Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

A duk faɗin duniya, miliyoyin mutane suna fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Manya da yara, ko da yaya matsayinsu yake ko iliminsu ko addininsu ko daga ina ne suka fito, dukansu suna iya fama da ciwon nan. Me ake nufi da matsalar ƙwaƙwalwa kuma ta yaya take shafan mutane? A wannan mujallar, za a tattauna muhimmancin neman taimako daga asibiti idan mutum yana fama da ciwon nan da kuma yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimakawa a hanyoyi da dama.