Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Wannan Duniyar Za Ta Kare?

Shin Wannan Duniyar Za Ta Kare?

Wataƙila, ka san cewa Littafi Mai Tsarki ya yi maganar ƙarshen duniya. (1 Yohanna 2:17) Hakan yana nufin cewa ’yan Adam ba za su kasance a duniya kuma ba? Duniya za ta zama kango ne inda babu wani abu mai rai, ko za a hallaka ta gabaki ɗaya?

AMSAR DA LITTAFI MAI TSARKI YA BAYAR GA TAMBAYOYIN NAN GUDA BIYU ITA CE, A’A!

Mene ne Ba Zai Ƙare Ba?

‘YAN ADAM

Littafi Mai Tsarki ya ce: Allah “bai halicci duniya ta zama wofi ba, ya yi ta domin a zauna a cikinta.” ​—ISHAYA 45:18.

DUNIYA

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wani tsara yakan wuce, wani tsara kuma ya zo, amma duniya tana nan daram har abada.”​—MAI-WA’AZI 1:4.

ABIN DA HAKAN YAKE NUFI: Littafi Mai Tsarki ya ce ba za a taɓa hallaka duniya ba, kuma mutane za su zauna a cikinta har abada. To, me ake nufi da ƙarshen duniya?

KA YI TUNANI A KAN WANNAN: Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙarshen duniyar nan da abin da ya faru a zamanin Nuhu. A lokacin, duniya “ta cika da tashin hankali.” (Farawa 6:13) Amma Nuhu mutum ne mai adalci. Don haka, Allah ya ceci shi da iyalinsa amma ya hallaka mugaye da ambaliya. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da abin da ya faru a lokacin, ya ce an ‘halaka duniya ta wancan zamani, lokacin da babban ruwa ya zo ya sha kanta.’ (2 Bitrus 3:6) Yadda duniya ta ƙare a lokacin ke nan. Amma me aka hallaka? Ba a hallaka duniya da kanta ba, amma mutanen da ke cikinta ne. Saboda haka, a duk lokacin da Littafi Mai Tsarki ya yi maganar ƙarshen duniya, ba hallakar doron ƙasa yake nufi ba. A maimakon haka, yana magana ne game da hallakar mugaye da tsarinsu.

Me Zai Ƙare?

MATSALOLI DA MUGUNTA

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba da daɗewa ba mugaye za su ɓace, ko ka duba inda suke a dā, ba za ka gan su ba. Amma masu sauƙin kai za su gāji ƙasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”​—ZABURA 37:10, 11.

ABIN DA HAKAN YAKE NUFI: Ambaliyar da aka yi a zamanin Nuhu bai kawar da mugunta gaba ɗaya ba. Bayan Ambaliyar, mugaye sun sake sa mutane cikin wahala. Amma nan ba da daɗewa ba, Allah zai kawar da mugunta. Kamar yadda wani marubucin zabura ya faɗa, “mugaye za su ɓace.” Jehobah zai kawo ƙarshen mugunta ta wurin Mulkinsa, wato, gwamnati da za ta yi mulki daga sama a kan ’yan Adam da suke yi wa Allah biyayya.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN: Shin, masu mulki a wannan duniyar za su amince da Mulkin Allah? Littafi Mai Tsarki ya ce ba za su yi hakan ba. Saboda wautarsu, za su yi adawa da Mulkin Allah. (Zabura 2:2) Mene ne hakan zai jawo? Mulkin Allah zai sauya dukan gwamnatocin ’yan Adam, kuma “mulkin nan zai kasance har abada.” (Daniyel 2:44) Me ya sa ake bukatar a kawo ƙarshen mulkin ’yan Adam?

ABIN DA MUKE BUKATA​—Ƙarshen Mulkin ’Yan Adam

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba mutum ne yake da iko ya kiyaye tafiyarsa ba.”​—IRMIYA 10:23.

ABIN DA HAKAN YAKE NUFI: Ba a halicci ’yan Adam don su yi mulkin kansu ba. Ba sa iya ja-gorantar ’yan’uwansu ko kuma magance matsalolinsu.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN: Wani littafin bincike ya ce gwamnatocin ’yan Adam ba za su iya “magance matsaloli kamar talauci da yunwa da cututtuka da bala’o’i da kuma yaƙe-yaƙe ko mugunta ba.” Littafin ya daɗa cewa: “Wasu . . . sun ce sai an sami gwamnati ɗaya da ke mulki a kan duniya ne za a iya magance matsalolin nan.” Amma, ko da gwamnatocin ’yan Adam sun haɗa kai, ba za su iya magance matsalolin da aka ambata a baya ba, domin dukansu ajizai ne. Mulkin Allah ne kaɗai gwamnatin da za ta iya magance matsaloli gabaki ɗaya.

Saboda haka, bisa ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, ƙarshen duniya, wato ƙarshen wannan zamanin, ba abin da mutane masu aminci za su ji tsoronsa ba ne. A maimakon haka, abu ne da ya kamata mu yi marmarin sa, domin Allah zai sauya wannan muguwar duniyar da sabuwar duniya mai kyau!

Yaushe ne abubuwan nan za su faru? Talifi na gaba zai nuna amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar.