Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Alkawuran da Za Su Cika

Alkawuran da Za Su Cika

Ana wa’azin Mulkin Allah a dukan duniya kamar yadda Yesu ya annabta cewa za a yi. (Matiyu 24:14) Littafin Daniyel ya gaya mana cewa Mulkin, gwamnatin Allah ne. Sura ta biyu na littafin yana ɗauke da labarin gwamnatoci ko mulkoki tun daga zamanin Babila ta dā har zuwa yanzu. Aya ta 44 ta annabta abin da zai faru a nan gaba cewa:

“Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a ba waɗansu su gāje shi ba. Mulkin nan zai farfashe dukan waɗannan mulkokin, ya kawo ƙarshensu. Amma mulkin nan zai kasance har abada.”

Wannan annabcin da wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Mulkin Allah zai maye gurbin gwamnatocin ’yan Adam. Ban da haka ma, sun nuna cewa zai daidaita kome a duniya. Yaya mutane za su yi rayuwa sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta? Ga wasu annabcin da za su cika ba da daɗewa ba.

  • BA ZA A SAKE YIN YAƘI BA

    Zabura 46:9: “[Allah] ya tsai da yaƙe-yaƙe a dukan duniya, ya kakkarye baka, ya lalatar da māshi, ya ƙone garkuwa da wuta.”

    Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance idan ana amfani da kuɗaɗe da basira a hanyar da ’yan Adam za su amfana maimakon a yi amfani da su wajen ƙera makamai da ake kashe mutane da su. Alkawarin da Allah ya yi na kawar da yaƙi zai cika a Mulkinsa.

  • BA ZA A SAKE YIN CIWO BA

    Ishaya 33:24: “Ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’”

    Ka yi tunanin lokacin da mutanen duniya ba za su riƙa fama da ciwon zuciya da ciwon kansa da zazzabin cizon sauro da kuma wasu cututtuka ba. A lokacin, ba wanda zai bukaci asibitoci balle ma magunguna. A nan gaba, mazaunan duniya za su zama da ƙoshin lafiya.

  • BA ZA A SAKE YIN YUNWA BA

    Zabura 72:16: Za a “sami hatsi a yalwace a ƙasar, a sa amfanin gona ya rufe kan tuddai.”

    Ƙasa za ta ba da amfani sosai kuma kowa zai sami abinci a yalwace. Ba za a sake yin yunwa ba sam.

  • BA BAƘIN CIKI DA KUKA DA KUMA MUTUWA

    Ru’uyar da Aka Yi Wa Yohanna 21:4: “[Allah] zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun ɓace.”

    Hakan yana nufin cewa mutane za su yi rayuwa har abada a aljanna a duniya! Wannan shi ne alkawarin da Jehobah, Mahaliccinmu ya yi mana.

“ZA TA YI ALBARKA”

Shin kana ganin alkawuran nan za su cika kuwa? Yawancin mutane sun yarda cewa yadda aka kwatanta rayuwa a Littafi Mai Tsarki abin sha’awa ne sosai, duk da haka, wasu suna ganin cewa ba zai yiwu mutane su yi rayuwa a duniya har abada ba. Hakan ba abin mamaki ba ne domin babu wani ɗan Adam da ya taɓa yin rayuwa kamar haka da zai ba mu labari.

Mutane suna fama da zunubi da mutuwa. Ban da haka ma, sun daɗe suna baƙin ciki da wahala da bala’i har sun saba da hakan kuma suna ganin haka rayuwa take. Amma ba irin wannan rayuwar ce Mahaliccinmu, Jehobah ya nufi ’yan Adam da ita ba.

Don Allah ya taimaka mana mu gaskata da dukan alkawuran da ya yi, ya ce game da hakan: “Ba za ta koma wurina wofi ba, amma za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.”​—Ishaya 55:​11, Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah, Allah ne “da ba ya ƙarya.” (Titus 1:2) Da yake ya yi wannan alkawarin game da nan gaba, zai dace mu yi wannan tambayar: Shin zai yiwu ’yan Adam su yi rayuwa har abada a Aljanna a nan duniya? Me za mu yi don mu amfana daga alkawuran nan da Allah ya yi? Za ka sami bayanin da zai ba da amsoshin waɗannan tambayoyin a shafofi na gaba a wannan mujallar.