Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Koya Mutunta Kaina da Kuma Mata

Na Koya Mutunta Kaina da Kuma Mata
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1960

  • ƘASAR HAIHUWA: FARANSA

  • TARIHI: MAI YAWAN FAƊA DA SHAN ƘWAYOYI DA KUMA RAINA MATA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a wata unguwar da ke cike da ‘yan iska a arewa maso gabashin Faransa. Abin da na sani tun ina yaro shi ne faɗace-faɗacen da iyalai suke yi a unguwarmu. Ba a mutunta mata a iyalinmu balle ma a ji shawararsu. An ce aikin mata shi ne dafa abinci da kuma kula da maza da yara.

Yanayin da na yi girma a ciki ba sauƙi ko kaɗan. Mahaifina ya rasu sa’ad nake ɗan shekara goma don tsabar shan giya da yake yi. Bayan shekara biyar, yayana ya kashe kansa. A cikin shekarar kuma, na ga yadda aka kashe wani a iyalinmu sakamakon faɗa kuma hakan ya tsorata ni sosai. Dangina sun koya mini yin faɗa da wuƙaƙe da kuma bindigogi. A sakamakon haka, sai na cika jikina da zane-zane kuma na soma shan giya.

Ina shan kwalaben giya 10 zuwa 15 a rana a lokacin da nake shekara 16, kuma ba da daɗewa ba, sai na soma shan ƙwayoyi. Don in sami kuɗin kashewa, na fara sayar da ƙarafa, daga baya na soma sata. An sako ni daga fursuna sa’ad da nake ɗan shekara 17. Na shiga kurkuku sau 18 sanadiyyar sata da kuma faɗa.

Yanayina ya daɗa muni sa’ad da na kai shekara 20 da wani abu. Ina shan wajen karan wi-wi 20 a rana kuma ina shan wasu miyagun ƙwayoyi. Sau da dama na kusan mutuwa don yawan ƙwayoyin da nake sha. A kullum ina tare da wuƙaƙe da kuma bindigogi don sana’ar sayar da miyagun ƙwayoyi da nake yi. Akwai lokacin da na harbi wani amma harsashin bai same shi ba. Mahaifiyata ta rasu sa’ad da nake shekara 24 kuma hakan ya sa na daɗa zama mai zafin hali. Idan mutane suka gan ni ina wucewa, sai ka ga kowa yana canja hanya don tsoro. A yawancin lokuta, a ofishin ‘yan sanda nake kwana ko kuma asibiti don raunukan da na ji.

Na yi aure sa’ad da nake shekara 28. Kuma ban ɗauki matata da muhimmanci ba don ina zaginta da kuma dūkan ta a koyaushe. Ba ma taɓa yin abu tare. Na ɗauka cewa za ta yi farin ciki idan ina ba ta gwalagwalan da na sato. Sai farat ɗaya, matata ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Bayan da aka yi nazari da ita sau ɗaya, sai ta daina shan taɓa da kuma karɓan kuɗin da nake satowa, har ma ta mayar mini da gwalagwalan da na ba ta. Ban ji daɗin hakan ba sam kuma na soma ƙoƙarin hana ta nazarin, a wani lokaci ma ina busa mata hayaƙin sigari a fuska. Ina mata ba’a da kuma dariya a gaban maƙwabtanmu.

Akwai wata rana da na cinna wa gidanmu wuta daddare domin na bugu da giya. Matata ce ta ceto ni da ‘yarmu mai shekara biyar daga wutan. Sa’ad da na farfaɗo, na ji kunya sosai kuma na ɗauka cewa Allah ba zai taɓa gafarta mini ba. Na tuna yadda wani limamin coci ya koya mana cewa za a jefa masu mugunta cikin wuta. Kuma likitan taɓaɓɓu da yake mini jinya ya ce min: “Kai kam, ba ka da wata mafita don ka fi ƙarfinmu.”

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Bayan gobarar, sai muka ƙaura zuwa gidan iyayen matata. Yayin da Shaidun Jehobah suka zo nazari da matata, sai na tambaye su, “Allah zai iya gafarta mini dukan zunubaina kuwa?” Sai suka karanta mini 1 Korintiyawa 6:​9-11 daga cikin Littafi Mai Tsarki. Ayoyin sun nuna halayen da Allah ya tsana. Amma aya ta sha ɗaya ta ce: “Waɗansu ma a cikinku dā haka ku ke.” Nassin nan ya tabbatar mini da cewa zan iya canja halayena. Shaidun sun sake nuna mini 1 Yohanna 4:8 da ta daɗa tabbatar da ni cewa Allah yana ƙauna ta. Hakan ya ƙarfafa ni sosai, sai na amince Shaidun Jehobah su riƙa nazari da ni sau biyu a mako, kuma nan da nan na soma halartar taronsu. Na yi addu’a ga Jehobah a kai a kai.

A cikin wata ɗaya, sai na yanke shawarar daina shan ƙwayoyi da kuma giya. Hakan ba sauƙi sam domin na fuskanci ƙalubale da yawa kamar su, mafarkai masu ban tsoro da ciwon kai da ciwon gaɓaɓuwa da na ciki da dai sauransu. Amma duk da haka, Jehobah ya ƙarfafa ni kuma na shaida yanayin manzo Bulus sa’ad da ya ce: “Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafata.” (Filibiyawa 4:​13, Littafi Mai Tsarki) Daga baya, na daina shan taɓa.—2 Korintiyawa 7:1.

Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini na gyara rayuwata da kuma na iyalina. Na soma daraja matata sosai kuma ina ce mata “don Allah” da kuma “na gode.” Na kuma zama mahaifin kirki ga ‘yata. Bayan da na yi shekara ɗaya ina nazari da Shaidun Jehobah, sai na yi baftisma kamar matata.

YADDA NA AMFANA:

Babu shakka, bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka mini in ci gaba da rayuwa har yau. Dangina waɗanda ba Shaidun Jehobah ba ma sun san cewa da ba don taimakon Littafi Mai Tsarki ba, da na riga na mutu sanadiyyar shan giya da kuma faɗa.

Mun kyautata rayuwar iyalinmu don yanzu ina bin ƙa’idodin da Allah ya ba uba da kuma miji. (Afisawa 5:25; 6:⁠4) Muna yin kome tare a matsayin iyali. Ni da matata da ke wa’azi na awoyi saba’in kowane wata muna jin daɗin zuwa wa’azi tare. Ƙari ga haka, ba na ɗauka cewa aikinta dafa abinci ne kawai kamar dā. Ita ma tana jin daɗin taimaka mini don in iya yin aikina na dattijo a ikilisiya.

Ƙauna da kuma jinƙai da Jehobah ya nuna mini ya canja rayuwata sosai. Ina jin daɗin yin wa’azi ga mutanen da ake gani ba su da mafita a rayuwarsu, domin ni ma haka aka ɗauke ni a dā. Yanzu na tabbata cewa Littafi Mai Tsarki zai iya gyara rayuwar kowane irin mutum. Littafi Mai Tsarki ya koya mini yadda zan nuna ƙauna da kuma mutunta mutane maza da mata har ma da kaina.