Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Rayuwa a Yau

Rayuwa a Yau

A CE kana kallon fim game da wata mawaƙiya da ta yi suna sosai. Da farko an nuna lokacin da take ƙarama, da lokacin da ta soma koyon yin kiɗa, da kuma yadda take ƙoƙari don ta ƙware. Sai aka nuna ta tana zuwa ƙasashe dabam-dabam tana waƙa a gaban jama’a. Amma kafin ka ankara, sai ta tsufa kuma a ƙarshe ta mutu.

Wannan fim ba tatsuniya ba ce, abu ne da ya faru da wata. Kuma abin da yake faruwa da mutane ke nan, ko da mawaƙa ne ko ’yan kimiyya ne ko dai sauran shahararrun mutane. Da ba don tsufa ko mutuwa ba, da mutane sun cim ma abubuwa fiye da waɗanda suke cim ma a rayuwarsu, ko ba haka ba?

Abin takaici ne idan muka yi tunanin yanayin ’yan Adam, amma a gaskiya abin da yake faruwa da kowa ke nan. (Mai-Wa’azi 9:5) Duk da ƙoƙarin da ’yan Adam suke yi, a kwana a tashi, za su tsufa kuma su mutu. Ban da haka ma, hatsari ko rashin lafiya mai tsanani zai iya zama sanadiyyar mutuwar mutum. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta rayuwarmu da hazon da ke ‘bayyana na ɗan lokaci sa’an nan ya ɓace.’​—Yaƙub 4:14.

Domin rayuwa ba ta da tabbas, mutane da yawa suna da ra’ayin nan cewa ‘mu yi ta ci da sha, tun da gobe za mu mutu.’ (1 Korintiyawa 15:32) Amma abin da ya sa mutane suke da irin wannan ra’ayin shi ne, suna ganin bayan sun mutu, tasu ta ƙare ke nan. A kwana a tashi, musamman idan mutum ya sami kansa a tsaka mai wuya, zai iya tambayar kansa, ‘Ana haifan mu don mu yi girma mu mutu ne kawai?’ Ta yaya za mu san amsar tambayar nan?

Mutane da yawa suna dogara ga ’yan kimiyya. Kuma ’yan kimiyya da likitoci sun gano wasu abubuwan da suke ƙara tsawon rayuwar ɗan Adam. Amma har wa yau, suna kan bincike don su ga ko za su iya daɗa tsawon rayuwa. Kuma ko da sun yi nasara ko a’a, mutane za su ci gaba da yin tambayoyin nan: Me ya sa muke tsufa da kuma mutuwa? Za a daina mutuwa wata rana kuwa? A talifofi na gaba, za a tattauna batutuwan nan, kuma za a ba da amsar tambayar nan: Mutuwa ce ƙarshen ’yan Adam?