ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE
3 | Ka Cire Kiyayya Daga Zuciyarka
Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
“Ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku. Ta haka za ku iya tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.”—ROMAWA 12:2.
Abin da Ayar Take Nufi:
Irin tunani da muke yi yana da muhimmanci a wurin Allah. (Irmiya 17:10) Kuma ƙiyayya takan soma a tunanin zuciyar mutum ne, kafin ma ya faɗi wani abu ko ya aikata shi. Saboda haka, idan muna so mu daina ƙin mutane, dole mu daina tunanin abubuwa da za su sa mu ƙi su. Abin da zai sa mu “canja” ke nan.
Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:
Ka bincika irin abubuwan da kake tunani a kai da kuma yadda kake ganin mutane, musamman waɗanda ƙasarsu ko ƙabilarsu ba ɗaya ba ne da naka. Ka tambayi kanka: ‘Yaya nake ganinsu? Abin da na sani game da su ne ya sa nake da wannan ra’ayin? Ko na ƙi jininsu ne kawai don sun bambanta da ni?’ Ka guji kallon bidiyoyi ko karanta duk wani bayani da ake yi da ke zuga mutane su nuna ƙiyayya ko su yi mugunta. Har da waɗanda ake yaɗawa ta dandalin sada zumunta.
Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu cire ƙiyayya daga tunanin zuciyarmu
Bai da sauki mutum ya bincika kansa ya san ko tunaninsa da yadda yake ji a ransa ya dace ko bai dace ba. Amma Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu “gane duk tunani da nufin da suke cikin zuciya.” (Ibraniyawa 4:12) Don haka, ka ci gaba da yin binciken Littafi Mai Tsarki don ka ga ko tunaninka ya jitu da abin da ya ce. Idan ka ga cewa tunanin da kake yi bai dace ba, ka yi iya ƙoƙarinka ka yi gyara. Maganar Allah za ta iya taimaka mana mu daina ƙin mutane ko da ƙiyayyar ta yi “ƙarfi” a zukatanmu.—2 Korintiyawa 10:4, 5.