HASUMIYAR TSARO Na 1 2022 | Yadda Za A Magance Kiyayya
Ana nuna ƙiyayya sosai a wannan duniyar tamu. Kuma mutane suna nuna ƙiyayyarsu a hanyoyi da dama. Alal misali, wasu sukan nuna wa mutane bambanci, ko su yi musu bakar magana, ko su kai musu hari don su cutar da su. Akwai mafita kuwa? Talifofin da ke wannan mujallar, za su bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da zai taimaka maka ka daina nuna ƙiyayya. Ban da haka, za su nuna abin da Allah zai yi a nan gaba don ya magance matsalar ƙiyayya har abada.
Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!
Me ke sa kiyayya ta ci gaba? A wadanne hanyoyi ne ake yawan nuna kiyayya?
Me Ya Sa Kiyayya Ta Yi Yawa Haka?
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana asalin kiyayya, da abin da ya sa mutane suke saurin kin juna, da abin da ya sa take ci gaba.
Abin da Mutum Zai Yi don Ya Daina Kin Mutane
Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mutane da yawa su gyara halinsu.
ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE
1 | Kar Ka Nuna Bambanci
Allah ba ya nuna bambanci, kai ma ka daina wannan halin don ka daina kin mutane.
ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE
2 | Kar Ka Rama da Mugunta
Ka tuna cewa Allah ya kusan magance dukan mugunta, don haka kar ka yi ramako.
ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE
3 | Ka Cire Kiyayya Daga Zuciyarka
Ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki don ka cire kiyayya daga tunaninka.
ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE
4 | Ka Nemi Taimakon Allah don Ka Daina Kin Mutane
Ruhu mai tsarki na Allah zai iya sa ka samu halaye masu kyau da za su taimaka maka ka daina kin mutane.
Lokacin da Za A Daina Kiyayya Kwata-kwata!
Ta yaya za a kawo karshen kiyayya gabaki daya?
Kiyayya Tana a Ko’ina a Duniya
Me mutum zai yi don ya daina nuna kiyayya? Akwai mutane da yawa a fadin duniya da suka daina nuna kiyayya. Kuma a kwana a tashi, kiyayya za ta zama labari.