Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina

Jehobah Yana Ƙaunar Ka Sosai

Jehobah Yana Ƙaunar Ka Sosai

“Uban yana ƙaunarku da kansa.”YOH. 16:27.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda sanin irin ƙaunar da Jehobah yake da shi zai sa mu ƙara kusantarsa, ya ba mu kwanciyar hankali, kuma ya tabbatar mana cewa zai kula da mu.

1. A ganinka, yaya Jehobah yake?

 KA TAƁA tunanin yadda Jehobah yake? Idan kana adduꞌa, wane irin tunani kake yi game da shi? Ko da yake ba ma iya ganin Jehobah, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mana yadda yake a hanyoyi da yawa. Alal misali, an kwatanta shi da ‘haske’ da ‘garkuwa’ da kuma ‘wuta mai cinyewa.’ (Zab. 84:11; Ibran. 12:29) An kuma kwatanta shi da dutsen saffaya mai daraja, da ƙarfen da aka goge kuma yana ƙyalli, da kuma bakan gizo da ke haskakawa. (Ezek. 1:​26-28) Idan muka yi tunanin yadda aka kwatanta Jehobah a ayoyin nan, mai yiwuwa ya sa mu yi mamaki ko kuma ya tsoratar da mu.

2. Me yake sa ya yi ma wasu wuya su yarda cewa Jehobah yana ƙaunar su?

2 Da yake ba mu taɓa ganin Jehobah ba, ƙila yana yi mana wuya mu yarda cewa yana ƙaunar mu. Wasu kuma abin da ya taɓa faruwa a rayuwarsu ne ya sa suke ganin ba zai yiwu Jehobah ya ƙaunace su ba. Mai yiwuwa mahaifinsu bai nuna musu ƙauna ba. Jehobah ya san dukan abubuwan nan kuma ya san cewa zai iya yi mana wuya mu yarda da ƙaunarsa a gare mu. Shi ya sa ya gaya mana halayensa masu kyau a Littafi Mai Tsarki.

3. Me ya sa yake da kyau mu ƙara yin bincike a kan ƙaunar Jehobah?

3 Hali mafi girma da Jehobah yake da shi, shi ne ƙauna. Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) Duk abin da Jehobah yake yi saboda ƙaunarsa ne. Allah yana da ƙauna sosai shi ya sa yake nuna ƙauna ga kowa, har da waɗanda ba sa ƙaunar sa. (Mat. 5:​44, 45) A wannan talifin, za mu yi bincike sosai game da Jehobah da kuma ƙaunarsa. Idan muka ƙara sanin Allahn da muke bauta wa, hakan zai sa mu ƙara ƙaunar sa.

JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU SOSAI

4. Yaya tunanin yawan ƙaunar Jehobah yake sa ka ji? (Ka kuma duba hoton.)

4 Jehobah “mai yawan tausayi” ne. (Yak. 5:11) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙaunarsa da irin ƙaunar da mahaifiya take yi wa ɗanta. (Isha. 66:​12, 13) Ka yi tunanin yadda uwa take kula da jaririnta. Takan ɗaga shi ta sa shi a cinyarta, kuma takan yi masa maganganu masu daɗin ji. Idan ya soma kuka ko wani abu yana damun sa, takan tabbata cewa ta samo masa abin da yake bukata. Mu ma idan muna cikin matsala, Jehobah yana kula da mu saboda ƙaunarsa. Wani marubucin Zabura ya ce: “Saꞌad da damuwoyi sukan yi mini yawa, taꞌaziyarka takan ƙarfafa raina.”—Zab. 94:19.

