Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 25

‘Ni da Kaina Zan Nemi Tumakina’

‘Ni da Kaina Zan Nemi Tumakina’

“Ni da kaina zan bi baya, in nemi tumakina, kuma zan samo su. . . . I, zan yi kiwon tumakina.”​—EZEK. 34:​11, 16.

WAƘA TA 105 “Allah Ƙauna Ne”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa Jehobah ya gwada kansa da mace mai jego?

JEHOBAH ya yi wata tambaya a zamanin annabi Ishaya cewa: “Mace za ta iya mantawa da jaririnta ne?” Sai Allah ya gaya wa mutanensa cewa zai “yiwu mace ta manta da ɗan cikinta, amma ni kam, ba zan taɓa mantawa da ke” ba. (Isha. 49:15) Jehobah ba ya yawan gwada kansa da mahaifiya, amma ya yi hakan a wannan lokacin. Jehobah ya yi amfani da yadda mahaifiya take ƙaunar ɗanta don ya bayyana yadda yake ji game da bayinsa. Yawancin mata masu yara suna da irin ra’ayin wata ’yar’uwa mai suna Jasmin da ta ce: “Sa’ad da kake renon jaririnka, kana ƙulla dangantaka ta musamman da yaron muddar ranka.”

2. Yaya Jehobah yake ji sa’ad da ɗaya cikin bayinsa ya bijire?

2 Jehobah ya san lokacin da ɗaya cikin bayinsa ya daina fita wa’azi da kuma halartan taro. Kuma babu shakka cewa yana baƙin ciki sa’ad da ya ga dubban bayinsa sun daina yin waɗannan abubuwa * a kowace shekara.

3. Mene ne Jehobah yake so?

3 Da yawa cikin waɗannan ’yan’uwan suna komowa ga Jehobah, kuma muna farin ciki sa’ad da suka yi hakan! Jehobah yana so su komo, mu ma muna so su yi hakan. (1 Bit. 2:25) Ta yaya za mu taimaka musu su komo? Kafin mu ba da amsar, zai dace mu san abin da ya sa wasu suka daina halartan taro da kuma fita wa’azi.

ME YA SA WASU SUKA DAINA BAUTA WA JEHOBAH?

4. Ta yaya aiki zai iya shafan mutum?

4 Wasu sun shagala da aikinsu. Wani ɗan’uwa mai suna Hung * da ke zama a kudu maso gabashin Asiya ya ce: “Nakan shagala sosai a aikina, kuma na yi tunani cewa zan bauta wa Jehobah da ƙwazo idan na yi arziki. Saboda haka, sai na ƙara sa’o’in da nake aiki. Hakan ya sa ya yi min wuya in riƙa halartan dukan taro, kuma daga baya, na daina gabaki ɗaya. Shaiɗan yana amfani da abin duniya a hankali-hankali don ya sa mutane su daina bauta wa Allah.”

5. Ta yaya matsaloli masu yawa suka shafi wata ’yar’uwa?

5 Wasu ’yan’uwa suna da matsaloli da yawa da ke sa su sanyin gwiwa. Wata ’yar’uwa mai suna Anne daga Birtaniya tana da yara biyar, kuma ta ce: “Ɗaya cikin yarana naƙasasshe ne. Da shigewar lokaci, an yi wa ’yata yankan zumunci kuma wani cikin yarana ya soma taɓin hankali. Na yi baƙin ciki sosai, har na daina halartan taro da fita wa’azi.” Muna tausaya wa Anne da iyalinta da wasu da suke cikin irin wannan yanayin!

6. Ta yaya ƙin bin abin da ke littafin Kolosiyawa 3:13 zai sa mutum ya daina bauta wa Jehobah?

6 Karanta Kolosiyawa 3:13. Wasu ’yan’uwa suna fushi don wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ɓata musu rai. Manzo Bulus ya fahimci cewa a wasu lokuta wani ɗan’uwa yana iya yi mana “laifi.” Ban da haka, ana iya yi mana rashin adalci. Idan ba mu mai da hankali ba, muna iya riƙe ’yan’uwan a zuciya. Yin fushi yana iya sa mutum ya daina cuɗanya da mutanen Jehobah. Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Pablo da ke Amirka ta Kudu. Ya rasa gatar da yake da shi a ikilisiya don an ɗora masa sharri. Ta yaya hakan ya shafe shi? Pablo ya ce, “Na yi fushi sosai kuma a hankali na daina bauta wa Jehobah.”

