Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hoton wani sashen littafin Ishaya da aka samo daga Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri a saman fassarar littafin Ishaya a Larabci na zamani. Wannan ya nuna cewa ba a canja Nassosi Masu Tsarki ba

Shin An Canja Sakon da Ke Rubutacciyar Kalmar Allah?

Shin An Canja Sakon da Ke Rubutacciyar Kalmar Allah?

Wasu mutane suna ganin kamar an canja abin da ke rubutacciyar Kalmar Allah. Amma annabi Ishaya ya ce Kalmar Allah “tana nan har abada!” (Ishaya 40:8) Me ya tabbatar mana cewa ba a canja saƙon da ke Kalmar Allah ba?

Allah yana da ikon kāre Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki don kada a halaka shi ko a canja abin da ke ciki. A zamanin dā, da hannu ake kofar Nassosi Masu Tsarki. Wasu masu kofar sukan ƙirga kalmomi da kuma haruffan da ke Nassosin don su tabbata cewa ba su ƙara, ko canja, ko cire wani abu daga ciki ba. Duk da haka, da yake ’yan Adam ajizai ne, wasun su sun yi ’yan kurakure, amma kurakuren ba su canja ainihin sakon da ke nassosin ba.

YA ZA MU TABBATAR CEWA AINIHIN SAƘON ALLAH NE YAKE NASSOSI NA YAU?

Akwai dubban rubuce-rubucen Nassosi Masu Tsarki da aka kofa tun dā. Saboda haka, idan an ɗan yi kuskure wajen kofa wani sashe na Nassosi Masu Tsarki, za a iya ganewa ta wajen duba sauran don a tabbatar da gaskiyar lamarin.​—Don ƙarin bayani, ka karanta talifin nan, “An Canja Ko Kuma Sake Saƙon Littafi Mai Tsarki Ne?” a dandalin jw.org/ha.

Ga wani misali, a shekara ta 1947, wasu Larabawa maƙiyaya sun samo Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri a wani ƙogo kusa da Tekun Gishiri. Littattafan da suka samo na ɗauke da wasu sassan Nassosi Masu Tsarki da aka rubuta fiye da shekaru dubu biyu da suka shige. Masana sun gwada abin da ke cikin littattafan nan da Nassosi Masu Tsarki da muke da su a yau. Me suka gano?

Masanan sun gano cewa abin da ke Nassosi Masu Tsarki da muke da su a yau ya jitu da abin da ke ainihin Nassosi Masu Tsarki na dā. * Bayan da aka bincika rubuce-rubucen Nassosi Masu Tsarki na dā da kyau, an gano cewa saƙon da ke cikinsu ɗaya ne da namu a yau. Babu shakka, Allah ya kāre Kalmarsa don amfaninmu.

Don haka, za mu iya karanta Kalmar Allah da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinta ba. Yanzu bari mu ga abin da annabawan Allah suka bayyana mana game da shi.

^ sakin layi na 7 Daga littafin nan, The Complete Dead Sea Scrolls in English, shafi na 16, Geza Vermes ne ya wallafa.