin hakan har sai dukan al’ummar ta ƙaura.

Wataƙila yana yi maka wuya ka amince da wasu canje-canje da aka yi a ƙungiyar Jehobah. Mai yiwuwa kana ganin cewa canje-canjen sun yi yawa. Ko kuma ƙila ka saba da wasu abubuwa da ake yi a dā kuma ba ka son a canja. Mai yiwuwa ya yi maka wuya ka kasance da haƙuri yayin da kake sabawa da canjin, kuma ya ɗau lokaci kafin ka saba. Duk da haka, idan muka ƙoƙarta muka bi canje-canje da aka yi za mu amfana kuma Allah zai yi farin ciki da mu.

A zamanin Musa, Jehobah ya ja-goranci miliyoyin mutane a cikin jeji. Da a ce bai ja-gorance su ba da kuma kula da su, da ba su tsira ba. A yau, Jehobah yana mana ja-goranci a wannan mugun kwanaki na ƙarshe. Yana taimaka mana mu kusace shi kuma mu riƙe bangaskiyarmu. Saboda haka, bari dukanmu mu ƙuduri niyyar bin umurni yadda Isra’ilawa suka yi sa’ad da suka ji ƙarar kakaki!