KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | SARATU
Allah Ya Kira Ta Sarauniya
SARATU ta tashi bayan ta daɗe tana yin aiki, sai ta kalli nesa. Bayin da ke mata aiki suna farin ciki domin tana mutunta su. Saratu ma mace mai ƙwazo ce sosai. Ka yi tunanin yadda take matsa hannayenta don ta fitar da gajiya. Wataƙila ta shagala da ɗinka wuraren da suka yage a tantin da suke zama a ciki. An yi tantin da fatar awaki kuma ya soma yagewa domin sun yi shekaru da yawa suna amfani da shi. Babu shakka, ganin tantin na tuna wa Saratu cewa sun daɗe suna kai-da-kawowa. Ta ga sa’ad da Ibrahim * ya bar gida da safe, amma yanzu gari ya soma duhu. Sai ta soma kallon hanyar da ya bi da safe sa’ad da ya fita. Da ta hango shi yana tahowa daga nesa, sai ta soma murmushi mai ban sha’awa.
An yi shekara goma tun da Ibrahim da iyalinsa da kuma bayinsa suka haye Kogin Yufiretis zuwa Kan’ana. Saratu ta goyi bayan maigidanta a wannan tafiyar da suka yi. Me ya sa? Domin ta san cewa ta zuriyarsa ce dukan mutane za su sami albarka. Amma Saratu kuma fa, ta yaya za ta taimaka wajen ciki nufin Allah? Ba ta taɓa haihuwa ba kuma yanzu ta kai shekara 75. Babu mamaki, ta yi tunani cewa, ‘Ta yaya nufin Jehobah zai cika idan Ibrahim bai sake aure ba?’ Ba abin mamaki ba ne idan ta ji hakan, ko kuma in hankalinta ya tashi.
A wasu lokuta, za mu iya ƙosa ganin alkawuran Allah sun cika. Yana iya yi mana wuya mu jimre musamman ma idan muna jiran wani abu da muke so sosai. Wane darasi ne za mu iya koya daga bangaskiyar wannan matar?
JEHOBAH YA HANA NI HAIHUWA
Ba a daɗe ba da Ibrahim da iyalinsa suka bar ƙasar Masar. (Farawa 13:1-4) Sun kafa sansani a tudun da ke gabashin birnin Bethel, wanda Kan’aniyawa suke kira Luz. Saratu tana ganin wasu yankunan Ƙasar Alkawari daga wannan wurin. Tana ganin ƙauyukan Kan’aniyawa da kuma hanyoyin da ake bi zuwa wasu ƙasashe. Amma Saratu ta fi sha’awar birnin Ur inda ta girma. Birnin Ur na yankin Mesopotamiya wanda ke da nisan mil 1,200, wato kilomita 1,900 daga birnin Bethel. A birnin ne ’yan’uwanta da yawa ke zama kuma akwai kasuwanni da shaguna da ake cinikayya. Gidan da take zama a dā na da rufi mai kyau da katanga ƙila har da ruwan fanfo. Amma wannan matar ba ta zauna tana da-na-sani don ta bar gida ba.
Ku yi la’akari da abin da aka hure manzo Bulus ya rubuta shekaru 2,000 bayan wannan lokacin. Manzon ya yi wannan furucin game da bangaskiyar Ibrahim da Saratu. Ya ce: “Da suna marmarin ƙasan nan da suka baro ne, da sun sami damar komawa.” (Ibraniyawa 11:8, 11, 15, Littafi Mai Tsarki) Ibrahim da Saratu ba su yi kewar abin da suka baro ba. Da a ce sun yi hakan, da wataƙila sun koma gida. Da sun koma birnin Ur, ba za su more albarkun da Jehobah ya shirya musu ba. Ƙari ga haka, da an manta da su domin ba za a rubuta sunayensu cikin mutane masu bangaskiya ba.
