Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 24

Za Ka Iya Kuɓuta Daga Tarkon Shaiɗan!

Za Ka Iya Kuɓuta Daga Tarkon Shaiɗan!

Ku “kuɓuta daga tarkon Shaiɗan.”​—2 TIM. 2:26.

WAƘA TA 36 Mu Riƙa Kāre Zuciyarmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa za mu iya kwatanta Shaiɗan da mafarauci?

ABIN DA mafarauci ya sa a kan gaba shi ne kama ko kuma kashe dabba. Kamar yadda ɗaya daga cikin abokan ƙarya na Ayuba ya faɗa, mafarauci zai iya yin amfani da tarko iri-iri. (Ayu. 18:​8-10) Ta yaya mafarauci yake jawo hankalin dabba don ta fāɗa tarkonsa? Yakan bincika inda dabbar take zuwa, abin da take so da kuma abin da yake jan hankalinta. Shaiɗan yana kama da mafaraucin nan. Yakan duba inda muke zuwa da abin da muke so. Sa’an nan ya sa tarkon da yake fatan zai kama mu ba zato. Amma Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa idan muka fāɗa a tarkon Shaiɗan, za mu iya kuɓuta. Ƙari ga haka, yana taimaka mana mu guji fāɗawa a tarkon Shaiɗan.

Abubuwan da Shaiɗan ya fi yin amfani da su a matsayin tarko su ne girman kai da kuma haɗama (Ka duba sakin layi na 2) *

2. Waɗanne abubuwa biyu ne Shaiɗan yake amfani da su sosai?

2 Abubuwa biyu da Shaiɗan ya fi amfani da su a matsayin tarko su ne girman kai da haɗama. * Shaiɗan ya yi shekaru yana amfani da waɗannan halaye marasa kyau. Yana kama da mafarauci da yake jan hankalin dabba don ta fāɗa a tarkonsa. (Zab. 91:3) Amma ba lallai ba ne mu fāɗa a tarkon Shaiɗan. Don me muka ce hakan? Domin Jehobah ya bayyana mana dabarun Shaiɗan.​—2 Kor. 2:11.

Za mu iya koyan darussa daga misalan da ke Littafi Mai Tsarki kuma mu guji fāɗawa a tarkon Shaiɗan (Ka duba sakin layi na 3) *

3. Me ya sa aka rubuta labaran mutane da suka zama masu girman kai ko haɗama a cikin Littafi Mai Tsarki?

3 Jehobah ya nuna mana yadda girman kai da haɗama suke da haɗari ta wajen gaya mana abin da ya faru da wasu bayinsa. Ta haka, za mu guje wa kurakuren da suka yi. A misalin da za mu tattauna, za mu ga yadda Shaiɗan ya sa mutanen da suka yi shekaru suna bauta wa Jehobah su fāɗa a tarkonsa. Shin hakan yana nufin cewa ba za mu iya guji zama masu girman kai da haɗama ba ne? A’a. Jehobah ya sa a rubuta waɗannan misalan a cikin Littafi Mai Tsarki don ya “yi mana gargaɗi.” (1 Kor. 10:11) Ya san cewa za mu iya koyan darussa daga misalan kuma mu guji fāɗawa a tarkon Shaiɗan. In kuma mun riga mun fāɗi, za mu san yadda za mu kuɓuta.

GIRMAN KAI TARKO NE

Ka duba sakin layi na 4

4. Mene ne girman kai zai iya jawo mana?

4 Shaiɗan yana so mu zama masu girman kai. Ya san cewa idan muka zama masu girman kai kamar shi, ba za mu sami rai na har abada ba. (K. Mag. 16:18) Manzo Bulus ya ce zai yiwu mutum ya zama mai girman kai, kuma hakan zai sa “ya shiga cikin irin hukuncin da aka yi wa Shaiɗan.” (1 Tim. 3:​6, 7) Hakan zai iya faruwa da kowannenmu ko da mun yi shekaru muna bauta wa Jehobah, ko ba mu daɗe da soma bauta masa ba.

