Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 25

Kada Ka Sa “Yara Kananan Nan” Tuntube

Kada Ka Sa “Yara Kananan Nan” Tuntube

“Kada ku rena ko ɗaya daga cikin yara ƙananan nan.”​—MAT. 18:10.

WAƘA TA 113 Salamar da Muke Morewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Jehobah ya yi wa kowannenmu?

JEHOBAH ne ya jawo kowannenmu wurinsa. (Yoh. 6:44) Ka yi tunanin abin da hakan yake nufi. Sa’ad da Jehobah yake bincika zuciyar biliyoyin mutane a duniya, ya ga cewa kana da zuciyar kirki kuma za ka ƙaunace shi. Hakan ya sa ka kasance da daraja a gaban Jehobah. (1 Tar. 28:9) Jehobah ya san ka, ya san yadda kake ji kuma yana ƙaunar ka. Sanin hakan yana da ban ƙarfafa!

2. Ta yaya Yesu ya kwatanta yadda Jehobah yake ƙaunar kowannenmu?

2 Jehobah ya damu da kai da kuma dukan bayinsa. Yesu ya kwatanta Jehobah da makiyayi don ya taimaka mana mu gane cewa Jehobah ya damu da mu sosai. Idan 1 daga cikin tumaki 100 ta ɓata, mene ne makiyayin zai yi? Zai “bar sauran casa’in da taran a tuddai suna kiwo ya je neman ɗayarsu da ta ɓata.” Sa’ad da makiyayin ya sami tunkiyar, ba zai yi fushi da ita domin ta ɓata ba. Amma zai yi murna. Mene ne hakan ya koya mana? Jehobah yana ƙaunar kowannenmu. Yesu ya ce: ‘Ba nufin Ubanku wanda yake cikin sama ba ne ɗaya daga cikin yara ƙananan nan ya ɓata.’​—Mat. 18:​12-14.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Hakika ba za mu so mu sa wani ɗan’uwanmu ya yi sanyin gwiwa ba. Ta yaya za mu guji sa ’yan’uwanmu tuntuɓe? Kuma me za mu yi idan wani ya ɓata mana rai? Za mu tattauna tambayoyin nan a wannan talifin. Amma da farko, bari mu ga ko su waye ne “yara ƙananan nan” da aka yi maganar su a Matiyu sura 18.

SU WAYE NE “YARA ƘANANAN NAN”?

4. Su waye ne “yara ƙananan nan”?

4 “Yara ƙananan nan” suna nufin mabiyan Yesu, yara da manya. Kome yawan shekarunsu suna kamar “ƙananan yara” domin suna so su koya daga wurin Yesu. (Mat. 18:3) Ko da yake halayensu da al’adunsu da kuma wurin da suka fito sun bambanta, sun ba da gaskiya ga Kristi. Kristi kuma yana ƙaunar su sosai.​—Mat. 18:6; Yoh. 1:12.

5. Yaya Jehobah yake ji idan wani ya sa bawansa tuntuɓe ko kuma baƙin ciki?

5 Jehobah yana ƙaunar duka “yara ƙananan nan.” Domin mu fahimci hakan, bari mu yi la’akari da yadda muke ɗaukan ƙananan yara. Mukan yi ƙoƙari mu kāre su domin ba su da ƙarfi ko hikima kuma ba su ƙware kamar waɗanda suka manyanta ba. Ba ma jin daɗi idan muka ga wani yana wulaƙanta ɗan’uwansa, balle ma a ce yana wulaƙanta yara. Haka ma, Jehobah yana so ya kāre mu, kuma yana fushi idan ya ga wani yana ƙoƙari ya sa bawansa yin tuntuɓe ko baƙin ciki!​—Isha. 63:9; Mar. 9:42.

6. Kamar yadda 1 Korintiyawa 1:​26-29 suka nuna, yaya mutane suka ɗauke almajiran Yesu?

6 A wace hanya ce kuma almajiran Yesu suka yi kama da ‘yara ƙanana’? Waɗanne irin mutane ne ake ɗaukan su da muhimmanci a duniya? Masu arziki ko masu iko ko kuma waɗanda suka yi suna. Amma almajiran Yesu ba su da arziki ko iko ko kuma suna. Shi ya sa mutane suka ɗauke su kamar ba su isa kome ba. (Karanta 1 Korintiyawa 1:​26-29.) Amma ba haka Jehobah yake ɗaukan su ba.