A maimakon yin da-na-sani, Saratu ta mai da hankali a kan maƙasudinta. Ta ci gaba da goyon bayan maigidanta a tafiyar da suke yi. Tana taimaka masa su kwashe tantin da kafa su da kuma kwashe dabbobi. Ta kuma jimre wasu ƙalubale da kuma canje-canje a rayuwarta. Jehobah ya sake tabbatar wa Ibrahim da cewa zai cika alkawarin da ya yi masa, amma bai faɗi kome game da Saratu ba.—Farawa 13:14-17; 15:5-7.
A ƙarshe, Saratu ta ga cewa ya dace ta gaya wa maigidanta abin da ke ranta. Ka yi tunanin yadda fuskarta ta kasance sa’ad da take gaya masa cewa: “Ga shi yanzu, Ubangiji ya riƙe mani haihuwa.” Sai ta ce wa maigidanta ya auri baiwarta Hajaratu don ta haifa masa yara. Ka yi tunanin irin ƙuncin da Saratu take ciki yayin da take yin wannan maganar. Wataƙila abin da Saratu ta yi zai sa mu mamaki, amma a zamanin dā hakan ruwan dare gama gari ne. * Mai yiwuwa Saratu ta yi tunani cewa yin hakan zai taimaka wajen cika alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim. Ko da yaya abin ya faru, Saratu tana a shirye ta yi wannan sadaukarwa mai wuya. Mene ne Ibrahim ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim “ya ji maganar” Saratu.—Farawa 16:1-3.
Shin labarin ya nuna cewa Jehobah ne ya sa Saratu ta yi wannan maganar? A’a. Abin da ta roƙa ya nuna yadda ’yan Adam suke tunani. Ta yi tsammani cewa Allah ne ya ɗora mata wannan masifar, kuma ba ta yi tunanin cewa zai magance matsalar ba. Abin da take so ta yi zai jawo mata baƙin ciki. A wannan duniyar, mutane sun fi so abu ya amfane su. Amma Saratu ta kafa misali mai kyau domin ba ta nuna son kai ba. Idan mun fi son nufin Allah ya cika maimakon namu, za mu nuna cewa muna yin koyi da bangaskiyar Saratu.
“KIN YI DARIYA”
Bayan ɗan lokaci, Hajaratu ta yi juna biyu, sai ta soma raina uwargidanta Saratu. Wataƙila tana tunani cewa ta fi uwargidanta daraja yanzu. Babu shakka, wannan abin taƙaici ne sosai ga Saratu! Da izinin maigidanta da kuma goyon bayan Allah, Saratu ta yi wa Hajaratu horo amma ba a gaya mana irin horon ba. Daga baya, Hajaratu ta haifi ɗa mai suna Isma’ilu. (Farawa 16:4-9, 16) Bayan shekaru da yawa sa’ad da Saratu take ’yar shekara 89 Ibrahim kuma 99, sai Jehobah ya sake aika musu saƙo. Wannan saƙo albishiri ne sosai!
Jehobah ya sake yi wa abokinsa Ibrahim alkawari cewa zai sa ’ya’yansa su cika ko’ina. Ƙari ga haka, Allah ya canja sunansa daga Abram zuwa Ibrahim wanda ke nufin “Uban Jama’a.” Jehobah ya kuma canja sunan Saraya wanda ke nufin “Masifaffiya” zuwa Saratu wanda mutane da dama suke amfani da shi a yau. Mene ne sunan yake nufi? Yana nufin “Sarauniya!” Jehobah yana da dalilin da ya sa ya ba ta sunan. Ya ce: “Zan albarkace ta, in ba ka ɗa kuma daga gareta: hakika, zan albarkace ta, za ta zama uwar al’ummai kuma: sarakunan al’ummai za su kasance daga gareta.” Wannan ne ƙaro na farko da Jehobah ya nuna yadda zai yi amfani da Saratu wajen cika nufinsa.—Farawa 17:5, 15, 16.
Ta wajen ɗan Saratu ne Jehobah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim cewa dukan al’ummai za su sami albarka ta wajen zuriyarsa. Allah ya ba yaron suna Ishaƙu wanda ke nufin “Dariya.” A lokaci na farko da Ibrahim ya ji cewa Saratu za ta haifa masa ɗa, sai ya “fāɗi a bisa fuskatasa, ya yi dariya.” (Farawa 17:17) Abin ya cika shi da mamaki da kuma farin ciki sosai. (Romawa 4:19, 20) Saratu fa?