7. Mene ne zai iya faruwa da mutumin da zuciyarsa take damunsa domin wani laifi da ya yi?

7 Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani a dā, yana iya yin baƙin ciki na dogon lokaci don yana ganin cewa Allah ba zai taɓa ƙaunar sa kuma ba. Ko da ya tuba kuma aka nuna masa jinƙai, yana iya ganin cewa bai cancanci yin cuɗanya da mutanen Allah ba. Haka ne wani ɗan’uwa mai suna Francisco ya ji. Ya ce: “An yi mini horo don na yi lalata, ko da yake da farko na ci gaba da halartan taro, na yi sanyin gwiwa kuma na soma ganin cewa ban cancanci yin cuɗanya da mutanen Jehobah ba. Zuciyata ta soma damuna kuma na soma ganin cewa Jehobah bai gafarta mini ba. Da shigewar lokaci, na daina halartan taro da fita wa’azi.” Yaya kake ji game da ’yan’uwa da suke cikin yanayi da aka ambata a nan? Kana jin tausayinsu kuwa? Mafi muhimmanci, ta yaya Jehobah yake ji game da su?

JEHOBAH YANA ƘAUNAR BAYINSA

Makiyayi Ba’isra’ile yana kula da tunkiyar da ta ɓata (Ka duba sakin layi na 8-9) *

8. Jehobah yana mantawa da waɗanda suka bijire kuwa? Ka bayyana.

8 Jehobah ba ya mantawa da waɗanda suka bauta masa a dā amma suka daina tarayya da mutanensa na ɗan lokaci. Kuma ba zai manta da su don abubuwan da suka yi a hidimarsa ba. (Ibran. 6:10) Annabi Ishaya ya yi wani kwatanci mai kyau don ya nuna yadda Jehobah yake kula da mutanensa. Ya ce: “Yana ciyar da tumakinsa kamar yadda makiyayi yake yi. Yana tara ’yan tumakin a hannuwansa, ya rungume su a ƙirjinsa.” (Isha. 40:11) Ta yaya Jehobah, Babban Makiyayi yake ji sa’ad da ɗaya cikin bayinsa ya daina bauta masa? Yesu ya nuna yadda Jehobah yake ji sa’ad da ya tambayi almajiransa: “Me kake tsammani, idan makiyayi yana da tumaki guda ɗari, sai ɗaya daga cikinsu ta ɓata, ba zai bar sauran casa’in da taran a tuddai suna kiwo ya je neman ɗayarsu da ta ɓata ba? Kuma idan ya same ta, gaskiya ina faɗa muku, murnar da yake yi a kanta, ta fi ta casa’in da taran da ba su ɓata ba.”​—Mat. 18:​12, 13.

9. Ta yaya makiyaya nagari a zamanin dā suke kula da tumakinsu? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

9 Me ya sa ya dace mu kwatanta Jehobah da makiyayi? Domin a zamanin dā, makiyayi nagari yana kula da tumakinsa sosai. Alal misali, Dauda ya yi faɗa da zaki da dabbar beyar don ya kāre tumakinsa. (1 Sam. 17:​34, 35) Makiyayi nagari zai san lokacin da tunkiyarsa guda ta ɓata. (Yoh. 10:​3, 14) Irin wannan makiyayin zai bar tumaki 99 a gidan dabbobi ko kuma ya gaya wa wasu makiyaya su kula da su don ya tafi ya nemi tunkiyar da ta ɓata. Yesu ya yi amfani da wannan kwatanci don ya koya mana darasi mai muhimmanci: “Ba nufin Uban ku wanda yake cikin sama ba ne ɗaya daga cikin yara ƙanana nan ya ɓata.”​—Mat. 18:14.

Wani makiyayi a Isra’ila a dā yana kula da tunkiyarsa da ta bijire (Ka duba sakin layi na 9)

JEHOBAH YANA NEMAN TUMAKINSA

10. Kamar yadda Ezekiyel 34:​11-16 suka nuna, mene ne Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi wa tumakinsa da suka ɓata?