7. Yaya Jehobah yake so mu ɗauki ’yan’uwanmu?

7 Jehobah yana ƙaunar duka bayinsa ko da sun daɗe suna bauta masa ko ba su daɗe ba. Dukan ’yan’uwanmu suna da muhimmanci a gaban Jehobah, don haka, ya kamata mu ma mu ɗauke su da muhimmanci. Muna bukatar mu ƙaunaci dukan “ ’yan’uwa masu bin Yesu” ba wasu kawai daga cikinsu ba. (1 Bit. 2:17) Ya kamata mu yi abin da zai sa su san cewa muna ƙaunar su kuma mu guji yin abin da zai ɓata musu rai. Idan muka lura cewa mun ɓata ma wani rai, kada mu yi kamar babu abin da ya faru, ko mu ce mutumin yana saurin fushi kuma ya kamata ya daina hakan. Mene ne zai iya ɓata wa mutum rai? Mai yiwuwa yadda aka yi renon wasu ya sa suna ƙasƙantar da kansu. Don hakan idan an gaya musu wani abu kaɗan, za su iya ɗauka kamar an rena su ne. Wasu kuma bai daɗe da suka soma bauta wa Jehobah ba, don haka, ba su gama fahimta cewa dole ne su gafarta ma waɗanda suka yi musu laifi ba. Ko da yaya yanayin yake, mu yi iya ƙoƙarinmu mu sasanta matsalar. Ƙari ga haka, mutumin da ransa yake saurin ɓacewa yana bukatar ya san cewa wannan hali ne da bai dace ba, kuma yana bukatar ya canja. Yana bukatar ya yi hakan don ya sami kwanciyar hankali kuma ya yi zaman lafiya da ’yan’uwa.

KA ƊAUKI WASU DA MUHIMMANCI FIYE DA KANKA

8. Wane ra’ayi ne mutane a zamanin Yesu suke da shi, kuma ta yaya hakan ya shafi almajiransa?

8 Mene ne ya sa Yesu ya yi magana game da “yara ƙananan nan”? Almajiransa sun yi masa wata tambaya, sun ce: “Wa ya fi girma duka a cikin mulkin sama?” (Mat. 18:1) Yahudawa da yawa a zamanin suna ganin kamar samun matsayi yana da muhimmanci sosai. Wani marubuci ya ce: “Mutane sukan yi iya ƙoƙarinsu don a riƙa ɗaukan su da muhimmanci ko su yi suna ko a amince da su ko kuma a riƙa daraja su.”

9. Mene ne ya kamata almajiran Yesu su yi?

9 Yesu ya san cewa ba zai kasance wa almajiransa da sauki su daina neman matsayi ba, domin al’adarsu ta ɗaukaka hakan. Ya ce musu: “Bari babba a cikinku ya zama kamar ƙarami, shugaba kuma ya zama kamar bawa.” (Luk. 22:26) Za mu zama kamar ƙananan yara idan muna ɗaukan wasu ‘da muhimmanci fiye da kanmu.’ (Filib. 2:3) Idan muka kasance da irin wannan halin, zai yi wuya mu sa mutane tuntuɓe.

10. Wace shawarar Bulus ce ya kamata mu tuna?

10 Akwai hanyoyi dabam-dabam da ’yan’uwanmu suka fi mu. Idan muna tunanin halaye masu kyau da ’yan’uwanmu suke da su, ba zai yi mana wuya mu fahimci cewa sun fi mu ba. Muna bukatar mu bi shawarar da manzo Bulus ya ba ’yan’uwan da ke Korinti. Ya ce: “Wane ne ya ce ka fi sauran? Mene ne kake da shi wanda ba Allah ne ya ba ka ba? To, in haka ne mene ne ya sa kana ɗaga kai kamar ba a kyauta ka samu ba?” (1 Kor. 4:7) Don haka, kada mu yi abin da zai sa wasu su ji kamar mun fi su muhimmanci. Alal misali, idan wani ɗan’uwa ya iya ba da jawabi sosai ko wata ’yar’uwa ta ƙware wajen samun ɗaliban Littafi Mai Tsarki, ya kamata su yabi Jehobah, ba kansu ba.

