Ta Yaya Yin Addu’a Zai Amfane Ka?
Da Pamela ta kamu da cutar kansa, ta je asibiti. Ban da haka, ta yi addu’a Allah ya taimaka mata ta jimre. Addu’a ta taimaka mata kuwa?
Pamela ta ce: “A lokacin da nake jinyar kansar, nakan ji tsoro sosai.” Ta kuma ce, “amma idan na yi addu’a ga Jehobah, hankalina yakan kwanta kuma nakan daina jin tsoro. Har yanzu ina fama da zafin ciwon, amma yin addu’a yana taimaka min kada in yi sanyin gwiwa. Idan mutane suka tambaye ni ya jiki, nakan ce, ‘Ina fama amma ina farin ciki.’ ”
Ba sai mun jira muna bakin mutuwa kafin mu yi addu’a ba. Dukanmu muna fuskantar matsaloli iri-iri kuma muna bukatar taimako don mu jimre. Kana ganin addu’a za ta iya taimakawa?
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Danƙa wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai, ko kaɗan ba zai bar masu adalci su jijjigu ba.” (Zabura 55:22) Hakika, wannan alkawari mai ban ƙarfafa ne! Ta yaya addu’a za ta taimaka maka? Idan ka yi addu’a a hanyar da ta dace, Allah zai taimaka maka da matsalolinka.—Don ƙarin bayani, ka dubi akwatin nan, “ Me Za Ka Samu Idan Ka Yi Addu’a?”