4 | Za Mu Sami Shawara Mai Kyau a Cikin Littafi Mai Tsarki
LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Duk Rubutacciyar Maganar Allah . . . tana . . . da amfani.”—2 TIMOTI 3:16.
Abin da Hakan Yake Nufi
Ko da yake Littafi Mai Tsarki ba littafin kiwon lafiya ba ne, amma shawarar da ke ciki za ta iya taimaka wa wanda yake fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Ga wasu misalai.
Yadda Yin Hakan Zai Taimaka
“Masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.”—MATIYU 9:12.
Littafi Mai Tsarki ya yarda cewa za mu iya neman taimakon likita. Mutane da yawa da suke fama da matsalar ƙwaƙwalwa sun sami taimako, ta wajen samun ingantattun bayanai game da cutar kuma sun nemi taimakon likita.
“Wasa jiki tana da amfaninta.”—1 TIMOTI 4:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
Yin abubuwan da za su taimaka wa lafiyar jikinka, za su taimaka maka ka kasance da lafiyar ƙwaƙwalwa. Abubuwan nan sun ƙunshi, motsa jiki a kai a kai, da cin abinci mai gina jiki, da kuma samun isashen barci.
“Zuciya mai murna magani ne mai kyau, amma zuciya mai baƙin ciki tana shanye ƙarfin mutum.”—KARIN MAGANA 17:22.
Karanta ayoyi masu ban ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki da kuma kafa maƙasudin da za ka
iya cim ma wa, za su taimaka maka ka riƙa farin ciki. Idan ka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da suke faruwa a rayuwarka, kuma ka yarda cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba, hakan zai taimaka maka ka san yadda za ka jimre da matsalar ƙwaƙwalwa.“Mai sauƙin kai mai hikima ne.”—KARIN MAGANA 11:2.
Wataƙila ka gano cewa, ba za ka iya yin abubuwan da kake so da kanka ba. Don haka, ka yarda wasu su taimaka maka. ꞌYanꞌuwa da abokan arziki ƙila za su so su taimaka maka amma ba su san me za su iya yi ba. Ka gaya musu irin taimakon da kake bukata. Kada ka yi tunani cewa za su yi abin da ya fi ƙarfinsu, kuma ka riƙa godiya don abubuwan da suka yi maka.
Yadda Shawarar da Ke Littafi Mai Tsarki Yake Taimaka Wa Masu Matsalar Nan
Wata mai suna Nicole a da take fama da ciwon bipolar, ta ce: “Na ji a jikina cewa ina da matsala, sai na je na ga likita. Likitar ta gano abin da ke damuna. Hakan ya sa na gane ainihin abin da ke damuna kuma na gano irin jinyar da zan iya zaɓa don in kula da lafiyata.”
Wani mai suna Peter da ke fama da ciwon baƙin ciki mai tsanani ya ce: “Na gano cewa karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai tare da matata yana taimaka min in soma kowace rana da raꞌayin da ya dace. A yawancin ranakun da ba na jin daɗi kuma, nakan samo ayar da za ta ƙarfafa ni.”
Wata mai suna Ji-yoo da take fama da matsalar cin abinci ta ce: “Yana min wuya in gaya wa mutane abin da nake fama da shi don ina jin kunya. Wata ƙawata ta saurare ni sosai kuma ta tausaya min don ta fahimci yadda nake ji. Ta taimaka min in sami sauƙi sosai don ba ta bar ni ni kaɗai ba.”
Wani mai suna Timothy da ya yi fama da cutar raɗaɗi wato OCD ya ce: “Littafi Mai Tsarki ya taimaka min in daidaita raꞌayina game da yadda nake yin aiki da kuma samun hutu. Shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki sun taimaka min in san yadda zan riƙa jimrewa da matsalolina.”
a An canja sunayen.