Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

HASUMIYAR TSARO Na 1 2021 | Amfanin Yin Addu’a

Ka taɓa ji kamar Allah ba ya amsa addu’arka? Ba kai kaɗai kake jin haka ba. Mutane da yawa suna roƙon Allah ya taimaka musu, amma sun ci gaba da fama da matsaloli. Talifofin da za mu tattauna a gaba za su taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa Allah yana jin addu’o’inmu. Ƙari ga haka, za su nuna mana abin da ya sa Allah ba ya amsa wasu addu’o’in, da kuma yadda za ka yi addu’a don Allah ya amsa.

 

Ra’ayoyin Mutane Game da Yin Addu’a

Shin, addu’a kyauta ce daga Allah, ko kuma al’ada ce kawai da mutane suke yi?

Allah Yana Jin Addu’o’inmu Kuwa?

Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Allah yana jin addu’armu muddin mun yi hakan a hanyar da ta dace.

Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana irin addu’o’in da Allah zai amsa da wadanda ba zai amsa ba.

Ta Yaya Za Ka Yi Addu’a Kuma Allah Ya Amsa?

Za ka iya yin addu’a a duk inda kake da kuma a kowane lokaci, a cikin zuciyarka ko ka furta a ji. Yesu ya taimaka mana mu san abin da za mu fada.

Ta Yaya Yin Addu’a Zai Amfane Ka?

Ta yaya yin addu’a zai taimaka maka sa’ad da kake fuskantar matsaloli

Shin, Allah Yana Jin Addu’arka?

Littafi Mai Tsarki ya ce idan kana addu’a Allah yana ji kuma yana so ya taimaka maka.