Me Za Ka Samu Idan Ka San Gaskiya?
Allah, wanda ba ya ƙarya, ya ba ka damar samun “rai na har abada.”—Yohanna 3:16.
ME KAKE BUKATAR KA YI?
Ka koyi abin da ke cikin Kalmar Allah.—Yohanna 17:3, 17.
Ka ƙudura cewa za ka yi wa Allah biyayya.—Maimaitawar Shari’a 30:19, 20.
Ka riƙa yin abin da Allah yake so a kullum.—Yaƙub 1:25.
Shaidun Jehobah a ko’ina a duniya suna amfana daga abin da suke koya a Littafi Mai Tsarki. Za su so su koya maka abin da suka koya.
Don ka koyi ƙarin gaskiya daga Littafi Mai Tsarki, ka duba ƙasidar nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa ta. Za ka iya samunt a dandalin www.pr418.com/ha.