Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zai Yiwu Ka Kyautata Rayuwarka Yanzu

Zai Yiwu Ka Kyautata Rayuwarka Yanzu

A NAN gaba, babu wanda zai yi ciwo, ko ya tsufa, balle ma ya mutu. Kuma kai ma za ka iya more irin rayuwar nan! Amma rayuwa a yau tana cike da matsaloli. Akwai abin da za ka iya yi don ka ji daɗin rayuwa a yau kuwa? Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda ’yan Adam za su iya inganta rayuwarsu a yanzu. Bari mu ga yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu magance wasu matsalolin rayuwa.

YADDA ZA KA GAMSU DA ABIN DA KAKE DA SHI

Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: “Ku yi nesa da halin son kuɗi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi.” ​Ibraniyawa 13:5.

A yau, akwai abubuwa da yawa da mutane suke cewa ya kamata mu saya. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce za mu iya gamsuwa ‘da abin da muke da shi.’ Ta yaya za mu yi hakan?

Ka guji son kuɗi. Mutane da yawa a yau sukan sadaukar da lafiyarsu, ko iyalansu, ko abokantakarsu, har ma su zub da mutuncinsu tsabar son kuɗi. (1 Timoti 6:10) Hakika, wannan ba ƙaramar hasara ba ce! A ƙarshe kuwa, mai son arziki ba zai taɓa “ƙoshi da abin da yake samuwa” ba.​—Mai-Wa’azi 5:10.

Ka daraja mutane maimakon kayan duniya. Babu shakka, wasu kayan duniya suna da amfani. Amma waɗannan abubuwa ba za su iya ƙaunar mu ko su gode mana ba. Mutane ne kaɗai za su iya yin haka. “Abokin kirki” zai iya taimaka maka ka gamsu da abin da kake da shi.​—Karin Magana 17:​17, New World Translation.

ZA MU KYAUTATA RAYUWARMU YANZU IDAN MUNA YIN ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊA

JIMREWA DA RASHIN LAFIYA

Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: “Zuciya mai murna magani ne mai kyau.”​Karin Magana 17:22.

Yin murna zai taimaka mana sa’ad da muke rashin lafiya kamar yadda “magani . . . mai kyau” yake taimakon marar lafiya. Amma me zai taimaka mana mu yi murna sa’ad da muke fama da rashin lafiya?

Ka riƙa nuna godiya. Idan muka yi ta tunanin matsalolinmu kawai, ba za mu ji daɗin “dukan kwanakin[mu]” ba. (Karin Magana 15:15) A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce, mu “kasance masu godiya.” (Kolosiyawa 3:15) Ka riƙa gode wa Allah don abubuwa masu kyau da kake morewa, kome ƙanƙantansu. Za ka ji daɗin rayuwa idan kana godiya don abubuwan da ke kewaye da mu kamar, yadda sararin sama take kyau sa’ad da rana take faɗuwa, ko ana iska mai daɗi, ko kuma ka ga wani da kake ƙauna yana murmushi.

Ka taimaka wa mutane. Ko da mutum yana rashin lafiya ne, “ya fi albarka a bayar da a karɓa.” (Ayyukan Manzanni 20:35) Mukan yi farin ciki sosai idan mutane suka gode mana don wani abin da muka yi musu, kuma hakan zai sa mu rage tunani a kan matsalolinmu. Idan muka taimaka wa mutane, za mu inganta rayuwarmu.

KU KYAUTATA ZAMAN AURENKU

Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa: Ka riƙa “zaɓar abin da ya fi kyau.”​Filibiyawa 1:10.

Idan ma’aurata ba sa yawan kasancewa tare, za su iya ɓata dangantakarsu. Shi ya sa ya kamata ma’aurata su ɗauki aurensu da muhimmanci sosai.

Ku riƙa yin abubuwa tare. Ku shirya yadda za ku riƙa yin abubuwa tare. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma mutum biyu da mutum ɗaya.” (Mai-Wa’azi 4:9) Ku yi aikin gida tare, ku yi wasa tare, ku ci abinci tare ko ku koyi wani sabon abu tare.

Ku nuna wa juna soyayya. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa ma’aurata su so juna kuma su riƙa daraja juna. (Afisawa 5:​28, 33) Yin murmushi, da rungumar juna, ko ba wa juna kyauta, ko da ƙaramin abu ne, zai iya kyautata zaman aure. Amma, idan ya zo ga batun nuna wa juna soyayya, ya kamata ma’aurata su yi hakan tsakanin su biyu kawai.​—Ibraniyawa 13:4.