5. Kamar yadda Mai-Wa’azi 7:​16, 20 suka faɗa, ta yaya mutum zai iya nuna girman kai?

5 Masu son kai ne suke zama masu fahariya. Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa mu yi tunanin kanmu maimakon Jehobah, musamman sa’ad da muke da matsala. Alal misali, wani ya taɓa yi maka sharri ko rashin adalci? Idan haka ne, Shaiɗan zai so ka yi fushi da Jehobah ko ’yan’uwanka. Shaiɗan zai so ka ɗauka cewa hanyar da za ka magance matsalar ita ce yin abin da ke zuciyarka, maimakon ka bi ƙa’idodin da ke cikin Kalmar Allah.​—Karanta Mai-Wa’azi 7:​16, 20.

6. Mene ne za ka iya koya daga misalin wata ’yar’uwa a Holan?

6 Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa a Holan, wadda ta yi fushi da ’yan’uwan da ba ta son halinsu. Ta yanke shawara cewa za ta fita sha’anin ’yan’uwan. Ta ce: “Na kaɗaita kuma na ce ba zan iya gafarta musu ba. Sai na ce wa maigidana mu ƙaura zuwa wata ikilisiya dabam.” Amma da ta kalli shirin Maris na 2016 a Tashar JW, ta ga wasu shawarwari da aka bayar a kan abin da ya kamata mu yi idan ba ma son wani halin da ’yan’uwanmu suke da shi. ’Yar’uwar ta ƙara cewa: “Na ga cewa ina bukatar in nuna sauƙin kai kuma in tuna cewa ni ma ina kuskure, maimakon in yi ƙoƙarin tilasta wa ’yan’uwa a ikilisiya su canja halinsu. Shirin ya taimaka mini in mai da hankali a kan Jehobah da kuma ikonsa.” Shin ka fahimci abin da hakan yake nufi? Idan kana fuskantar wata matsala, ka riƙa tunani a kan Jehobah. Ka roƙe shi ya taimaka maka ka kasance da ra’ayi mai kyau game da ’yan’uwa. Jehobah ya san cewa suna kuskure, duk da haka, yana gafarta musu. Abin da yake so kai ma ka yi ke nan.​—1 Yoh. 4:20.

Ka duba sakin layi na 7

7. Mene ne ya faru da Sarki Uzziya?

7 Saboda girman kai, Sarki Uzziya na Yahudiya ya ƙi gargaɗi da aka ba shi kuma ya yi abin da ba a ba shi ikon yi ba. Da farko, Uzziya mutum ne da ya yi abubuwa da kyau sosai. Ya ci nasara a yaƙe-yaƙe da yawa, ya gina birane da yawa, kuma ya yi noma sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh ya sa ya yalwata.” (2 Tar. 26:​3-7, 10) Amma “sa’ad da Uzziya ya ga ya yi ƙarfi sosai, sai ya fara yin girman kai, wanda ya jawo masa halaka.” Dokar Jehobah ta ce firistoci ne kaɗai za su iya ƙona turare a haikali. Amma Sarki Uzziya ya yi ƙoƙarin ƙona turare a cikin haikali, abin da ba a ba shi iko ya yi ba. Jehobah ya yi fushi kuma ya buge shi da cutar kuturta. Har mutuwarsa, Uzziya bai warke daga wannan cutar ba.​—2 Tar. 26:​16-21.

