Yaushe Ne Mulkin Allah Zai Zo Duniya?
Wasu mabiyan Yesu sun so su san lokacin da Mulkin Allah zai zo duniya. Amma Yesu ya gaya musu cewa ba za su iya sanin ainihin ranar da mulkin zai soma sarauta a kan duniya ba. (Ayyukan Manzanni 1:6, 7) Amma kafin ya mutu, ya gaya musu cewa akwai abubuwa da za su faru a lokaci ɗaya da za su sa mabiyansa su san cewa “Mulkin Allah ya yi kusa.” Kuma a lokacin ne Mulkin Allah zai soma sarauta a kan duniya.—Luka 21:31.
WAƊANNE ABUBUWA NE YESU YA CE ZA SU FARU?
Yesu ya ce: “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi mummunar rawar ƙasa, da yunwa da bala’i a wurare dabam-dabam.” (Luka 21:10, 11) Idan duka abubuwan nan sun auku a lokaci ɗaya, za a gane cewa “Mulkin Allah ya yi kusa.” Shin, duka abubuwan nan sun faru a lokaci ɗaya kuwa? Ana ganin hakan ko’ina a duniya? Ga abin da tarihi ya nuna.
1. YAƘE-YAƘE
A 1914, an soma wani yaƙin da ya shafi mutane da yawa a ƙasashe da dama fiye da duk wani yaƙin da aka taɓa yi kafin shekarar. Masanan tarihi sukan ce shekara ta 1914 sabon shafi ne na tarihin ’yan Adam domin a shekarar ce aka fara yaƙin duniya. A yaƙin ne aka fara jefa bam daga sama, da amfani da tankunan yaƙi, da bindiga mai jigida, da iska mai guba, da dai sauran su wajen kakkashe mutane da yawa. Daga baya, an yi yaƙin duniya na 2, inda aka soma amfani da makaman nukiliya. Tun daga 1914, ’yan Adam ba su daina yaƙe-yaƙe ba, kuma yaƙe-yaƙen nan sun kakkashe miliyoyin mutane a wurare dabam-dabam.
2. GIRGIZAR ƘASA
Littafin da ake kira Britannica Academic da ke intane ya ce, a kowace shekara, ana yin girgizar ƙasa wajen 100 da suke “hallaka abubuwa.” Kuma rahoton United States Geological Survey ya nuna cewa, “bisa ga rahotannin da aka daɗe ana adanawa, (tun wajen shekara ta 1900), manyan girgizar ƙasa wajen 16 ne suke aukuwa a kowace shekara.” Ko da yake wasu suna ganin abin da ya sa ake cewa girgizar ƙasa tana ƙaruwa shi ne, akwai kayayyakin da suke sa a daɗa gano inda girgizar ƙasa take faruwa yanzu. Gaskiyar ita ce, manyan girgizar ƙasa suna wahalar da kuma kashe mutane a yau fiye da yadda yake a dā.
3. ƘARANCIN ABINCI
Wasu abubuwa da suke jawo ƙarancin abinci su ne, yaƙi, da cin hanci, da faɗuwar tattalin arziki, da rashin kula da harkokin noma ko rashin hangen gaba don kāre kayan gona daga yanayin da zai hallaka su. Rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya na “2018 Year in Review” ya ce: “Mutane miliyan 821 a duniya ba su da isashen abinci, kuma mutane miliyan 124 a cikinsu suna fama da yunwa mai tsanani.” Rashin cin abinci mai gina jiki yana cikin abubuwan da ke kashe yara wajen miliyan 3.1 kowace shekara. Kusan rabin yaran da suka mutu a 2011, rashin abinci mai gina jiki ne ya jawo hakan.
4. CUTUTTUKA DA ANNOBA
Wata jaridar Ƙungiyar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce: “Tun daga shekara ta 2001, an sami ɓarkewar munanan annoba da dama. Cututtukan da aka sani a dā, kamar kwalera da cutar shawara, sun sake ɓullowa, kuma sabbi kamar su cutar SARS, da wasu irin munanan mura, da cutar MERS da Ebola da Zika ma sun ɓullo.” Na kwanan nan shi ne annobar korona. Ko da yake ’yan kimiyya da likitoci sun gano abubuwa da dama game da cututtuka yanzu, har ila sun kasa magance cututtuka.
5. YIN WA’AZI A KO’INA A DUNIYA
Yesu ya ambata wani abu kuma da zai zama alamar zuwan Mulkin Allah sa’ad da ya ce: “Za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma, sa’an nan ƙarshen ya zo.” (Matiyu 24:14) Duk da matsalolin da ake fuskanta a duniya, mutane fiye da miliyan takwas suna wa’azin Mulkin Allah a ƙasashe 240, kuma suna hakan a yaruka fiye da 1,000. Hakan bai taɓa faruwa ba.
MECE CE MANUFAR ALAMAR NAN?
Babu shakka, dukan abubuwan da Yesu ya ce za su zama alamar zuwan Mulkin Allah suna faruwa a yau. Don me zai dace mu mai da hankali ga abubuwan nan? Yesu ya ce: “Idan kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.”—Luka 21:31.
Alamar da Yesu ya bayar da kuma lissafin shekaru da aka yi zancensu a Littafi Mai Tsarki, sun nuna cewa Allah ya kafa Mulkinsa a sama a shekara ta 1914. a A lokacin ne Allah ya naɗa Ɗansa, Yesu Kristi a matsayin Sarki. (Zabura 2:2, 4, 6-9) Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai soma sarauta a kan duniya, kuma zai hallaka duka gwamnatocin ’yan Adam, kuma ya mayar da duniya ta zama aljanna don mutane su zauna a ciki har abada.
Nan ba da daɗewa ba, addu’ar nan da Yesu ya koya wa mabiyansa cewa, “Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama,” za ta cika. (Matiyu 6:10) Amma mene ne wannan Mulkin ya yi tun da aka kafa shi a 1914? Kuma mene ne Mulkin zai yi idan ya fara sarauta a kan dukan ’yan Adam?
a Don samun ƙarin haske a kan shekara ta 1914, ka karanta darasi na 32 na littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa.