TALIFIN NAZARI NA 23
Jehobah Yana Tare da Kai
“Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi.”—ZAB. 145:18.
WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Me ya sa bayin Jehobah a wasu lokuta sukan ji kaɗaici?
YAWANCINMU mukan yi fama da kaɗaici a wasu lokuta. Wasu suna iya magance nasu da wuri. Wasu kuma suna iya fama da hakan na dogon lokaci. Za mu iya jin kaɗaici ko da muna tare da mutane. Yana yi ma wasu wuya su sami abokai idan suka ƙaura zuwa wata ikilisiya. Wasu sun saba yin abubuwa tare da iyalinsu, shi ya sa idan suka rabu da iyalinsu, sai su soma jin kaɗaici. Wasu kuma suna kewar wani a iyalinsu ko kuma abokinsu da ya rasu. Ƙari ga haka, wasu Kiristoci musamman ma waɗanda ba su daɗe da soma bauta ma Jehobah ba, sukan ji kaɗaici sa’ad da iyalinsu ko abokansu na dā suka ƙi su, ko kuma suka soma tsananta musu.
2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
2 Jehobah ya san kome game da mu. Idan muna fama da kaɗaici, Jehobah ya san da hakan, kuma zai iya taimaka mana mu daina jin kaɗaici. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana? Ta yaya za mu iya taimaka ma kanmu? Kuma ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiyarmu da suke fama da kaɗaici? Bari mu ga amsoshin waɗannan tambayoyin.
JEHOBAH YA DAMU DA MU
3. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya damu da Iliya?
3 Jehobah yana so dukan bayinsa su riƙa farin ciki. Yana kusa da kowannenmu, kuma idan muna fama da baƙin ciki, ya sani. (Zab. 145:18, 19) Ka lura da yadda Jehobah ya nuna cewa ya damu da annabinsa Iliya. Annabin ya yi rayuwa a mawuyacin zamani. A lokacin, mutane masu iko suna tsananta wa bayin Jehobah kuma sun so su kashe Iliya. (1 Sar. 19:1, 2) Wani abu kuma da wataƙila ya dame Iliya shi ne, ya ɗauka cewa shi kaɗai ne annabin Jehobah da ya rage. (1 Sar. 19:10) Jehobah ya ɗauki mataki nan da nan don ya taimaka wa Iliya. Jehobah ya tura mala’ikansa ya tabbatar wa annabi Iliya cewa akwai Isra’ilawa da yawa da suke bauta masa cikin aminci. Don haka, ba shi kaɗai ba ne ya rage!—1 Sar. 19:5, 18.
4. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa ya damu da bayinsa da iyalinsu ko abokansu suka ƙi su? (Markus 10:29, 30)
4 Jehobah ya san cewa wasu cikinmu sun yi sadaukarwa sosai sa’ad da suka yi alkawarin bauta masa. Ɗaya daga cikin abubuwan da wataƙila suka sadaukar shi ne taimakon da suke samu daga iyalinsu da abokansu na dā. Mai yiwuwa tunanin hakan ne ya sa Bitrus ya yi wa Yesu tambayar nan: “Mun bar kome domin mu bi ka, to, me za mu samu?” (Mat. 19:27) Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa ’yan’uwa a ikilisiya za su zama kamar iyalinsu. (Karanta Markus 10:29, 30.) Ban da haka, Jehobah Ubanmu na sama ya yi alkawari cewa zai kula da dukan waɗanda suke bauta masa. (Zab. 9:10) Za mu tattauna wasu abubuwan da za ka iya yi domin Jehobah ya taimaka maka ka daina jin kaɗaici.
ABIN DA ZA KA IYA YI IDAN KA KAƊAITA
5. Me ya sa yake da kyau mu yi tunani a kan yadda Jehobah yake taimaka mana?
5 Ka yi tunanin yadda Jehobah yake taimaka maka. (Zab. 55:22) Hakan zai taimaka maka ka ga cewa Jehobah yana tare da kai. Wata ’yar’uwa mai suna Carol * da ba ta yi aure ba, kuma ita kaɗai ce take bauta ma Jehobah a iyalinsu, ta ce: “Idan na tuna da yadda Jehobah ya taimaka mini a lokacin da nake cikin matsala, ina gaya wa kaina cewa Jehobah bai bar ni ni kaɗai ba. Ina da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da kasancewa tare da ni.”
6. Ta yaya 1 Bitrus 5:9, 10 za su iya ƙarfafa waɗanda suke fama da kaɗaici?
6 Ka yi tunanin yadda Jehobah yake taimaka ma ’yan’uwa da suka kaɗaita. 1 Bitrus 5:9, 10.) Wani ɗan’uwa mai suna Hiroshi wanda ya yi shekaru yana bauta ma Jehobah shi kaɗai a iyalinsu, ya ce: “A cikin ikilisiya, za ka ga cewa kowa ma yana da nasa matsaloli. Mun san cewa dukanmu muna yin iya ƙoƙarinmu ne don mu bauta wa Jehobah. Hakan yana ƙarfafa mu da iyalanmu ba sa bauta wa Jehobah.”
(Karanta7. Ta yaya addu’a take taimaka maka?
7 Ka riƙa addu’a da karanta Littafi Mai Tsarki a kullum kuma ka halarci taro a kai a kai. Ka riƙa gaya wa Jehobah yadda kake ji. (1 Bit. 5:7) Wata matashiya mai suna Massiel da ta kaɗaita sa’ad da ta soma bauta ma Jehobah domin iyalinta ba sa yin hakan, ta ce: “Wani abu da ya fi taimaka mini in magance matsalar kaɗaici da na yi fama da shi, shi ne yin addu’a kullum ga Jehobah. Shi Ubana ne, shi ya sa nake yin addu’a a gare shi sau da yawa a kowace rana kuma ina gaya masa yadda nake ji.”
8. Ta yaya karanta Kalmar Allah da yin bimbini a kai yake taimaka maka?
8 Ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana, kuma ka yi tunani a kan nassosi da suka nuna cewa Jehobah yana ƙaunar ka. Wata ’yar’uwa mai suna Bianca da ta yi fama da baƙar magana daga iyalinta, ta ce: “Karanta da kuma yin bimbini a kan labaran bayin Jehobah na dā da suka fuskanci matsaloli irin nawa ya taimaka mini sosai.” Wasu Kiristoci sukan haddace nassosi masu ban ƙarfafa kamar Zabura 27:10 da Ishaya 41:10. Wasu kuma sun lura cewa saurarar karatun littattafanmu sa’ad da suke shirya taro ko kuma yin nazari, yana taimaka musu su daina jin kaɗaici.
9. Ta yaya halartan taro yake taimaka maka?
9 Ka yi iya ƙoƙarinka don ka riƙa halartan taro. Abubuwan da za a tattauna a taron za su ƙarfafa ka kuma za ka kusaci ’yan’uwanka. (Ibran. 10:24, 25) Massiel, wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Ko da yake ina jin kunya, nakan yi iya ƙoƙarina don in halarci kowace taron ikilisiya kuma in yi kalami. Hakan ya taimaka mini in kusaci ’yan’uwa a ikilisiya.”
10. Me ya sa yake da kyau mu yi abokantaka da ’yan’uwa a ikilisiya?
10 Ka yi abokantaka da Kiristoci masu aminci. Ka yi abokantaka da ’yan’uwa da za ka iya koyan halaye masu kyau daga wurinsu, ko da su ba tsararka ba ne, ko kuma sun fito daga wani wuri dabam. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “a wurin tsofaffi” ne ake samun hikima. (Ayu. 12:12) Tsofaffi ma za su iya koya daga wurin matasa a cikin ikilisiya. Jonathan ya girme Dauda sosai, amma hakan bai hana su zama abokai na kud da kud ba. (1 Sam. 18:1) Dauda da Jonathan sun taimaka ma juna su ci gaba da bauta wa Jehobah duk da matsalolin da suka fuskanta. (1 Sam. 23:16-18) Wata ’yar’uwa mai suna Irina, wadda ita kaɗai ce take bauta wa Jehobah a iyalinsu ta ce: “ ’Yan’uwanmu masu bi za su iya zama kamar iyalinmu. Jehobah zai iya yin amfani da su ya biya bukatunmu.”
11. Me za mu yi don mu iya samun abokan kirki?
11 Samun abokai bai da sauki, musamman idan kai mai jin kunya ne. Wata ’yar’uwa da ke jin kunya, mai suna Ratna, ta soma bauta wa Jehobah duk da cewa ta fuskanci hamayya. Ta ce: “Na lura cewa ina bukatar taimako da goyon bayan ’yan’uwana a ikilisiya.” Zai iya yi maka wuya ka gaya ma wani yadda kake ji, amma yin hakan zai sa ku zama abokai. Abokanka za su so su ƙarfafa ka kuma su taimaka maka, amma sai ka gaya musu yadda kake so su taimaka maka kafin su yi hakan.
