Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!

Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!

An taɓa nuna maka ƙiyayya?

Ko ba a taɓa ƙin ka ba, ba mamaki ka taɓa ganin ana ƙin mutane. Mun saba jin labaran mutane da aka ƙi jininsu don ƙasarsu, ko ƙabilarsu, da dai sauransu. Shi ya sa a wasu wurare, gwamnati take kafa dokoki don a hukunta duk wanda ya cutar da mutum sakamakon irin wannan ƙiyayyar.

A yawancin lokaci, mutane suna ƙin waɗanda suke ƙinsu. Idan aka cuce su, sukan rama. Da haka sai ka ga mutane sun ci gaba da ƙin juna kuma suna cutar da junansu.

Ƙila kai ma an taɓa nuna maka bambanci, ko an ƙi jininka, ko an yi maka dariya, ko an zage ka, ko kuma an yi maka barazana. Ban da haka, ƙiyayya takan sa mutane su aikata mugunta iri-iri. Alal misali, ƙiyayya takan sa a zalunci mutane, a kai musu hari ko a yi musu ɓarna, ko a yi wa mutum fyaɗe, ko a kashe shi, har ma a shiga kisan ƙāre dangi.

Wannan mujallar za ta bayyana yadda za a daina nuna ƙiyayya. Kuma za ta ba da amsar tambayoyin nan:

  • Me ya sa ƙiyayya ta yi yawa haka?

  • Me mutum zai yi don ya daina nuna ƙiyayya?

  • Shin lokaci na zuwa da ba za a sake nuna ƙiyayya ba?