Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Wane irin keken-doki ne mutumin Itiyofiya yake tafiya a ciki saꞌad da Filibus ya same shi?

A HELENANCI, kalmar nan “keken-doki” da aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki tana iya nufin karusai iri-iri. (A. M. 8:​28, 29, 38) Amma, kamar dai karusa ko keken-dokin da mutumin Itiyofiyan nan ya yi tafiya a ciki babba ne, ba irin ƙananan kekunan-doki da ake yaƙi ko kuma tsere da su ba. Ga wasu dalilan da suka sa muka faɗi haka.

Mutumin yana da matsayi sosai kuma ya zo daga wuri mai nisa. Yana da “babban matsayi a mulkin Kandis, sarauniyar Itiyofiya. Shi ne kuma maꞌajin sarauniyar.” (A. M. 8:27) Ƙasar Itiyofiya a dā ta haɗa da ƙasar Sudan da wani ɓangaren kudancin ƙasar Masar na yau. Wataƙila ba keken-dokin nan ne kawai mutumin ya yi dogon tafiya a ciki ba, kuma da alama ya yi tafiyar da kayayyaki da yawa. Wasu kekunan-doki da ake amfani da su a ɗauki fasinjoji, suna da tayoyi guda huɗu kuma a rufe suke. Wani littafi mai suna Acts—An Exegetical Commentary da ya yi bayani a kan littafin Ayyukan Manzanni ya ce: “Yin tafiya a irin keken-dokin nan yana da sauƙi, yana ba wa mutum damar ɗaukan kayayyaki da yawa, kuma da alama yana iya zuwa wurare masu nisa sosai.”

Mutumin Itiyofiyan yana karatu saꞌad da Filibus ya same shi. Littafi Mai Tsarki ya ce “Filibus ya gudu zuwa wurinsa, ya ji shi [bābān] yana karatun littafin annabi Ishaya.” (A. M. 8:30) Kekunan-doki da ake tafiya da su ba sa guduwa sosai. Keken-dokin ba ya guduwa sosai, shi ya sa mutumin Itiyofiyan ya iya yin karatu a ciki, kuma Filibus ya same shi da kafa.

Mutumin Itiyofiyan “ya ce wa Filibus ya hau keken-dokin su zauna tare.” (A. M. 8:31) Keken-doki da ake tsere da shi ba shi da wurin zama. Don haka, matukansa tsayawa suke yi. Amma keken-doki da ake tafiya a ciki yana da wurin zama, shi ya sa mutumin Itiyofiyan da Filibus suka zauna a ciki.

Saboda abin da ke littafin Ayyukan Manzanni sura 8 da kuma abubuwan da ꞌyan tarihi suka gano, littattafanmu na kwana-kwanan nan sun nuna mutumin Itiyofiyan yana tafiya a cikin keken-doki da ke da girma, ba ƙarami wanda ake yaƙi da shi ko kuma tsere ba.