12. Ta yaya yin wa’azi zai sa ka sami abokan kirki?
12 Wata hanya mai muhimmanci na samun abokai ita ce ta wajen yin wa’azi tare da ’yan’uwanmu. ’Yar’uwa Carol da aka ambata ɗazu ta ce: “Yin wa’azi da kuma wasu ayyuka a ikilisiya tare da ’yan’uwana mata ya sa na sami abokai. Jehobah ya daɗe yana amfani da ’yan’uwan nan yana taimaka mini.” Za mu amfana idan muka yi abokantaka da ’yan’uwanmu Kiristoci. Jehobah yana amfani da ’yan’uwan nan ya ƙarfafa mu musamman a lokacin da muka kaɗaita.—K. Mag. 17:17.
MU TAIMAKA WA ’YAN’UWA SU ƊAUKE MU A MATSAYIN IYALINSU
13. Wane hakki ne kowa a ikilisiya yake da shi?
13 Dukanmu muna da hakkin tabbatar da cewa akwai salama da ƙauna a ikilisiyarmu don kada kowa ya kaɗaita. (Yoh. 13:35) Za mu iya yin hakan ta furucinmu da kuma ayyukanmu. Wata ’yar’uwa ta ce: “Bayan da na soma bauta wa Jehobah, ’yan’uwa a ikilisiyarmu sun zama kamar abokaina. Da a ce ba su taimaka mini ba, da ba zan iya zama Mashaidiyar Jehobah ba.” Ta yaya za ka taimaka wa waɗanda iyalinsu ba sa bauta ma Jehobah su san cewa ’yan’uwa a ikilisiya suna ƙaunar su?
14. Mene ne za ka yi don ka ƙulla abokantaka da sabbi?
14 Ka yi abokantaka da sabbi. Idan muka lura cewa akwai ɗalibai da suka fara halartan taro a ikilisiyarmu ko ’yan’uwa da suka ƙaura ko kuma waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba, zai dace mu marabce su. (Rom. 15:7) Amma akwai abin da ya kamata mu yi ban da gaisuwa kawai. Ya kamata mu zama abokansu da shigewar lokaci. Ka nuna musu cewa ka damu da su. Ka yi ƙoƙari ka san matsalolin da suke fuskanta, amma kada ka yi musu tambayoyin da za su kunyatar da su. Zai iya ma wasu wuya su gaya maka yadda suke ji. Idan hakan ya faru, kada ka matsa musu su yi magana. Maimakon ka tilasta musu, ka yi musu tambaya cikin basira kuma ka saurare su sa’ad da suke ba ka amsa. Alal misali, za ka iya tambayar su abin da ya sa suka soma bauta wa Jehobah.
15. Ta yaya ’yan’uwa da suka manyanta za su iya taimaka ma sauran ’yan’uwa a ikilisiya?
15 Za mu ƙarfafa bangaskiyar juna,
idan muna nuna cewa mun damu da juna, musamman ma idan dattawa ko ’yan’uwa da suka manyanta ne suke kan gaba a yin hakan. Wata ’yar’uwa mai suna Melissa, wadda mamarta ce ta koya mata game da Jehobah ta ce: “Ina godiya sosai ga ’yan’uwa da suka zama kamar uba a gare ni. ’Yan’uwan nan sun kasance tare da ni kuma sun nuna mini cewa sun damu da ni. A duk lokacin da nake so in faɗi yadda nake ji, sukan saurare ni.” Wani ɗan’uwa matashi mai suna Mauricio, ya yi baƙin ciki kuma ya kaɗaita sa’ad da wanda ya yi nazari da shi ya daina bauta wa Jehobah. Ya ce: “Yadda dattawa suka nuna sun damu da ni ya taimaka mini. Sukan tattauna da ni a kai a kai. Sukan fita wa’azi tare da ni, suna gaya mini darussa masu kyau da suka koya daga nazarinsu kuma mukan yi wasanni tare.” A yanzu, Melissa da Mauricio suna yin hidima a Bethel.16-17. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya taimaka ma ’yan’uwanmu?