8. Ta yaya bin abin da ke 1 Korintiyawa 4:​6, 7 zai taimaka mana mu guji zama masu girman kai?

8 Shin za mu iya zama masu girman kai har mu yi zunubi kamar yadda Uzziya ya yi? Ka yi la’akari da labarin José. Shi mai kuɗi ne sosai kuma shi dattijo ne a cikin ikilisiya. Yakan ba da jawabai a taron da’ira da taron yanki, kuma masu kula da da’ira sukan nemi shawara daga wurinsa. Ya ce: “Amma na dogara ga iyawata da kuma abin da na sani a rayuwa, maimakon in dogara ga Jehobah. Na ɗauka cewa ina da bangaskiya sosai, don haka, na ƙi bin gargaɗin Jehobah.” Hakan ya sa José ya yi wani zunubi mai tsanani kuma aka yi masa yankan zumunci. Amma yanzu ya yi shekaru da dawowa ƙungiyar Jehobah. Ya ce: “Jehobah ya koya mini cewa ba yin ayyuka a cikin ƙungiyarsa ne ya fi muhimmanci ba, amma yin abin da ya ce mu yi ne yake da muhimmanci.” Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ne ya ba mu kowace baiwar da muke da ita da kuma ayyukan da muke yi a ikilisiya. (Karanta 1 Korintiyawa 4:​6, 7.) Jehobah ba zai yi amfani da mu ba idan muna da girman kai.

HAƊAMA TARKO CE

Ka duba sakin layi na 9

9. Me haɗama ta sa Shaiɗan da Hauwa’u suka yi?

9 Idan ana maganar haɗama, wanda zai zo zuciyarmu shi ne Shaiɗan Iblis. Babu shakka, kafin Shaiɗan ya yi rashin aminci, Jehobah ya ba shi ayyuka masu muhimmanci sosai ya yi. Amma hakan bai ishe shi ba. Ya so a bauta masa, abin da Jehobah ne kaɗai ya cancanci a yi masa. Shaiɗan yana so mu zama kamar sa, shi ya sa yake ƙoƙarin ya sa mu biɗi ƙarin abubuwa. Ya soma yin hakan ne sa’ad da ya yi magana da Hauwa’u. Jehobah ya yi wa Hauwa’u da mijinta tanadin abinci a yalwace, wato ya ba su damar “ci daga kowane itace na gonar,” ban da guda ɗaya kawai. (Far. 2:16) Duk da haka, Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u. Sai ta ɗauka cewa tana bukatar ta ci ’ya’yan itacen da aka ce kar su ci. Hauwa’u ba ta gamsu da abin da aka ba ta ba, amma ta nemi ƙari. Mun san mummunan sakamako da hakan ya jawo. Hauwa’u ta yi zunubi kuma a ƙarshe ta mutu.​—Far. 3:​6, 19.

Ka duba sakin layi na 10

10. Mene ne ya faru sa’ad da Dauda ya yi haɗama?

10 Haɗama ta sa Sarki Dauda ya manta da abubuwan da Jehobah ya ba shi, kamar dukiya da matsayi da kuma nasara a kan maƙiyansa. Dauda da kansa ya ce abubuwa da Allah ya ba shi “sun fi gaban ƙirge!” (Zab. 40:5) Amma saboda haɗama, Dauda ya manta da abubuwan da Jehobah ya ba shi. Dauda ya auri mata da yawa, amma ya fara sha’awar matar wani duk da cewa Jehobah ya haramta hakan. Sunan matar Batsheba, mijinta kuma Uriya mutumin kabilar Hitti. Saboda son kai, Dauda ya kwana da Batsheba kuma ta yi ciki. Abin da Dauda ya yi yana da muni sosai, amma sai ya yi abin da ya fi hakan muni. Ya ƙulla a kashe Uriya. (2 Sam. 11:​2-15) Shin Dauda bai yi tunani a lokacin da yake yin abubuwan nan ba ne? Ya ɗauka cewa Jehobah ba zai iya ganin sa ba ne? Ko da yake Dauda ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Jehobah, ya yi haɗama, kuma hakan ya jawo masa matsaloli da yawa. Daga baya, Dauda ya amince cewa ya yi zunubi kuma ya tuba. Ya yi farin ciki sa’ad da Jehobah ya gafarta masa.​—2 Sam. 12:​7-13.