“Yadda mama take taꞌazantar da yaronta, haka zan taꞌazantar da ku” (Ka duba sakin layi na 4)


5. Ya kake ji in ka tuna cewa ƙaunar da Jehobah yake maka marar canjawa ce?

5 Jehobah Allah mai aminci ne. (Zab. 103:8) Ko da mun yi abin da bai dace ba, ba zai daina ƙaunarmu ba. Israꞌilawa sun yi ta yin abin da ya ɓata wa Jehobah rai. Amma da suka tuɓa, ya nuna musu cewa ƙaunarsa a gare su ba ta canja ba, ya ce: ‘Kuna da daraja a idanuna, ina girmama ku, ina kuma ƙaunarku.’ (Isha. 43:​4, 5) Irin ƙaunar da Jehobah yake yi mana ke nan, a koyaushe yana ƙaunar mu. Ko da mun yi zunubi mai tsanani, Jehobah ba zai yashe mu ba. Za mu ga cewa har yanzu yana ƙaunar mu sosai. Ya ce zai “yi gafara a yalwace.” (Isha. 55:​7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Littafi Mai Tsarki ya ce idan Jehobah ya gafarta wa mutum, yakan sami wartsakewa.—A. M. 3:19.

6. Mene ne littafin Zakariya 2:8 ta koya mana game da Jehobah?

6 Karanta Zakariya 2:8. Saboda ƙaunar da Jehobah yake yi mana, da zarar wani abu ya same mu, shi ma yakan ji shi a ransa kuma yana so ya kāre mu. Shi ya sa kowannenmu zai iya roƙon Jehobah cewa: ‘Ka kiyaye ni kamar ƙwayar idonka.’ (Zab. 17:8) Ƙwayar ido yana saurin jin zafi, kuma ba ma wasa da shi. Don haka, da Jehobah ya ce mu kamar ƙwayar idonsa ne, yana nufin cewa, duk wanda ya taɓa mu ya taɓa abin da Jehobah ba ya wasa da shi.

7. Me ya sa muke bukatar mu ƙara tabbatar wa kanmu cewa Jehobah yana ƙaunar mu?

7 Jehobah yana so ka san cewa yana ƙaunar ka. Amma ya san cewa wani lokaci saboda abin da ya taɓa faruwa da mu, za mu iya ganin kamar ba zai iya ƙaunar mu ba. Mai yiwuwa kuma, kana cikin wani hali a yanzu da ke sa ya yi maka wuya ka gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar ka. Me zai taimaka maka? Wani abin da zai tabbatar maka cewa Jehobah yana ƙaunar ka shi ne idan ka ga yadda Jehobah ya bayyana ƙaunarsa ga Yesu, da shafaffun Kiristoci da kuma dukanmu.

YADDA JEHOBAH YA NUNA ƘAUNARSA

8. Me ya sa Yesu bai yi shakkar cewa Jehobah yana ƙaunar sa ba?

8 Jehobah da Yesu sun daɗe suna rayuwa fiye da kowa. A biliyoyin shekaru da suka yi suna tare a sama, sun kusanci juna sosai kuma sun ƙaunaci juna. Da bakinsa, Jehobah ya bayyana yadda yake ƙaunar Yesu a littafin Matiyu 17:5. A ayar nan, da Jehobah zai gaya mana kawai cewa, ‘Wannan shi ne wanda nake jin daɗinsa.’ Amma da yake yana so mu san yawan ƙaunar da yake yi wa Yesu, ya ce da shi “Ɗana, wanda nake ƙauna.” Jehobah yana alfahari da Yesu, musamman don yadda ya yarda ya ba da ransa dominmu. (Afis. 1:7) Yesu shi ma ya san cewa Jehobah yana ƙaunar sa sosai, bai taɓa yin shakkar cewa Ubansa yana ƙaunar sa ba ko kaɗan. Akwai lokuta da yawa da Yesu ya bayyana cewa Jehobah yana ƙaunar sa sosai.—Yoh. 3:35; 10:17; 17:24.

9. Wane furuci ne ya nuna irin ƙaunar da Jehobah yake yi wa shafaffun Kiristoci? Ka bayyana. (Romawa 5:5)

9 Jehobah ya kuma tabbatar wa shafaffun Kiristoci cewa yana ƙaunar su. (Karanta Romawa 5:5.) Ayar ta ce: ‘Ya zuba ƙaunarsa cikin zukatansu.’ Wani littafi da ke bayyana kalmomin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda Allah ya zubo musu ƙaunarsa da yadda ruwan rafi yake “zubowa daga kan tudu.” Wannan kwatancin ya nuna yawan ƙaunar da Jehobah yake yi wa Kiristoci shafaffu! Shafaffun Kiristoci sun san cewa Jehobah yana ƙaunar su sosai. (Yahu. 1) Manzo Yohanna ya gaya mana yadda suke ji. Ya ce: “Ina misalin ƙaunar da Uban ya yi mana a yalwace, har da ake ce da mu ꞌyaꞌyan Allah!” (1 Yoh. 3:1) Amma shafaffun Kiristoci ne kawai Jehobah yake ƙauna? Aꞌa, Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar dukanmu.