10 Jehobah yana ƙaunar kowannenmu har da “yara ƙanana” da suka bijire daga garkensa. Ta wurin annabi Ezekiyel, Allah ya yi alkawari cewa zai nemi tumakinsa da suka ɓata kuma ya taimaka musu su sake ƙulla dangantaka da shi. Jehobah ya tsara matakan da zai ɗauka don ya cece su, irin matakan da makiyayi a Isra’ila zai ɗauka don ya nemi tunkiyar da ta ɓace. (Karanta Ezekiyel 34:​11-16.) Da farko, makiyayin zai nemi tunkiyar, kuma hakan yana iya ɗaukan lokaci da kuzari. Sa’an nan, muddin ya samo ta, makiyayin zai dawo da ita garken. Ƙari ga haka, idan tunkiyar ta ji rauni ko kuma tana jin yunwa, makiyayin zai yi mata jinya, ya kula da ita kuma ya ciyar da ita. Dattawa da suke kula da “garken Allah” suna bukatar su ɗauki irin matakan nan don su taimaka ma wani da ya daina bauta wa Jehobah. (1 Bit. 5:​2, 3) Dattawa suna neman su don su taimaka musu su dawo ikilisiya, kuma su sake zama abokan Jehobah. *

11. Mene ne makiyayi nagari ya sani?

11 Makiyayi nagari ya san cewa tunkiya za ta iya ɓacewa. Idan tunkiyar ta ɓata, makiyayin ba zai yi mata horo ba. Ka yi la’akari da misalin da Allah ya kafa sa’ad da yake taimaka wa wasu cikin bayinsa da suka ɗan bijire.

12. Ta yaya Jehobah ya bi da Yunana?

12 Annabi Yunana ba ya so ya yi aikin da Jehobah ya ba shi. Amma, Jehobah bai ƙi Yunana ba. Kamar makiyayi nagari, Jehobah ya cece shi kuma ya taimaka masa ya samu ƙarfin da yake bukata don ya yi aikin da aka ba shi. (Yona 2:7; 3:​1, 2) Daga baya, Allah ya yi amfani da wani ɗan tsiro don ya taimaka wa Yunana ya fahimci cewa ran ’yan Adam yana da daraja. (Yona 4:​10, 11) Wane darasi ne muka koya? Bai kamata dattawa su yi saurin yasar da waɗanda suka bijire ba. A maimakon haka, suna ƙoƙari su fahimci dalilin da ya sa ’yan’uwan suka bijire daga garken. Kuma sa’ad da suka komo ga Jehobah, dattawa za su ci gaba da nuna musu ƙauna.

13. Mene ne muka koya daga matakin da Jehobah ya ɗauka don abin da marubucin Zabura ta 73 ya faɗa?

13 Marubucin Zabura ta 73 ya yi sanyin gwiwa sa’ad da ya lura cewa kamar dai mugaye suna samun ci gaba. Sai ya soma tunani cewa bauta wa Allah ba shi da amfani. (Zab. 73:​12, 13, 16) Mene ne Jehobah ya yi? Bai yasar da shi ba, amma ya sa a rubuta kalmominsa a cikin Littafi Mai Tsarki. Daga baya, wannan marubucin zabura ya fahimci cewa dangantaka mai kyau da Jehobah ce ta fi muhimmanci. (Zab. 73:​23, 24, 26, 28) Wane darasi muka koya? Bai kamata dattawa su yi saurin shari’anta mutanen da suka soma ganin cewa bauta wa Jehobah ba shi da amfani. Maimakon haka, wajibi ne su ƙoƙarta su fahimci dalilin da ya sa ’yan’uwan suke da wannan ra’ayin. Yin hakan zai taimaka wa dattawa su yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su ƙarfafa ’yan’uwan.

14. Me ya sa Iliya yake bukatar taimako, kuma yaya Jehobah ya taimaka masa?

14 Annabi Iliya ya gudu don kada Sarauniya Jezebel ta kashe shi. (1 Sar. 19:​1-3) Iliya yana ganin cewa Jehobah ba shi da wani annabi a Isra’ila, kuma aikinsa ba shi da amfani. Iliya ya yi sanyin gwiwa sosai har ya so ya mutu. (1 Sar. 19:​4, 10) Maimakon Jehobah ya yasar da Iliya, ya tabbatar masa da cewa da akwai wasu annabawa. Ban da haka, Allah ya gaya wa Iliya cewa zai iya dogara da shi, kuma har ila da akwai aiki da yawa da zai yi. Jehobah ya saurari Iliya sa’ad da yake furta damuwarsa kuma ya ba shi sabon aiki. (1 Sar. 19:​11-16, 18) Wane darasi ne muka koya? Ya kamata dukanmu musamman dattawa su bi da bayin Jehobah a hankali. Ko da mutum yana fushi ko kuma ya ce yana ganin Jehobah ba zai taɓa gafarta masa ba, ya kamata dattawa su saurare shi sa’ad da yake gaya musu yadda yake ji. Bayan haka, za su yi ƙoƙari su tabbatar masa da cewa Jehobah yana ƙaunar sa.

YAYA ZA MU ƊAUKI WANDA YA BIJIRE?

15. Kamar yadda Yohanna 6:39 ta nuna, ta yaya Yesu yake ɗaukan tumakin Jehobah?

15 Ta yaya Jehobah yake so mu ɗauki ’yan’uwan da suka bijire? Za mu iya yin koyi da Yesu. Yesu ya san cewa dukan bayin Jehobah suna da tamani a gaban Allah. Shi ya sa Yesu ya yi iya ƙoƙarinsa ya taimaka wa “tumakin Isra’ila waɗanda suka ɓata” su komo ga Jehobah. (Mat. 15:24; Luk. 19:​9, 10) A matsayin Yesu na makiyayi nagari, ya yi iya ƙoƙarinsa don kada ko ɗaya daga cikin tumakin Jehobah ya ɓata.​—Karanta Yohanna 6:39.

16-17. Yaya ya kamata dattawa su riƙa ji game da taimaka ma waɗanda suka bijire? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Ɗan’uwan da Ya Bijire Zai Iya Ji.”)

16 Manzo Bulus ya ƙarfafa dattawan ikilisiyar Afisa su yi koyi da Yesu. Ya ce: “Dole ku yi aiki haka don mu taimaka wa marasa ƙarfi. Kuna tuna kuma da kalmar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Ya fi albarka a bayar da a karɓa.’ ” (A. M. 20:​17, 35) Hakan ya nuna cewa dattawa suna da aiki mai muhimmanci a wannan batun. Wani dattijo mai suna Salvador a ƙasar Sifen ya ce: “Sa’ad da na yi tunani a kan yadda Jehobah yake kula da bayinsa da suka bijire, hakan yana sa in yi iya ƙoƙarina don in taimaka musu. Na san cewa Jehobah yana so in kula da su.”

17 An taimaka wa dukan ’yan’uwan da suka bijire da aka ambata a wannan talifin su komo ga Jehobah. A yanzu, ’yan’uwa da yawa da suka bijire suna son su komo. A talifi na gaba, za a bayyana dalla-dalla abin da za mu iya yi don mu taimaka musu su komo ga Jehobah.

WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna

^ sakin layi na 5 Me ya sa wasu da suka yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah suka daina hakan? Yaya Allah yake ji game da su? Za a ba da amsoshin waɗannan tambayoyin a wannan talifin. Za a kuma tattauna darasi da muka koya daga yadda Jehobah ya taimaka wa mutane a zamanin dā da suka daina bauta masa na ɗan lokaci.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Mutum ya bijire sa’ad da ya yi watanni shida ko fiye da hakan bai fita wa’azi da ba da rahoto ba. Duk da haka, waɗannan mutanen ’yan’uwanmu ne kuma muna ƙaunar su.

^ sakin layi na 4 An canja wasu sunaye.

^ sakin layi na 10 A talifi na gaba, za a bayyana yadda dattawa za su bi waɗannan matakan.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: Don Ba’isra’ile makiyayi ya damu da tunkiyar da ta ɓata, zai neme ta kuma ya dawo da ita garken. Dattawa a yau suna yin hakan.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: Yayin da wata ’yar’uwa da ta daina halartan taro da fita wa’azi take jiran bas ya tashi, ta ga Shaidu biyu suna yin wa’azi da amalanke.