Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zai dace ka taimaka wa mutane, ko da inda kuka fito, da addininku da shekarunku ba ɗaya ba ne

Yin Alheri Zai Sa Mu Sami Albarka

Yin Alheri Zai Sa Mu Sami Albarka

A yau mutane da yawa suna bukatar abinci da wurin kwana. Wasu kuma suna bukatar a ƙarfafa su ne kawai. Idan mun yi ƙoƙarin taimaka wa mutane, Allah zai albarkace mu.

GA ABIN DA NASSOSI MASU TSARKI SUKA CE

“Mai yi wa . . . talaka kirki, kamar ya ba Yahweh rance ne, Yahweh kuwa zai saka masa.”​—KARIN MAGANA 19:17.

TA YAYA ZA MU TAIMAKA WA MUTANE?

Yesu Almasihu ya taɓa ba da labarin wani Bayahude da ɓarayi suka yi masa dūka, kuma suka bar shi a bakin rai da mutuwa. (Luka 10:​29-37) Da wani mutumin kirki ya zo ya gan shi, sai ya taimaka masa. Mutumin ya taimaka masa duk da cewa shi ba Bayahude ba ne.

Mutumin ya yi wa wanda ɓarayi suka yi masa dūka tanadin magani da kuɗin jinya. Ƙari ga haka, ya ƙarfafa shi kuma ya taimaka masa ya fita daga yanayin da yake ciki.

Mene ne labarin nan ya koya mana? Almasihu ya nuna cewa ya kamata mu riƙa taimaka wa mutane a duk hanyar da za mu iya yin hakan. (Karin Magana 14:31) Nassosi Masu Tsarki sun ce, nan ba da daɗewa ba Allah zai kawo ƙarshen wahala da talauci. Ƙila ka ce, ‘Ta yaya Allah zai yi hakan, kuma yaushe?’ A talifi na gaba, za ka ga albarkun da za ka iya samuwa daga wurin Mahaliccinka.