Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Idan muna bin dokokin Allah, za mu yi farin ciki

Masu Yi wa Allah Biyayya Za Su Sami Albarka

Masu Yi wa Allah Biyayya Za Su Sami Albarka

Annabi Musa ya ce idan mun bi dokokin Allah, Allah zai yi mana albarka. (Maimaitawar Shari’a 10:13; 11:27) Allah yana da halaye masu kyau, shi ya sa ya kamata mu ƙaunace shi kuma mu guji yin abin da zai ɓata masa rai. Zai dace mu yi wa Allah biyayya don muna ƙaunarsa, ba don muna tsoro cewa zai hukunta mu idan muka ƙi yi masa biyayya ba. Kalmarsa ta ce: “Ƙaunarmu ga Allah ita ce, mu kiyaye umarnansa.”​—1 Yohanna 5:3.

Amma ta yaya yi wa Allah biyayya yake kawo albarka? Ga hanyoyi biyu da za mu amfana.

1. YIN BIYAYYA ZAI SA MU ZAMA MASU HIKIMA

“Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya koya muku domin amfanin kanku, wanda ya nuna muku hanyar da za ku bi.”​—ISHAYA 48:17.

Mahaliccinmu Jehobah ya san mu, kuma yana gaya mana abin da ya kamata mu yi. Idan muna so mu yanke shawarwari masu kyau, wajibi ne mu riƙa bincika Nassosi Masu Tsarki don mu san abin da Allah yake so mu yi kuma mu yi shi.

2. YIN BIYAYYA ZAI SA MU YI FARIN CIKI

“Waɗanda suke jin kalmar Allah, kuma suna kiyaye ta ne suke farin ciki!”​—LUKA 11:​28, New World Translation.

Miliyoyin mutane a yau suna farin ciki domin suna bin abin da ke Kalmar Allah. Alal misali, akwai wani mutum ɗan ƙasar Sifen. Shi mai saurin fushi ne kuma ba ya mutunta kowa har da matarsa. Wata rana, ya karanta labarin Yusuf ɗan Yakub wanda annabi Musa ya rubuta. Mutumin ya ga halin kirkin da Yusuf ya nuna. Duk da cewa an sayar da shi a matsayin bawa kuma an jefa shi a kurkuku ba tare da ya yi wani laifi ba, Yusuf ya kasance mai haƙuri, mai son zaman lafiya, da kuma gafartawa. (Farawa, surori 37-45) Mutumin ya ce: “Da na yi tunani a kan abin da Yusuf ya yi, hakan ya sa na zama mai haƙuri, mai alheri da kuma kamun kai. A sakamakon haka, ina jin daɗin rayuwa yanzu, kuma ina farin ciki.”

Nassosi Masu Tsarki sun yi bayani sosai a kan yadda ya kamata mu mutunta mutane. A talifi na gaba, za a tattauna wannan batun.