10. Mene ne ya fi tabbatar maka da cewa Jehobah yana ƙaunar ka?

10 Mene ne ya fi tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu? Fansar da ya bayar ne. Babu wanda ya taɓa nuna irin wannan ƙaunar! (Yoh. 3:16; Rom. 5:8) Jehobah ya ba da Ɗansa wanda yake ƙauna sosai, ya bar shi ya mutu domin a iya gafarta zunubanmu, kuma mu iya zama aminansa. (1 Yoh. 4:10) Idan muka yi tunani mai zurfi a kan irin sadaukarwar da Jehobah da Yesu suka yi, hakan zai sa mu fahimci irin ƙaunar da suke yi wa kowannenmu. (Gal. 2:20) A gun Jehobah, ana bukatar a ba da fansar don a yi adalci, amma ba abin da ya sa ya ba da fansar ke nan ba. Ya yi hakan ne don yana ƙaunar mu. Kuma wanda ya fi daraja a gare shi ne Jehobah ya bayar, wato Yesu. Hakan ya nuna cewa yana ƙaunar mu sosai. Jehobah ya yarda Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu domin mu.

11. Mene ne littafin Irmiya 31:3 ta koya mana?

11 Kamar yadda muka gani, Jehobah yana ƙaunar mu kuma ya gaya mana hakan da bakinsa. (Karanta Irmiya 31:3.) Jehobah yana ƙaunar mu shi ya sa ya jawo mu gunsa. (Ka ga misalin hakan a Maimaitawar Shariꞌa 7:​7, 8.) Babu abin da zai iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana. (Rom. 8:​38, 39) Yaya wannan ƙaunar take sa ka ji? Ka karanta Zabura sura 23 don ka ga yadda Dauda ya ji saꞌad da ya yi tunani a kan yadda Jehobah ya ƙaunace shi kuma ya kula da shi. Ayoyin nan za su kuma ƙara ba ka tabbacin cewa Jehobah zai kula da kai.

YAYA ƘAUNAR JEHOBAH TAKE SA KA JI?

12. A taƙaice, mene ne littafin Zabura sura 23 ta koya mana?

12 Karanta Zabura 23:​1-6. Zabura sura 23, waƙa ce da ta nuna tabbacin da Dauda yake da shi cewa Jehobah yana ƙaunar sa kuma zai kula da shi. A wannan Zaburar, Dauda ya bayyana irin ƙaunar da ke tsakaninsa da Makiyayinsa, wato Jehobah. Dauda ya bar Jehobah ya yi masa ja-goranci, kuma ya dogara gare Shi da dukan zuciyarsa. Dauda ya san cewa ƙaunar Jehobah marar canjawa za ta yi ta bin shi dukan kwanakin rayuwarsa. Me ya ba shi wannan tabbacin?

13. Me ya tabbatar wa Dauda cewa Jehobah zai kula da shi?

13 ‘Ba zan rasa kome ba.’ Dauda ya ce bai rasa kome ba domin a ko da yaushe Jehobah yana ba shi abin da yake bukata. Dauda ya kuma san cewa Jehobah abokinsa ne kuma ya yarda da shi. Shi ya sa ya kasance da tabbaci cewa ko da me zai faru, Jehobah zai biya masa dukan bukatunsa. Maimakon Dauda ya riƙa damuwa, ya riƙa farin ciki kuma ya gamsu, domin ya san cewa Jehobah yana ƙaunarsa kuma zai kula da shi.—Zab. 16:11.

