“Abin da Zai Faru A Nan Gaba”
Ka taɓa tunanin yadda rayuwarka da ta iyalinka za ta kasance a nan gaba? Shin kana ganin za ta yi kyau ne ko kuma muni? Za ka yi rayuwa na dogon lokaci ne ko kuma na ɗan lokaci? Mutane sun yi shekaru da yawa suna tunani a kan waɗannan tambayoyin.
A yau, masana suna yin bincike a kan abubuwan da suke faruwa a duniya kuma hakan yana sa su faɗi abin da suke ganin zai faru a nan gaba. Ko da yake wasu abubuwan da suke faɗa suna faruwa da gaske, amma wasu kuma ba sa faruwa. Alal misali, a shekara ta 1912, Guglielmo Marconi, wanda ya kirkiro rediyo ya ce: “Ci gaban da aka samu a fannin fasaha zai sa a daina yaƙi.” Wani shugaban kamfanin Decca Record da ya bar mawaƙan Beatles a shekara ta 1962, ya gaskata cewa a nan gaba, ba za a sami rukunonin mawaƙa da suke kaɗa jita ba.
Mutane da yawa suna zuwa wurin masafa don su san abin da zai faru a nan gaba. Wasu suna neman shawara daga wurin masanan taurari kuma akan saka bayanan sihiri a jaridu da mujallu. Ƙari ga haka, wasu suna zuwa wurin masu dūba don su san abin da zai faru da su a nan gaba. Masu dūba suna da’awar cewa za su iya sanin rayuwar mutum a nan gaba ta wajen amfani da katin tarot da wasu lambobi ko kuma zanen tafin hannun mutum.
Wasu mutane ma a zamanin dā sun je wurin bokaye da malamai don su san abin da zai faru a nan gaba. Alal misali, Sarkin Lydia mai suna Croesus ya aika ma wata boka a Delphi da ke Hellas kyaututtuka masu yawa don yana so ya san abin da zai faru da shi idan ya yi yaƙi da Sarkin Fasiya, wato Sayirus. Bokar ta gaya wa Croesus cewa zai halaka “wata daula mai girma” idan ya yi yaƙi da Sayirus. Hakan ya ba wa Croesus ƙarfin gwiwa kuma ya je don ya yaƙi Sayirus domin yana tsammanin cewa shi ne zai yi nasara. Amma a ƙarshe, daularsa ce aka halaka.
Abin da bokar ta gaya wa sarki Croesus bai da wani amfani. Me ya sa? Domin ta yi amfani da dabara wajen gaya masa cewa zai halaka wata daula mai girma amma ba ta faɗi sunan daular ba. Bayanin da ta yi ya yaudari Croesus kuma ya sa ya rasa kome da yake da shi. Shin za mu ce waɗanda suke amfani da hanyoyi dabam-dabam a yau don su san abin da zai faru a nan gaba suna yin nasara kuwa?