Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO

Me Ya Sa Yesu Ya Sha Wahala Kuma Ya Mutu?

Me Ya Sa Yesu Ya Sha Wahala Kuma Ya Mutu?

‘Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi.’​—Romawa 5:12

Idan wani ya ce maka, “Za ka so ka rayu har abada kuwa?” Me za ka ce masa? Babu shakka, mutane da yawa za su ce e, amma za su ji cewa hakan ba zai taɓa yiwuwa ba. Mutuwa ta zama ruwan dare gama gari a yau, wasu sun ce rigar kowa ce.

Amma wace amsa ce za ka bayar idan an tambaye ka cewa, “Za ka so ka mutu?” Babu shakka, mutane da yawa za su ce a’a. Me ya sa? Domin kome tsananin wahalar da muke sha, muna son mu ci gaba da rayuwa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya halicci mutane da marmarin yin rayuwa. Ya ce Allah ya ‘sa madawwaman zamanai a cikin zuciyarmu.’​—⁠Mai-Wa’azi 3:⁠11.

Amma a yau, mutane ba sa rayuwa har abada. Mene ne ya jawo hakan? Shin Allah ya ɗauki mataki don ya magance matsalolinmu? Amsoshin da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna da ban ƙarfafa kuma sun nuna dalilan da suka sa Yesu ya sha wahala kuma ya mutu.

ME YA SA KOME YA LALACE?

Littafin Farawa surori ɗaya zuwa uku sun yi bayani cewa Allah ya halicci Adamu da Hawwa’u, ya ba su gatan yin rayuwa har abada kuma ya ba su dokokin da za su bi don su ci gaba da moran wannan rayuwar. Bayan haka, littafin ya bayyana yadda suka yi rashin biyayya ga Allah kuma suka yi hasarar wannan gatan. Littafi Mai Tsarki ya faɗi labarin kai tsaye kuma hakan ya sa wasu sun ce tatsuniya ce. Amma littafin Farawa yana kamar Linjila domin labaran da ke cikinsa gaskiya ne. *

Mene ne sakamakon rashin biyayyar da Adamu ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.’ (Romawa 5:12) Adamu ya yi zunubi sa’ad da ya yi rashin biyayya ga Allah. Hakan ya sa ya yi hasarar yin rayuwa har abada kuma daga baya ya mutu. Mun gāji zunubi daga wurinsa domin mu ‘ya’yansa ne. A sakamakon haka, muna ciwo da tsufa da kuma mutuwa. Wannan bayanin da aka yi ya jitu da abin da ‘yan kimiyya suke koyar a yau game da gādan hali da yara suke yi daga iyayensu. Shin da akwai wani matakin da Allah ya ɗauka don ya magance wannan matsalar?

MATAKIN DA ALLAH YA ƊAUKA

Allah ya yi shirye-shirye don ya ‘yantar da mutane daga zunubin da suka gāda daga Adamu kuma su sami zarafin yin rayuwa har abada. Ta yaya Allah ya cim ma hakan?

Littafin Romawa 6:23 ya ce sakamakon “zunubi mutuwa ne.” Hakan ya nuna cewa mutuwa ce sakamakon zunubi. Adamu ya yi zunubi kuma ya mutu. Hakazalika, muna zunubi kuma muna samun sakamakon zunubi, wato mutuwa. An haife mu cikin wannan yanayin ko da yake ba mu yi wani laifi ba. Amma Allah ya ƙaunace mu kuma ya aiko da Ɗansa, Yesu, don ya kawar mana da sakamakon “zunubi.” Ta yaya hakan ya yiwu?

Mutuwar Yesu ta ba mu zarafin yin rayuwa har abada

Da yake mutum ɗaya, wato Adamu ne ya jawo mana zunubi da kuma mutuwa ta rashin biyayyarsa, ana bukatar kamiltaccen mutum ɗaya ya kasance da aminci har mutuwa don ya cece mu daga sakamakon zunubi. Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa: “Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci.” (Romawa 5:​19, Littafi Mai Tsarki) Yesu ne wannan “mutum ɗaya” da aka ambata. Ya bar sama, ya zama kamiltaccen mutum * kuma ya mutu dominmu. Hakan ya sa mun sami zarafin samun dangantaka mai kyau da Allah da kuma yin rayuwa har abada a nan gaba.

