Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?

Babu wanda ba a taɓa masa rasuwa ba. Amma idan mutum ya mutu shi ke nan? An manta da shi ke nan har abada? Zai sake rayuwa kuwa?

GA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

BA A MANTA DA WAƊANDA SUKA MUTU BA

“Duk waɗanda suke cikin kaburbura za . . . su fito.”​—Yohanna 5:​28, 29.

Allah bai manta da waɗanda suka mutu ba; zai ta da waɗanda yake tune da su.

ZA A TA DA WAƊANDA SUKA MUTU

“Za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.”​—Ayyukan Manzanni 24:15.

Za a ta da biliyoyin mutane kuma za su yi rayuwa har abada a cikin kwanciyar hankali.

HAKIKA, ZA A TA DA WAƊANDA SUKA MUTU

‘Allah yakan lissafta yawan taurari, yakan kira kowanne da sunansa.’​—Zabura 147:4.

Da yake Allah yana iya kiran kowane tauraro da sunansa, tuna waɗanda zai ta da su ƙaramin alhaki ne.