KA RIƘA GAFARTAWA DA “ZUCIYA ƊAYA”

11. Wane darasi ne Yesu yake so mu koya daga labarin wani sarki da bawansa?

11 Jim kaɗan bayan Yesu ya gargaɗi mabiyansa cewa kada su sa mutane tuntuɓe, sai ya ba su labarin wani sarki da bawansa. Sarkin ya yafe wa bawansa bashi mai yawa da bawan ya kasa biya. Bayan haka, bawan ya ƙi yafe wa abokin aikinsa ƙaramin bashi da yake bin sa. A ƙarshe, sarkin ya sa wannan bawa marar tausayi a kurkuku. Wane darasi muka koya? Yesu ya ce: “Haka kuwa Ubana wanda yake cikin sama zai yi wa kowannenku da ya ƙi yafe wa ɗan’uwansa da zuciya ɗaya.”​—Mat. 18:​21-35.

12. Idan muka ƙi gafarta ma ɗan’uwa ko ’yar’uwa, ta yaya hakan zai shafi sauran ’yan’uwanmu?

12 Abin da bawan nan ya yi ya jawo masa da kuma wasu baƙin ciki. Na farko, bai tausaya wa abokin aikinsa ba, amma ya ‘je ya sa shi a kurkuku, har sai ya biya bashin.’ Na biyu, ya ɓata ran sauran bayin da suka ga abin da ya faru. Littafi Mai Tsarki ya ce “da abokan aikinsa suka ji abin da ya faru, sai ba su ji daɗi ba.” Haka ma, abin da muke yi yana shafan wasu. Me zai iya faruwa idan wani ya yi mana laifi kuma muka ƙi gafarta masa? Na farko, za mu sa shi baƙin ciki domin mun ƙi gafarta masa, mun ƙi ba shi lokacinmu, kuma mun ƙi nuna masa ƙauna. Na biyu, sauran ’yan’uwa a ikilisiya ba za su ji daɗi ba idan suka lura cewa akwai matsala a tsakaninmu da wani.

Shin za ka riƙe ’yan’uwanka a zuciya ko kuma za ka gafarta musu? (Ka duba sakin layi na 13-14) *

13. Mene ne ka koya daga labarin wata majagaba?

13 Idan mun gafarta ma ’yan’uwanmu, za mu amfana kuma ’yan’uwanmu ma za su amfana. Abin da ya faru da wata majagaba da za mu kira ta da suna Crystal ke nan. Wata ’yar’uwa a ikilisiyarsu ta ɓata mata rai. Crystal ta ce: “A wasu lokuta kalmominta suna mini zafi sosai. Ban so ma in fita wa’azi tare da ita ba. A hankali, na daina jin daɗin fita wa’azi kuma na soma baƙin ciki.” A ganin Crystal, tana da hujjar yin fushi. Amma ba ta riƙe ’yar’uwar a zuciya ko kuma ta mai da hankali ga yadda take ji ba. Me ya sa? Ta nuna sauƙin kai kuma ta bi shawarar Littafi Mai Tsarki da aka rubuta a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1999. Talifin da ta karanta shi ne, “Ka Gafarta Daga Zuciyarka.” Crystal ta gafarta wa ’yar’uwar kuma ta ce: “Yanzu na fahimci cewa dukanmu muna ƙoƙari mu yi canje-canje a rayuwarmu, kuma Jehobah yana a shirye ya gafarta mana a kowace rana. Sai na ji kamar an sauke wani kaya mai nauyi daga kaina. Yanzu ina farin ciki.”

14. Bisa ga Matiyu 18:​21, 22, wace matsala ce wataƙila manzo Bitrus ya yi fama da ita, kuma me ka koya daga abin da Yesu ya faɗa masa?

14 Mun san cewa ya kamata mu riƙa gafarta wa mutane. Amma yin haka bai da sauƙi. Wataƙila manzo Bitrus ya yi fama da hakan a wasu lokuta. (Karanta Matiyu 18:​21, 22.) Me zai taimaka mana? Abu na farko da zai taimaka mana shi ne, yin tunani a kan yadda Jehobah yake gafarta mana. (Mat. 18:​32, 33) Ba mu cancanci ya gafarta mana ba, amma yana yin hakan a sake. (Zab. 103:​8-10) Kalmar Allah ta ce dole ne mu ma mu ƙaunaci juna. Don haka, dole ne mu riƙa gafarta wa ’yan’uwanmu. (1 Yoh. 4:11) Na biyu, ka yi tunanin sakamako mai kyau da za mu samu idan muka gafarta wa ’yan’uwanmu. Idan mun gafarta wa mutumin da ya yi mana laifi, hakan zai taimaka wa mutumin, ikilisiyar za ta kasance da haɗin kai, za mu kāre dangantakarmu da Jehobah kuma za mu sami kwanciyar hankali. (2 Kor. 2:7; Kol. 3:14) A ƙarshe, ka yi addu’a ga Jehobah wanda ya ce mu riƙa gafartawa. Kada ka bari Shaiɗan ya ɓata dangantakarka da ’yan’uwanka. (Afis. 4:​26, 27) Muna bukatar taimakon Jehobah don mu guji fāɗawa a tarkon Shaiɗan.