11. Kamar yadda Afisawa 5:​3, 4 suka nuna, me zai taimaka mana mu guji zama masu haɗama?

11 Me muka koya daga misalin Dauda? Mun koyi cewa za mu guji zama masu haɗama idan muna godiya don abubuwan da Jehobah ya yi mana tanadin su. (Karanta Afisawa 5:​3, 4.) Dole ne mu gamsu da abin da muke da shi. Idan muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, muna ƙarfafa su su riƙa tuna abu ɗaya da Jehobah ya yi musu kuma su gode masa. Idan mutum ya yi hakan a kowace rana, a mako ɗaya zai yi godiya a kan abubuwa bakwai. (1 Tas. 5:18) Abin da kake yi ke nan? Idan kana tunani a kan dukan abubuwa da Jehobah ya yi maka, hakan zai sa ka nuna godiya. Kuma idan kana nuna godiya, za ka gamsu da abin da kake da shi. Idan kuma ka gamsu da abin da kake da shi, ba za ka zama mai haɗama ba.

Ka duba sakin layi na 12

12. Mene ne haɗama ta sa Yahuda Iskariyoti ya yi?

12 Haɗama ce ta sa Yahuda Iskariyoti ya ci amanar Yesu. Da farko, shi mutumin kirki ne. (Luk. 6:​13, 16) Yesu ya zaɓe shi ya zama manzonsa, kuma babu shakka shi mutum ne da za a iya dogara da shi a lokacin. Shi ya sa aka ba shi riƙon jakar kuɗi. Yesu da manzanninsa sun yi amfani da kuɗin nan don biyan bukatunsu yayin da suke wa’azi. Kuɗin yana kamar gudummawa da ake bayarwa don tallafa wa aikin wa’azi da muke yi a yau. Amma daga baya, Yahuda ya soma satar kuɗin, duk da cewa ya sha jin yadda Yesu yake yi wa mutane gargaɗi a kan haɗama. (Mar. 7:​22, 23; Luk. 11:39; 12:15) Yahuda ya yi banza da gargaɗin.

13. A wane lokaci ne Yahuda ya nuna cewa ya riga ya zama mai haɗama?

13 Jim kaɗan kafin Yesu ya mutu, Yahuda ya nuna cewa ya riga ya zama mai haɗama. Yesu da almajiransa, haɗe da Maryamu da ’yar’uwarta Marta sun je gidan Siman kuturu. Yayin da suke cin abinci, sai Maryamu ta tashi ta zuba wani māi mai ƙanshi sosai da kuma tsada a kan Yesu. Sai Yahuda da sauran manzannin suka yi fushi sosai. Mai yiwuwa wasu almajiran Yesu sun ɗauka cewa zai fi kyau a yi amfani da kuɗin wajen tallafa wa mabukata. Amma wani dalili dabam ne ya sa Yahuda fushi. Shi “ɓarawo ne” kuma yana so ya saci kuɗin. Daga baya, haɗama ta sa Yahuda ya ci amanar Yesu a kan farashin bawa.​—Yoh. 12:​2-6; Mat. 26:​6-16; Luk. 22:​3-6.

14. Ta yaya wasu ma’aurata suka bi shawarar da ke Luka 16:13?

14 Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga kuɗi duk gaba ɗaya.” (Karanta Luka 16:13.) Wannan maganar gaskiya ce har a yau. Ka yi la’akari da misalin wasu ma’aurata a Romaniya da suka bi abin da Yesu ya faɗa. Sun sami aiki na ɗan lokaci a wata ƙasa mai arziki. Sun ce: “Mun riga mun ci bashin kuɗi mai yawa a banki, don haka, mun ɗauka cewa wannan aikin albarka ce daga wurin Jehobah da zai taimaka mana.” Amma mun ga cewa akwai wata matsala. Idan suka amince da aikin, hakan zai shafi hidimarsu ga Jehobah. Bayan da suka karanta wani talifi mai jigo, “Ka Kasance da Aminci da Zuciya Ɗaya” a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Agusta, 2008, sai suka yanke shawara. Sun ce: “Idan muka ƙaura zuwa wata ƙasa don mu nemi kuɗi, hakan zai shafi dangantakarmu da Jehobah, kuma zai nuna cewa dangantakarmu da Jehobah ba shi ne abin da ya fi muhimmanci a gare mu ba. Mun tabbata cewa dangantakarmu da Jehobah za ta yi sanyi.” Saboda haka, sun ƙi amincewa da aikin. Me ya faru bayan hakan? Maigidan ya samu wani aiki da zai iya biyan bukatunsu a ƙasarsu. Matar ta ce: “Jehobah yana kula da bayinsa.” Waɗannan ma’aurata suna farin ciki cewa sun mai da Jehobah Shugabansu, ba kuɗi ba.

