Allah Ya Damu da Kai
A LITTAFI MAI TSARKI ne za mu iya samun shawara mafi kyau, domin Kalmar Allah ce. Ba littafin kiwon lafiya ba ne amma zai taimaka mana mu san yadda za mu bi da yanayoyi masu wuya, da matsalolin da suke damunmu a zuciya da waɗanda suke damunmu a jiki da kuma ƙwaƙwalwa.
Mafi muhimmanci ma, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Mahaliccinmu Jehobah a ya san abubuwan da suke damunmu fiye da kowa. Yana shirye ya taimaka mana da duk wata matsalar da muke fama da ita. Ga wasu ayoyi daga Littafi Mai Tsarki da za su iya kwantar mana da hankali:
“Ga waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa, Yahweh yana kusa da su, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya.”—ZABURA 34:18.
“Gama ni Yahweh Allahnka ne, ina riƙe da hannun damanka. Ni ne kuma nake ce maka, ‘Kada ka ji tsoro, ni ne mai taimakonka.’”—ISHAYA 41:13.
Amma ta yaya Jehobah zai taimaka mana idan muna fama da matsalar ƙwaƙwalwa? A talifofi na gaba, za ka ga yadda Jehobah ya damu da mu a hanyoyi da dama.
a Jehobah ko kuma Yahweh shi ne sunan Allah.—Zabura 83:18.