Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“A Ina Allah Yake”

“A Ina Allah Yake”

“A KULLUM NAKAN CE: DON ME ALLAH BAI HANA BALA’IN BA?”​—In ji Paparoma Benedict na 16, a lokacin da ya ziyarci sansanin Auschwitz, a Polan.

IDAN BALA’I YA AFKU, KAKAN CE, ‘DON ME ALLAH BAI KAWAR DA BALA’IN BA?’ KO KUWA A LOKACIN DA KAKE SHAN WAHALA, SHIN KANA GANIN ALLAH BAI DAMU DA KAI BA?

Haka wata mai suna Sheila, da ke zama a Amirka ta ji. Iyayenta masu son yin ibada ne sosai. Ga abin da ta ce: “Tun ina ƙarama ina ƙaunar Allah don shi ne Mahaliccinmu. Amma ban taɓa kusantarsa ba. Na ɗauka cewa yana ganina amma ba ya son in kusace shi. Na san Allah bai tsane ni ba amma ban gaskata cewa yana ƙaunata ba.” Me ya sa Sheila take shakka? Ta ce: “Iyalinmu ta fuskanci bala’i ɗaya bayan ɗaya. Don haka, na ɗauka cewa Allah bai damu da mu ba ko kaɗan.”

Kamar Sheila, kai ma za ka iya gaskata cewa Allah yana wanzuwa, amma wataƙila ba ka ganin ya damu da kai da gaske. Ayuba mai adalci ya gaskata cewa Allah Mahalicci yana da iko da hikima, amma ya yi shakkar ko Allah ya damu da shi. (Ayuba 2:3; 9:4) A lokacin da bala’i ya auko wa Ayuba ɗaya bayan ɗaya kuma ba shi da bege, ya tambayi Allah ya ce: “Don me kake ɓoye mini fuskarka, me ya sa ka ɗauke ni kamar abokin gābanka?”​—Ayuba 13:24.

Me Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan? Allah ne yake jawo mana bala’in da muke fama da shi? Shin akwai wani abin da ya nuna cewa Allah ya damu da kai da kuma dukan ’yan Adam? Shin kowannenmu ya tabbata cewa Allah ya san da zamansa, ya fahimci yanayinsa, yana tausaya masa da kuma taimaka masa a lokacin da yake shan wahala?

A talifi na gaba, za mu bincika darussan da za mu iya koya daga halittu da suka nuna cewa Allah ya damu da mu. (Romawa 1:20) Bayan haka, za mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yadda Allah yake kula da mu. Idan ka yi ƙoƙari don ka “san shi” ta wurin bincika halittu da kuma Kalmarsa, za ka kasance da tabbaci cewa yana “lura” da kai.​—1 Yohanna 2:3; 1 Bitrus 5:7.