Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: “Ta wurin Koyarwar Musa na zama matacce ga Koyarwar Musa”?​—Gal. 2:19.

Bulus ya ce: “Ai, ta wurin Koyarwar Musa na zama matacce ga Koyarwar Musa, domin in rayu ga Allah.”​—Gal. 2:19.

Abin da Bulus ya rubuta a ayar nan ya jitu da muhimmin bayanin da yake so ’yan’uwa a ikilisiyoyin yankin Galatiya na Roma su fahimta. Malaman ƙarya sun rinjayi wasu Kiristoci. Suna koyar da cewa idan mutum yana so ya tsira, yana bukatar ya bi Koyarwar Musa, musamman dokar da aka bayar game da kaciya. Amma Bulus ya san cewa Allah ba ya bukatar Kiristoci su yi kaciya. Ya yi bayani mai kyau da ya nuna cewa wannan koyarwar ba gaskiya ba ce. Hakan ya sa ’yan’uwan sun daɗa yin imani da hadayar Yesu.​—Gal. 2:4; 5:2.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa idan mutum ya mutu, ba ya sanin kome, kuma babu abin da zai iya shafan sa. (M. Wa. 9:5) Sa’ad da Bulus ya ce: “Ta wurin Koyarwar Musa na zama matacce,” yana nufin cewa Dokar da Aka Ba da Ta Hannun Musa ba ta shafe shi kuma ba. Maimakon haka, Bulus yana da tabbaci cewa domin ya ba da gaskiya ga fansar Yesu, ya “rayu ga Allah.”

Dokar da Aka Ba da Ta Hannun Musa ne ta canja yanayin Bulus. Ta yaya? Kafin ya yi furucin, ya ce: “Mutum ba zai sami zaman marar laifi a gaban Allah ta wurin bin Koyarwar Musa ba, sai dai idan ya ba da gaskiya ga Yesu Almasihu.” (Gal. 2:16) Dokar ta cim ma wani abu mai muhimmanci. Bulus ya bayyana wa Galatiyawa cewa: “An yi ƙari da Koyarwar ne domin a nuna mana zunubanmu a fili. An kawo ta da nufi cewa za a yi aiki da ita har ranar da zuriyar nan ta Ibrahim za ta zo, wadda dominsa ne aka yi alkawarin.” (Gal. 3:19) Hakika, Dokar da Aka Ba da Ta Hannun Musa ta nuna cewa mutane ajizai ba za su iya bin Dokar ba tare da yin kuskure ba. Don haka, suna bukatar hadaya marar aibi. Dokar ta taimaka wa mutane su san cewa Yesu shi ne “zuriyar nan.” Idan mutum ya ba da gaskiya ga Yesu Kristi, zai zama mai adalci a gaban Allah. (Gal. 3:24) Bulus ya zama mai adalci a gaban Allah domin ta wurin Dokar ne ya san Yesu kuma ya yi imani da shi. Saboda haka, Bulus ya zama “matacce ga Koyarwar Musa” amma ya “rayu ga Allah.” Hakan ya nuna cewa Dokar ta daina iko a kansa amma Allah ya ci gaba da iko a kan Bulus.

Abin da Bulus ya faɗa a wasiƙarsa ga Romawa ke nan. Ya ce: “’Yan’uwana, . . . kun zama matattu game da ikon Koyarwar Musa, . . . amma yanzu kam, mun sami ’yanci daga ikon Koyarwar Musa gama mun mutu ga abin da ya ɗaure mu.” (Rom. 7:​4, 6) Ayar nan da kuma Galatiyawa 2:19 sun nuna cewa Bulus ba ya maganar mutuwa a matsayin mai laifi a ƙarƙashin Dokar. A maimakon haka, yana magana ne game da samun ’yanci. A yanzu, Dokar ta daina iko a kansa da dukan Kiristoci da suka sami ’yanci don sun ba da gaskiya ga fansar Yesu. Hadayar Kristi ta sa sun sami ’yanci.