14. Mene ne Jehobah zai iya yi mana don ya nuna cewa yana ƙaunar mu da kula da mu?

14 Jehobah yakan kula da mu sosai musamman idan wani mummunan abu ya faru mu. Akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Claire a da ta yi fiye da shekaru 20 tana hidima a Bethel. A lokacin da matsaloli suka yi ta abko ma ꞌyan iyalinta, ꞌyarꞌuwar ta rasa abin da za ta yi don ta taimaka musu. Mahaifinta ya kamu da cutar shanyewar jiki kuma an yi wa ƙanwarta yankan zumunci. Ɗan sanaꞌa da suke yi a gidan ma sun ƙasa yin sa, kuma banki ya kwace gidansu. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar su? ꞌYarꞌuwa Claire ta ce: “Kowace rana, Jehobah ya yi ta yi wa ꞌyan iyalina tanadin abin da suke bukata. Akwai lokuta da yawa da Jehobah ya yi mana tanadi fiye da abin da muke bukata. Nakan yi tunanin lokutan da Jehobah ya taimaka mana, kuma ba zan taɓa manta da ƙaunarsa ba. Idan na tuna da abin da ya yi mana, hakan yana sa in ci-gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki duk da matsalolin da nake fuskanta.”

15. Me ya sa Dauda ya ce Jehobah ya sabunta ransa? (Ka kuma duba hoton.)

15 ‘Yakan sabunta raina.’ Akwai lokutan da Dauda ya gaji sosai saboda matsalolin da yake fuskanta. (Zab. 18:​4-6) Amma yadda Jehobah ya kula da shi ya sabunta ransa. Kamar dai Jehobah ya bi da abokinsa “wuraren kiwo masu ɗanyar ciyawa” ne da “gefen tafkunan ruwa masu gudu a hankali” don ya samu ya huta. Hakan ya sa Dauda ya sake samun ƙarfin ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci.—Zab. 18:​28-32.

Har a lokacin da Dauda ya gaji sosai tsananin damuwa, ƙaunar Jehobah da kulawarsa sun sabunta ransa (Ka duba sakin layi na 15)


16. Ka gaya mana yadda ƙaunar da Jehobah ya nuna maka ta sa ka wartsake.

16 A yau ma, “ƙaunar Jehobah marar canjawa ne ya sa ba mu halaka ba” duk da matsalolin da muke fuskanta a rayuwa. (Mak. 3:​22, New World Translation; Kol. 1:11) Misali, akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Rachel. Ta yi baƙin ciki sosai da maigidanta ya daina bauta wa Jehobah kuma ya gudu ya bar ta a lokacin annobar korona. Mene ne Jehobah ya yi mata? Ta ce: “Jehobah ya nuna min cewa yana ƙauna ta. Ya sa ꞌyanꞌuwa sun yi ta kawo min ziyara, sun zauna da ni, sun kawo min abinci, sun riƙa tura min saƙonni da nassosi don su ƙarfafa ni. Suna yin murmushi idan suka gan ni kuma sun yi ta tuna min da cewa Jehobah yana kula da ni. A ko da yaushe, ina godiya ga Jehobah don ya ba ni babban iyali da suke ƙauna ta.”

17. Me ya sa Dauda bai “ji tsoron kome ba”?

17 ‘Ba zan ji tsoron kome ba, gama kana nan tare da ni.’ Akwai lokuta da yawa da aka so a kashe Dauda kuma ya yi fama da maƙiya sosai. Amma ya san cewa Jehobah zai kāre shi domin yana ƙaunar sa. Dauda ya san cewa Jehobah yana tare da shi a kowane lokaci, hakan ya ƙarfafa shi. Shi ya sa ya ce: “[Jehobah] ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.” (Zab. 34:4) Ko da yake akwai lokutan da Dauda ya ji tsoro sosai, Ya shawo kan wannan tsoro domin ya san cewa Jehobah yana ƙaunar sa.