16 Ka yi abin da zai taimaka ma ’yan’uwa. (Gal. 6:10) Wani ɗan’uwa mai suna Leo, da ke wa’azi a ƙasar waje, ya ce: “A yawancin lokaci, idan aka yi mana alheri a lokacin da muke da bukata, kome ƙanƙancinsa, yakan ƙarfafa mu.” Ya ƙara da cewa: “Na tuna wata rana da na yi hatsari da mota. Da na isa gida, na damu sosai. Sai wasu ma’aurata suka gayyace ni in ci abinci tare da su a gidansu. Na manta abin da muka ci, amma na tuna cewa sun saurare ni sosai. Na ji daɗin kasancewa tare da su!”
17 Mukan ji daɗin taron da’ira da taron yanki domin mukan yi cuɗanya da ’yan’uwanmu a wurin kuma mukan tattauna abubuwan da muka koya daga taron. Amma Carol wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Nakan ji kaɗaici musamman sa’ad da na halarci taron da’ira da taron yanki.” Me ya sa? Ta ce: “Ko da yake ina tare da ’yan’uwa da yawa, a yawancin lokaci kowa yana zama tare da iyalinsa ne kawai. A duk lokacin da na ga suna zama tare, sai in daɗa jin kaɗaici.” Wasu kuma yana yi musu wuya su halarci taron da’ira ko taron yanki a lokaci na farko bayan mijinsu ko matarsu ta rasu. Shin ka san
wani da yake fuskantar irin waɗannan matsaloli? Idan ka sani, za ka iya gaya masa ya zauna tare da kai da iyalinka a taro na gaba.18. Ta yaya za mu bi abin da ke 2 Korintiyawa 6:11-13 yayin da muke nuna ma ’yan’uwanmu karimci?
18 Ka riƙa cuɗanya da ’yan’uwa. Ka riƙa gayyatar ’yan’uwa dabam-dabam ku shaƙata tare, musamman waɗanda suka kaɗaita. Zai dace mu riƙa nuna wa irin ’yan’uwan nan ƙauna. (Karanta 2 Korintiyawa 6:11-13.) Melissa da aka ambata ɗazu, ta ce: “A duk lokacin da ’yan’uwa suka gayyace mu gidansu don mu shaƙata ko kuma mu yi wata tafiya tare, mukan yi farin ciki sosai.” Akwai wani a ikilisiyarku da za ka iya nuna masa karimci?
19. A waɗanne lokuta ne musamman ya kamata mu kasance tare da ’yan’uwanmu?
19 Akwai wasu lokuta na musamman da ’yan’uwanmu za su bukaci mu yi cuɗanya da su. Zai yi ma wasu ’yan’uwa wuya su kasance tare da iyalinsu sa’ad da iyalin suke yin bukukuwa da ba su jitu da Littafi Mai Tsarki ba. Wasu sukan yi baƙin ciki sosai a wasu ranaku, alal misali, idan ranar mutuwar abokin aurensu ta zagayo. Idan mun gayyaci ’yan’uwa da suke fuskantar waɗannan matsaloli, za mu nuna cewa mun ‘damu da su sosai.’—Filib. 2:20.
20. Ta yaya abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 12:48-50 zai taimaka mana sa’ad da muke jin kaɗaici?
20 Akwai abubuwa dabam-dabam da za su iya sa Kirista ya kaɗaita. Amma, kada mu manta cewa Jehobah ya san yanayin da muke ciki. Sau da yawa, yana yin amfani da ’yan’uwanmu don ya tanada mana abubuwan da muke bukata. (Karanta Matiyu 12:48-50.) Za mu iya nuna wa Jehobah cewa muna godiya don ’yan’uwa da ya ba mu, ta wajen yin iya ƙoƙarinmu mu taimaka musu. Ko da wace matsala ce muke fuskanta, ya kamata mu san cewa Jehobah yana tare da mu.
WAƘA TA 46 Muna Godiya, Ya Jehobah
^ sakin layi na 5 Kana fama da kaɗaici a wasu lokuta? Idan haka ne, ka tabbata cewa Jehobah ya san da matsalarka, kuma yana a shirye ya taimaka maka. A wannan talifin, za mu tattauna abin da za ka iya yi don ka daina jin kaɗaici. Za mu kuma tattauna yadda za ka iya taimaka ma ’yan’uwa da ke fama da kaɗaici.
^ sakin layi na 5 An canja wasu sunayen.
^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwan da matarsa ta rasu yana samun ƙarfafa ta wajen saurarar karatun Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafanmu.
^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa da kuma ’yarsa sun ziyarci wani ɗan’uwa tsoho don su nuna masa karimci.