ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE
1 | Kar Ka Nuna Bambanci
Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
“Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.”—AYYUKAN MANZANNI 10:34, 35.
Abin da Ayar Take Nufi:
Jehobah * ba ya damuwa da ƙasar da mutum ya fito, ko ƙabilarsa, ko launin fatarsa ko kuma al’adarsa. Abin da ya fi muhimmanci a gare shi, shi ne ainihin halin mutum. “Mutum yakan duba yadda mutum yake daga waje, amma Yahweh yakan dubi zuciya ne.”—1 Sama’ila 16:7.
Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:
Ba za mu iya sanin tunanin zuciyar mutane ba. Amma za mu iya yin koyi da Allah ta wurin yi musu kirki ba tare da nuna musu bambanci ba. Ka yi ƙoƙari ka san halin mutum maimakon ka ce, ‘Haka mutanen nan suke.’ Ka tuna cewa kowa yana da nasa halin. Idan ka lura cewa kana ƙin wasu mutane don inda suka fito, ko ƙabilarsu, ka roƙi Allah ya taimake ka ka daina wannan halin. (Zabura 139:23, 24) Idan ka roƙi Allah ya taimake ka ka daina nuna bambanci, ba shakka zai ji addu’arka kuma zai taimaka maka ka yi hakan.—1 Bitrus 3:12.
^ sakin layi na 6 Jehobah ko kuma Yahweh shi ne sunan Allah.—Zabura 83:18.
“Ban taɓa zaman lafiya tare da bature haka ba . . . Yanzu na shiga cikin iyali da ke da ’yan’uwa a duk faɗin duniya.” —TITUS