KA GUJI TARKON SHAIƊAN

15. Me ya tabbatar mana cewa za mu iya kuɓuta daga tarkon Shaiɗan?

15 Mene ne za mu yi idan muka lura cewa mun soma girman kai ko kuma haɗama? Za mu iya canja halinmu! Bulus ya ce waɗanda suka fāɗa cikin tarkon Shaiɗan za su iya kuɓuta. (2 Tim. 2:26) Abin da ya faru da Dauda ke nan. Ya saurari gargaɗin Natan, ya tuba kuma ya gyara dangantakarsa da Jehobah. Jehobah ya fi ƙarfin Shaiɗan, don haka, idan muka amince da taimakonsa, za mu iya kuɓuta daga tarkon Shaiɗan.

16. Me zai taimaka mana mu guji tarkon Shaiɗan?

16 Hakika, zai fi dacewa mu guji zama masu haɗama ko kuma girman kai. Da taimakon Allah, za mu iya yin hakan. Kada mu ɗauka cewa ba za mu taɓa yin girman kai ko haɗama ba! Wasu da suka yi shekaru suna bauta wa Jehobah ma sun zama masu girman kai ko haɗama. A kullum, ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka bincika kanka don ka ga ko ka soma koyan munanan halayen nan. (Zab. 139:​23, 24) Ka yi iya ƙoƙarinka ka guji girman kai ko haɗama!

17. Me zai faru da Shaiɗan nan ba da daɗewa ba?

17 Shaiɗan ya yi shekaru da yawa yana farauta. Amma nan ba da daɗewa ba, za a hallaka shi. (R. Yar. 20:​1-3, 10) Muna ɗokin ganin wannan ranar. Kafin lokacin, ka ci gaba da guje wa tarkon Shaiɗan. Ka yi iya ƙoƙarinka don ka guji zama mai girman kai ko kuma haɗama. Ka ƙudura cewa ba za ka ‘ba Shaiɗan dama ba, shi kuwa zai guje maka.’​—Yak. 4:7.

WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama

^ sakin layi na 5 Shaiɗan mafarauci ne da ya ƙware. Yana so ya kama mu da tarkonsa ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko ba mu daɗe ba. A wannan talifin, za mu ga yadda Shaiɗan yake ƙoƙari ya yi amfani da girman kai da kuma haɗama ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Ƙari ga haka, za mu ga misalin wasu da suka zama masu girman kai da haɗama, kuma za mu ga yadda za mu guji fāɗawa a tarkon Shaiɗan.

^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: A wannan talifin, za mu tattauna game da girman kai, wato halin da yake sa mutum ya ɗauka cewa ya fi wani, da kuma haɗama, wato sha’awar kuɗi ko iko ko jima’i ko wasu abubuwa makamancin waɗannan.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa mai girman kai ya ƙi bin gargaɗin da aka yi masa. Wata ’yar’uwa da take da abubuwa da yawa tana neman ƙari.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani mala’ika da kuma Sarki Uzziya sun zama masu girman kai. Haɗama ce ta sa Hauwa’u ta ci ’ya’yan itacen da Allah ya haramta, Dauda ya yi zina da Batsheba, Yahuda kuma ya yi sata.