Jim kaɗan bayan haka, sai baƙi uku suka zo tantin Ibrahim da tsakar rana. Duk da haka, waɗannan ma’auratan sun tashi don su marabce su. Ibrahim ya ce wa Saratu: “Ki shirya mudu uku na gari mai-laushi da hanzari, ki cuɗe, ki yi waina.” Marabtar baƙi a lokacin ba ƙaramin aiki ba ne. Ibrahim bai bar matarsa kaɗai ta yi aikin ba. Ya fita da sauri ya yanka sā, ya gyara kuma ya ƙaro abinci da abin sha. (Farawa 18:1-8) Daga baya ne suka san cewa “mutanen” mala’ikun Jehobah ne! Wataƙila wannan labarin ne manzo Bulus yake magana a kai sa’ad da ya ce: “Kada a manta a nuna ƙauna ga baƙi: gama garin yin wannan waɗansu sun ciyar da mala’iku ba da saninsu ba.” (Ibraniyawa 13:2) Zai dace mu riƙa nuna karimci ga baƙi yadda Ibrahim da Saratu suka yi.
Sa’ad da ɗaya daga cikin mala’ikun ya maimaita wa Ibrahim alkawarin Allah cewa Saratu za ta haifi ɗa, Saratu tana cikin tantinta tana ji. Maganar ta sa ta mamaki sosai har ba ta iya riƙe kanta ba. Sai ta soma dariya cikin zuciyarta, tana cewa: “Bayan da na tsufa zan sami annishuwa?” Sai mala’ikan ya yi wa Saratu gyara ta wajen yi mata tambaya, “Ko akwai abin da ya fi ƙarfin Ubangiji?” Tambayar ta sa Saratu tsoro, sai ta musunta maganar. Ta ce: “Ban yi dariya ba.” Amma mala’ikan ya ce, “A’a; amma dai kin yi dariya.”—Farawa 18:9-15.
Dariyar da Saratu ta yi ta nuna cewa ba ta da bangaskiya ne? A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurin bangaskiya har Saratu da kanta ta sami iko da za ta yi juna biyu sa’anda ta rigaya ta wuce lokaci, tun da ta aza shi mai-aminci ne wanda ya yi alkawari.” (Ibraniyawa 11:11) Saratu ta san cewa Jehobah zai cika dukan alkawuran da ya yi. Babu shakka, dukanmu na bukatar irin wannan bangaskiyar. Zai dace mu san Allahn da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki sosai. Idan mun yi haka, za mu ga cewa Saratu tana da dalilin kasancewa da bangaskiya. Hakika, Jehobah Allah ne mai aminci kuma yana cika dukan alkawuransa. A wasu lokuta, yana cika su a hanyar da ba mu taɓa tsammani ba, har ya sa mu dariya!
“KA JI MAGANARTA”
Sa’ad da Saratu take ’yar shekara 90, ta sami abin da ta daɗe tana nema. Ta haifa wa Ibrahim ɗa sa’ad da yake da shekara 100. Ibrahim ya sa wa yaron suna Ishaƙu ko kuma “Dariya,” daidai yadda Allah ya ce masa. Ku yi tunanin yadda Saratu Farawa 21:6) Babu shakka, wannan mu’ujizar ta sa ta farin ciki muddar ranta. Ƙari ga haka, kula da yaron babban hakki ne a gare ta.
take murmushi sa’ad da ta ce: “Allah ya sa na yi dariya; wanda ya ji ni duka kuma za ya yi dariya tare da ni.” (Iyayen Ishaƙu sun yi masa biki sa’ad da suka yaye shi yana ɗan shekara biyar. Amma wata babbar matsala ta taso. Littafi Mai Tsarki ya ce Saratu ta “hangi” Isma’ilu wanda yake da shekara 19 a lokacin yana yawan yi wa Ishaƙu ba’a. Wannan ba’ar ba wasan yara ba ne. Manzo Bulus ya ce Isma’ilu yana tsananta wa Ishaƙu. Saratu ta ga cewa hakan barazana ce sosai ga rayuwar yaronta. Ta san cewa Ishaƙu ba ɗa ba ne kawai a gare ta, amma Jehobah zai yi amfani da shi wajen cika nufinsa. Saboda haka, sai ta yi wa maigidanta magana da gaba gaɗi. Ta ce ya sallami Hajaratu da ɗanta Isma’ilu.—Farawa 21:8-10; Galatiyawa 4:22, 23, 29.