ABIN DA YA SA YESU YA SHA WAHALA KUMA YA MUTU

Me ya sa ya zama dole Yesu ya mutu don a cim ma hakan? Shin Allah Maɗaukaki ba zai iya furta cewa dukan ‘ya’yan Adamu su rayu har abada ba? Babu shakka, yana da ikon yin hakan. Amma hakan zai saɓa wa dokar da ya kafa cewa sakamakon zunubi mutuwa ne. Wannan ba dokar da za a iya canjawa ba ne idan aka ga dama. Amma dokar ta nuna cewa Allah mai adalci ne.​—⁠Zabura 37:⁠28.

Allah yana bin ƙa’idarsa ta adalci a wannan batun, amma mutane suna iya tunani ko Allah zai bi wannan ƙa’idar a wasu batutuwa. Alal misali, shin zai bi wannan ƙa’idar wajen sanin ‘yan Adam da suka cancanci samun rai na har abada? Zai cika alkawuransa kuwa? Da yake Allah yana bin wannan ƙa’idar don ya tabbatar da cewa mun sami ceto, hakan ya nuna mana cewa zai ci gaba da yin abin da ya dace.

Allah ya yi amfani da fansar Yesu don ya ba mu zarafin samun rai na har abada cikin Aljanna a duniya. Ka yi la’akari da kalmomin da ke Yohanna 3:16: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Mutuwar Yesu ta nuna cewa Allah yana bin ƙa’idarsa ta adalci kuma yana ƙaunar mutane sosai.

Amma, me ya sa Yesu ya sha wahala kuma ya mutu kamar yadda aka bayyana a cikin Linjila? Yadda Yesu ya fuskanci wahala mai tsanani kuma ya kasance da aminci, ya nuna cewa abin da Shaiɗan ya faɗa cewa mutane ba za su kasance da aminci ga Allah ba idan suka fuskanci yanayi mai wuya ba gaskiya ba ne. (Ayuba 2:​4, 5) An ga kamar abin da Shaiɗan ya faɗa gaskiya ne sa’ad da ya sa Adamu, wanda shi kamiltaccen mutum ne ya yi zunubi. Amma Yesu, wanda shi ma kamiltacce ne ya kasance da aminci duk da matsanancin yanayin da ya fuskanta. (1 Korintiyawa 15:45) Yin hakan ya nuna cewa da Adamu ya kasance da aminci da a ce ya so ya yi hakan. Yesu ya kafa mana misali mai kyau ta wajen jimre da matsaloli. (1 Bitrus 2:21) Allah ya albarkaci Yesu don biyayyar da ya yi ta wajen ba shi rai marar mutuwa a sama.

YADDA ZA KA AMFANA

Yesu ya mutu da gaske kuma mutuwarsa ta sa mun sami zarafin yin rayuwa har abada. Shin kana son ka rayu har abada? Yesu ya faɗi abin da za mu yi don mu rayu har abada. Ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”​—Yohanna 17:3.

Mawallafan wannan mujallar suna son ka koyi wasu abubuwa game da Jehobah, wanda shi ne Allah na gaskiya da kuma Ɗansa, Yesu Kristi. Shaidun Jehobah da ke yankinku za su so su taimaka maka. Za ka kuma amfana ta wajen shigan dandalin nan www.pr418.com/ha.

^ sakin layi na 8 Ka duba “The Historical Character of Genesis,” (Abubuwan da Suka Nuna Cewa Littafin Farawa Gaskiya Ne) a shafuffuka na 922 na Insight on the Scriptures, Littafi na 1, Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.

^ sakin layi na 13 Allah ya kawar da ran Yesu daga sama zuwa mahaifar Maryamu kuma ruhu mai tsarki na Allah ya kāre Yesu don kada ya gāji ajizanci daga Maryamu.​—Luka 1:31, 35.