18. Idan ka tabbata cewa Jehobah yana ƙaunar ka, ta yaya hakan zai ƙarfafa ka saꞌad da kake jin tsoro?

18 Ta yaya sanin cewa Jehobah yana ƙaunar mu yake ƙarfafa mu saꞌad da muke cikin masifa? Wata ꞌyarꞌuwa da majagaba ce mai suna Susi ta faɗi yadda ita da maigidanta suka ji lokacin da ɗansu ya kashe kansa. Ta ce: “Idan mugun abu ya faru da mutum, yakan yi masa zafi sosai kuma ya ji kamar ba shi da mai taimako. Amma ƙaunar da Jehobah ya nuna mana ta sa hankalinmu ya kwanta.” ꞌYarꞌuwa Rachel da muka ambata a baya ta ce: “Akwai wata rana da dare da na ji baƙin ciki sosai. Na ji tsoro, sai na yi kuka ga Jehobah. Nan da nan, sai na ji kamar Jehobah ya zuba min ruwa mai sanyi a zuciyata, ya kwantar min da hankali kamar yadda uwa takan lallaɓi jaririnta. Sai barci ya ɗauke ni, ba zan taɓa manta da abin da ya faru ranar ba.” Akwai wani dattijo mai suna Tasos da aka ƙulle shi na shekaru huɗu a kurkuku don ya ƙi ya shiga soja. Ta yaya Jehobah ya nuna masa cewa yana ƙaunar sa, kuma ya damu da shi? Ya ce: “Jehobah ya ba ni dukan abubuwan da nake bukata har ma fiye da hakan. Wannan ya ƙara tabbatar min da cewa zan iya dogara da shi da dukan zuciyata. Ƙari ga haka, ta wurin ruhunsa mai tsarki, Jehobah ya sa na iya yin farin ciki, duk da cewa kurkuku wuri ne da zai iya sa mutum baƙin ciki sosai. Wannan ya tabbatar min cewa idan na ƙara dogara ga Jehobah, zan ƙara ganin cewa yana ƙauna ta. Don haka tun ina kurkuku, na soma yin hidimar majagaba na kullum.”

KA KUSACI ALLAHNKA MAI ƘAUNA

19. (a) Idan mun san cewa Jehobah yana ƙaunar mu, yaya adduꞌoꞌinmu za su kasance? (b) Me ya fi burge ka game da ƙaunar Jehobah? (Ka kuma duba akwatin nan “ Kalmomin da Suke Sa Mu Ji Cewa Jehobah Yana Ƙaunar Mu.”)

19 Labaran nan da muka tattauna sun nuna cewa Jehobah “Allah mai ƙauna” yana tare da mu. (2 Kor. 13:11) Ya damu da kowannenmu. Muna da tabbacin cewa ƙaunarsa marar canjawa ta “kewaye” mu. (Zab. 32:10) Idan muka ƙara yin tunani mai zurfi a kan yadda Jehobah ya nuna mana ƙauna, za mu ƙara ganin tabbaci cewa ya damu da mu sosai, kuma hakan zai sa mu ƙara kusantar sa. Za mu iya yin adduꞌa hankalinmu a kwance kuma mu roƙi Jehobah ya ci-gaba da nuna mana ƙaunarsa. Za mu iya gaya masa dukan abubuwan da ke damun mu don mun san cewa zai fahimce mu kuma yana so ya taimaka mana.—Zab. 145:​18, 19.

20. Ta yaya ƙaunar da Jehobah yake mana take sa mu yi kusa da shi?

20 Kamar yadda wuta take sa mu ji ɗumi idan ana sanyi, haka ma ƙaunar Jehobah tana ƙarfafa mu saꞌad da muke fuskantar matsaloli. Don haka, ka yi farin ciki sosai domin ƙaunar Jehobah za ta iya ƙarfafa ka kuma ta ba ka salama. Ka nuna cewa kai ma kana ƙaunar Jehobah kuma ka ce: “Ina ƙaunar [Jehobah].”—Zab. 116:1.

MECE CE AMSARKA?

  • Yaya za ka kwatanta ƙaunar da Jehobah yake mana?

  • Me ya tabbatar maka da cewa Jehobah yana ƙaunar ka sosai?

  • Yaya kake ji in ka tuna da irin ƙaunar da Jehobah yake maka?

WAƘA TA 108 Ƙauna ta Gaskiya Daga Allah

a An canja wasu sunayen.