Mene ne Ibrahim ya ce? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abin nan fa ya yi wa Ibrahim ciwo ƙwarai saboda ɗansa.” Yana son Isma’ilu, kuma hakkinsa ne ya kula da shi. Amma Jehobah ya fahimci batun sosai. Sai ya ce wa Ibrahim: “Kada wannan ya zama abu mai-zafi a gare ka saboda saurayin, da baiwarka kuma; cikin dukan abin da Saratu ta faɗa maka, sai ka ji maganarta; gama daga cikin Ishaƙu za a kira zuriyarka.” Jehobah ya tabbatar wa Ibrahim da cewa zai kula da Hajaratu da kuma ɗanta. Sai Ibrahim ya yi abin da ta ce.—Farawa 21:11-14.
Saratu matar kirki ce kuma tana taimaka wa Ibrahim sosai. Ba kawai abin da maigidanta yake so ya ji take gaya masa ba. Amma sa’ad da ta ga matsalar da za ta shafi iyalinta, ta gaya wa maigidanta ra’ayinta. Gaskiyar da ta faɗa ba rashin kunya ba ne. Har manzo Bitrus wanda shi ma yana da aure ya ambata Saratu cikin matan da suka ladabta mazajensu. (1 Korintiyawa 9:5; 1 Bitrus 3:5, 6) A gaskiya, da a ce Saratu ta yi shuru, da hakan ya zama rashin kunya domin da dukansu sun fuskanci mummunan sakamako. Saratu ta faɗi abin da ya kamata ta faɗa cikin ladabi.
Mata da yawa suna son misalin Saratu domin ya koya musu yin magana cikin ladabi da mazajensu. Wasu mata suna cewa, ‘Da ma a ce Jehobah zai gaya wa maigidana ya bi shawarar da na bayar yadda ya yi da Saratu.’ Amma duk da haka, sun koyi kasancewa da bangaskiya da nuna ƙauna da kuma yin haƙuri kamar Saratu.
Jehobah ya kira Saratu “Sarauniya,” amma ba ta sa rai cewa za a bi da ita kamar sarauniya ba
Ko da yake Jehobah ya ba wannan matar suna “Sarauniya,” amma ba ta sa rai cewa za a bi da ita kamar sarauniya ba. Shi ya sa da ta rasu tana ’yar shekara 127, Ibrahim ya yi “makoki saboda Saratu, ya yi kuka kuma dominta.” * (Farawa 23:1, 2) Ya yi kewar “Sarauniyarsa” sosai. Babu shakka, Jehobah ma ya yi kewar wannan mata mai aminci. Nan ba da jimawa ba, zai tashe ta daga matattu sa’ad da ya mayar da duniyar nan aljanna. Saratu da kuma dukan mutanen da suka yi koyi da misalinta za su yi rayuwa har abada cikin kwanciyar hankali a aljanna.—Yohanna 5:28, 29.
^ sakin layi na 3 A dā, sunayensu Abram da Saraya. Amma daga baya, Allah ya canja sunayensu, kuma sunayen da za mu yi amfani da su ke nan a wannan talifin.
^ sakin layi na 10 Jehobah ya ƙyale maza su auri mata da yawa a dā. Amma daga baya, ya sa Yesu ya komar da aure yadda yake a lambun Adnin, wato namiji ya auri mace guda.—Farawa 2:24; Matta 19:3-9.
^ sakin layi na 25 Saratu ce kaɗai macen da aka ambata shekarunta sa’ad da ta rasu a cikin Littafi Mai Tsarki.