Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

A ƙarƙashin sarautar Allah, halittunsa sun kasance da haɗin kai da kwanciyar hankali

Me Ya Sa Muke Bukatar Mulkin Allah?

Me Ya Sa Muke Bukatar Mulkin Allah?

A lokacin da aka halicci Adamu da Hauwa’u, Mahaliccinmu mai suna Jehobah ne kaɗai yake sarauta. Duk abin da ya yi wa Adamu da Hauwa’u a lokacin, ya yi ne don yana ƙaunarsu. Ya shirya wani lambu mai kyau da ake kira Eden, don su zauna a ciki, kuma ya ba su abinci a yalwace. Ƙari ga haka, ya ba su aikin da za su ji daɗin yi. (Farawa 1:​28, 29; 2:​8, 15) Da a ce Adamu da Hauwa’u sun ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin sarautar Allah, da sun zauna lami lafiya.

Adamu da Hauwa’u sun ƙi sarautar Allah

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wani mala’ika ya yi tawaye kuma ya ce Allah bai cancanci ya yi mulki a kan ’yan Adam ba. Wannan mala’ikan ne ake kira Shaiɗan Iblis. Ya ce mutane za su fi jin daɗi idan ba sa ƙarƙashin ja-gorancin Allah da kuma sarautarsa. Abin takaici shi ne, iyayenmu na farko, wato Adamu da Hauwa’u sun yarda da ƙaryar da Shaiɗan ya yi, kuma su ma suka yi wa Allah tawaye.​—Farawa 3:​1-6; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9.

Tawayen da Adamu da Hauwa’u suka yi ya sa Allah ya kore su daga cikin Aljanna inda suke zama, kuma sun rasa damar yin rayuwa har abada a cikin ƙoshin lafiya. (Farawa 3:​17-19) Abin da suka yi ya shafi ’ya’yan da suka haifa daga baya. Littafi Mai Tsarki ya ce zunubin da Adamu ya yi ne ya sa “zunubi ya shigo cikin duniya . . . , zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa.” (Romawa 5:12) Wata babbar matsala kuma da zunubi ya jawo mana ita ce, yadda waɗanda suka “sami mulki” suna sa mutane “su sha wuya a ƙarƙashinsu.” (Mai-Wa’azi 8:9) Hakan ya nuna cewa muddin ’yan Adam ne suke mulki, za a riƙa samun matsala.

YADDA MUTANE SUKA FARA SARAUTA

Nimrod ya yi wa Jehobah tawaye

Nimrod ne mutum na farko da Littafi Mai Tsarki ya ce ya yi sarauta, kuma ya yi wa Jehobah tawaye. Ya nuna cewa ba ya so Allah ya yi mulki a kan ’yan Adam. Tun daga zamanin Nimrod, mutane masu iko suna amfani da ikonsu su cuci mutanen da ke ƙarƙashinsu. Wajen shekaru 3,000 da suka shige, Sarki Sulemanu ya rubuta cewa: “Na ga hawayen waɗanda ake yi musu danniya, babu mai yi musu ta’aziyya. Masu yin danniyar su ne suke da iko. Waɗanda ake danne su, babu mai yi musu ta’aziyya.”​—Mai-Wa’azi 4:1.

Abin da ke faruwa ke nan har wa yau. A 2009, wata mujallar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rashin adalcin gwamnatoci “yana cikin abubuwan da suke jawo matsaloli a duniya.”

LOKACIN ƊAUKAN MATAKI!

Duniya tana bukatar shugaba nagari da kuma gwamnati mai adalci. Kuma abin da Mahaliccinmu ya yi mana alkawarinsa ke nan.

Ko gwamnatocin ’yan Adam da suka yi ƙoƙari ma sun kasa magance matsalolin da suke damun ’yan Adam

Allah ya kafa wani Mulki, ko gwamnati da za ta sauya duka mulkokin ’yan Adam, kuma “mulkin nan [ne kaɗai] zai kasance har abada.” (Daniyel 2:44) Mulkin nan ne miliyoyin mutane sun daɗe suna addu’a ya zo. (Matiyu 6:​9, 10) Amma ba Allah ne zai yi mulki da kansa ba. Ya riga ya zaɓi wani da ya taɓa yin rayuwa a nan duniya ya zama Sarkin Mulkin. Wane ne Allah ya zaɓa?