ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MALA’IKU?
Mala’iku Suna Taimaka Mana Kuwa?
Kenneth da matarsa Filomena da suke zama a ƙasar Curaçao, sun je wurin wasu ma’aurata da suke nazarin Littafi Mai Tsarki da su a ranar Lahadi da rana.
Kenneth ya ce, “Da muka isa gidan, mun sami ƙofar a rufe kuma ba mu ga motarsu ba. Amma wani abu ya ce mini in kira matar a waya.”
Matar ta amsa wayar kuma ta gaya musu cewa maigidanta ya tafi aiki. Amma da ta gane cewa suna waje, sai ta fito ta ce wa Kenneth da matarsa Filomena su shigo ciki.
A take suka gane cewa kuka take yi dama. Da Kenneth ya yi addu’a kafin su soma nazarin, sai matar ta soma kuka kuma. Sai Kenneth da Filomena suka tambaye ta abin da yake faruwa.
Matar ta gaya musu cewa dama tana so ta kashe kanta ne. Kuma tana kan rubuta wa maigidanta wasiƙa sa’ad da Kenneth ya kira ta a waya. Ta gaya musu cewa tana fama da baƙin ciki sosai. Sai suka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ƙarfafa ta. Ƙarfafa ta da suka yi ne ya hana matar kashe kanta.
Kenneth ya ce, “Mun gode wa Jehobah da ya sa muka taimaki wannan matar da take cikin damuwa, musamman ma don yadda ya yi amfani da ƙila mala’ikansa ko kuma ruhu mai tsarki ya sa muka kira ta a waya!” *
Shin da gaske ne cewa Allah ya yi amfani da mala’ikansa ko kuma ruhu mai tsarki don ya ja-goranci Kenneth da Filomena wurin wannan matar? Ko kuma, hakan ya faru ne kawai?
Ba mu san gaskiyar al’amarin ba. Amma mun san cewa Allah yana amfani da mala’ikunsa don su taimaka wa mutane su yi nufinsa. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya aika mala’ikansa ya ja-goranci Filibus zuwa wurin wani Bahabashe, wanda yake so ya koya game da Allah.—Ayyukan Manzanni 8:26-31.
Addinai da dama suna koyar da cewa akwai halittun ruhu masu iko sosai, kuma cewa wasu daga cikinsu masu kirki ne da suke yin nufin Allah ko kuma suke kāre ’yan Adam. Mutane da dama sun yi imani cewa mala’iku suna wanzuwa kuma suna taimaka musu a hanyoyi da yawa. Wasu mutane kuma ba su yarda cewa mala’iku suna wanzuwa ba.
Shin mala’iku suna wanzuwa kuwa? Idan haka ne, daga ina suka fito? Mece ce gaskiya game da mala’iku? Suna iya shafan rayuwarmu kuwa? Bari mu tattauna gaskiyar al’amarin.
^ sakin layi na 8 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.—Zabura 83:18.