Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mahaliccinmu Mai Ƙauna Ya Damu da Mu

Mahaliccinmu Mai Ƙauna Ya Damu da Mu

1. MAHALICCINMU NE YAKE SA RANA TA YI HASKE

Da a ce babu hasken rana, ya kake ganin rayuwa za ta kasance? Hasken rana ne yake taimaka wa itatuwa su fitar da ganyaye da furanni kuma su ba da ’ya’ya. Ƙari ga haka, rana tana taimaka wa itatuwa su ja ruwa daga ƙasa zuwa ganyayensu ta jijiyoyinsu, a ƙarshe, sai ruwan ta fita ta bi iska.

2. MAHALICCINMU NE YAKE SA A YI RUWAN SAMA

Allah ne yake ba da ruwan sama, kuma ruwa ne yake sa mu sami abinci. Allah yana ba mu ruwan sama da damina mai albarka, yana ƙosar da mu da abinci, kuma yana sa mu yi farin ciki.

3. MAHALICCINMU NE YAKE BA MU ABINCI DA RIGUNA

Magidanta da yawa sukan damu a kan yadda za su samar wa iyalansu abinci da sutura. Nassosi Masu Tsarki * sun ce: “Ku dubi tsuntsaye mana, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa tara a rumbuna. Duk da haka Ubanku na sama ne yake ciyar da su. Ba ku fi su daraja ba?”​—Matiyu 6:​25, 26.

“Ku dubi fulawar daji yadda suke girma . . . , ina gaya muku, ko Sarki [Sulemanu] da dukan darajarsa, bai taɓa ado kamar ɗaya daga cikinsu ba. To, idan har Allah zai yi wa ciyawar daji ado haka . . . , balle ku?”​—Matiyu 6:​28-30.

Tun da Allah zai iya ba mu abinci da sutura, ba shakka, zai iya taimaka mana mu sami abin biyan bukata. Idan muna yin abin da Allah yake so, zai iya taimaka mana mu sami abinci ko ya taimaka mana mu sami aikin da zai ba mu abin biyan bukata.​—Matiyu 6:​32, 33.

Hakika idan muka yi tunani a kan rana da ruwan sama da tsuntsaye da kuma furanni, za mu ga ƙwaƙƙwarar dalilin da zai sa mu ƙaunaci Allah. A talifi na gaba, za mu ga abin da Mahaliccinmu ya yi don ya isar da saƙonsa ga ’yan Adam.

^ sakin layi na 7 A duk inda aka ambata Nassosi Masu Tsarki, ana nufin Attaura da Zabura da Linjila.