KADA KA BAR WANI YA SA KA TUNTUƁE

15. Bisa ga abin da ke Kolosiyawa 3:​13, me ya kamata mu yi idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi abin da ya ɓata mana rai?

15 Idan wani ɗan’uwa ya yi abin da ya ɓata maka rai fa? Me ya kamata ka yi? Ka yi iya ƙoƙarinka don ku yi zaman lafiya. Ka gaya wa Jehobah yadda kake ji. Ka roƙi Jehobah ya taimaki mutumin da ya ɓata maka rai, kuma ya taimaka maka ka mai da hankali ga halaye masu kyau da mutumin yake da su. (Luk. 6:28) Idan ka gagara haƙura, ka yi tunanin hanyar da ta dace da za ka tattauna batun da shi. Kada ka ɗauka cewa da gangan ne ɗan’uwan ya ɓata maka rai. (Mat. 5:​23, 24; 1 Kor. 13:7) Idan kana magana da shi, ka ba shi dama ya bayyana kansa. In ba ya so ku sasanta kuma fa? Littafi Mai Tsarki ya ce ka yi “ta yin haƙuri” da shi. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Abin da ya fi muhimmanci shi ne, kada ka riƙe shi a zuciya, domin yin hakan zai iya ɓata dangantakarka da Jehobah. Kada ka bari wani ya sa ka yi tuntuɓe. Ta yin hakan, za ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah fiye da kome.​—Zab. 119:165.

16. Wane hakki ne kowannenmu yake da shi?

16 Muna farin ciki don muna iya bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu maza da mata, a matsayin “garke ɗaya,” a ƙarƙashin “makiyayi ɗaya” kuma! (Yoh. 10:16) A shafi na 165 na littafin nan, Organized to Do Jehovah’s Will, an rubuta cewa: “Da yake kana more zaman lafiya da ake yi a ikilisiya, kana da hakkin yin abin da zai sa zaman lafiyar nan ta dawwama.” Saboda haka, muna bukatar mu “koyi yadda za mu kasance da ra’ayin Jehobah game da ’yan’uwanmu.” Ga Jehobah, dukanmu “yara ƙanana” ne masu daraja. Yadda kake ɗaukan ’yan’uwanka maza da mata ke nan? Jehobah yana ganin dukan abubuwan da kake yi don ka taimaka musu da kuma kula da su.​—Mat. 10:42.

17. Me muka ƙuduri niyyar yi?

17 Muna ƙaunar ’yan’uwanmu masu bi. Saboda haka, mun ‘ɗauki niyya cewa ba za mu zama dalilin tuntuɓe ko abin sa zunubi ga ɗan’uwanmu ba.’ (Rom. 14:13) Muna ɗaukan ’yan’uwanmu a matsayin waɗanda suka fi mu, kuma muna so mu riƙa gafarta musu da zuciya ɗaya. Kada mu bari wasu su sa mu yi tuntuɓe. A maimakon haka, “mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama da ƙarfafawar juna.”​—Rom. 14:19.

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

^ sakin layi na 5 Da yake mu ajizai ne, za mu iya faɗa ko yi abin da zai ɓata wa ’yan’uwanmu rai. Me ya kamata ka yi idan hakan ya faru? Kana yin iya ƙoƙarinka don ka sasanta da wanda ya ɓata maka rai? Kana neman gafararsa ba tare da ɓata lokaci ba? Idan wani yana fushi da kai, za ka ce hakan ruwansa ne? Idan kuma kana saurin fushi fa? Kana ba da hujja ta wajen cewa haka kake? Ko kuma ka fahimci cewa kana bukatar ka canja halinka?

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa tana fushi da wata a ikilisiya. Bayan sun sasanta, kowannensu ta mance da batun kuma suka ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.