Allah Ya Kusan Kawar da Wahala
“Har yaushe, ya Yahweh, zan yi ta kukan neman taimako, kai kuwa ka ƙi ji? Ina ta kuka gare ka saboda tashin hankali, kai kuwa ka ƙi yin ceto.” (Habakkuk 1:2, 3) Abin da Habakkuk mutum mai aminci wanda kuma ya shaida alherin Allah ya faɗa ke nan. Shin abin da ya faɗa ya nuna cewa ba shi da bangaskiya ne? A’a! Allah ya tabbatar wa Habakkuk cewa ya shirya lokacin da zai kawo ƙarshen wahala.—Habakkuk 2:2, 3.
Idan kai ko ɗan’uwanka na cikin wahala, za ka iya yin tunanin cewa Allah ba ya ɗaukan mataki da sauri, domin ya kamata a ce ya taimaka muku a yanzu. Amma ga abin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Waɗansu suna cewa Ubangiji yana jan jiki game da cika alkawarinsa. Ai, ba haka ba ne. Haƙuri yake yi da ku. Ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.”—2 Bitrus 3:9.
YAUSHE ALLAH ZAI ƊAU MATAKI?
Nan ba da jimawa ba! Yesu ya ce wata tsara za ta ga wasu abubuwa da za su faru a lokaci ɗaya kuma abubuwan ne za su nuna cewa muna “ƙarshen zamani.” (Matiyu 24:3-42) Tun da yake annabcin da Yesu ya yi suna cika a zamaninmu, hakan ya nuna cewa Allah ya kusa ya ɗau mataki. a
Amma ta yaya Allah zai cire dukan wahaloli? A lokacin da Yesu yake duniya, ya yi abubuwa da suka nuna cewa Allah yana da ikon cire wahalolin ’yan Adam. Ga wasu misalai.
Bala’i: Akwai lokacin da Yesu da manzanninsa suke cikin jirgin ruwa a tekun Galili, sai iska ta so ta nitsar da su cikin tekun. Amma Yesu ya nuna cewa shi da Jehobah suna da iko a kan iska da duk wani abin da zai iya janyo bala’i. (Kolosiyawa 1:15, 16) Yesu ya ce: “Natsu! Ka yi shiru!” Sai me ya faru? “Sai iskar ta daina, wuri duk ya yi tsit.”—Markus 4:35-39.
Rashin Lafiya: Mutane sun shaida yadda Yesu ya warkar da makafi da guragu da kutare da masu farfaɗiya da kuma kowane irin ciwo. ‘Ya kuma warkar da duk marasa lafiya.’—Matiyu 4:23, 24; 8:16; 11:2-5.
Ƙarancin Abinci: Yesu ya yi amfani da ikon da Jehobah ya ba shi don ya tanadar wa mutane abinci. Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da yake duniya, ya ciyar da dubban mutane har sau biyu.—Matiyu 14:14-21; 15:32-38.
Mutuwa: Yadda Yesu ya tayar da mutane uku daga mutuwa ya sa mun yi imani cewa Allah yana da ikon ta da matattu. Ɗaya daga cikin mutanen da Yesu ya ta da su ya yi kwana huɗu da mutuwa.—Markus 5:35-42; Luka 7:11-16; Yohanna 11:3-44.
a Don ƙarin bayani game da kwanakin ƙarshe, ka karanta darasi na 32 a littafin nan Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi kuma za ka iya sauƙar da shi kyauta a dandalin www.pr418.com/ha.