Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 3

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

Jehobah Zai Taimaka Maka Idan Ka Shiga Yanayi Mai Wuya

Jehobah Zai Taimaka Maka Idan Ka Shiga Yanayi Mai Wuya

[Jehobah] zai kafa ku.”1 BIT. 5:10.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da za mu yi don Jehobah ya taimaka mana idan muka shiga yanayi mai wuya.

1-2. Waɗanne irin matsaloli ne bayin Jehobah suke fuskanta?

 IDAN wani abu marar kyau ya faru da mu, zai iya canja rayuwarmu gabaki ɗaya. Alal misali, wani ɗanꞌuwa mai suna Luis, a ya kamu da wata muguwar cutar kansa. Likita ya gaya masa cewa nan da ꞌyan watanni zai mutu. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Monika da maigidanta suna yin hidimarsu ga Jehobah da ƙwazo, sai wata rana Monika ta gano cewa mijinta da dattijo ne, yana yin zunubi a ɓoye. Wata ꞌyarꞌuwa marar aure mai suna Olivia ta gudu ta bar gidanta don ta ji cewa za a yi mahaukaciyar guguwa a yankinsu. Da ta dawo, sai ta ga cewa guguwar ta rushe gidanta. A cikin ƙanƙanin lokaci, rayuwar waɗannan ꞌyanꞌuwan ta canja gabaki ɗaya. Kai ma wani mugun abu ya taɓa faruwa da kai kuma ya canja rayuwarka gabaki ɗaya?

2 Ko da yake mu bayin Jehobah ne, mu ma muna fuskantar matsaloli kuma muna rashin lafiya kamar yadda sauran mutane suke yi. Ƙari ga haka, muna iya fuskantar hamayya ko kuma tsanantawa daga mutanen da ba sa son ganin mu. Jehobah ba ya hana abubuwan nan faruwa da mu, amma ya yi alkawarin cewa zai taimaka mana. (Isha. 41:10) Da taimakon Jehobah, ko da mun shiga yanayi mai wuya sosai, za mu iya yin farin ciki, mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu riƙe amincinmu. A wannan talifin, za mu ga hanyoyi huɗu da Jehobah yake taimaka mana saꞌad da muka shiga yanayi mai wuya. Za mu kuma ga abin da ya kamata mu yi don mu iya amfana daga taimakon da yake mana.

JEHOBAH ZAI TSARE KA

3. Me yake mana wuya mu yi idan muka shiga yanayi mai wuya sosai?

3 Matsalar. Idan muna fuskantar wani yanayi mai wuya, ba zai yi mana sauƙi mu natsu kuma mu yanke shawarar da ta dace ba. Me ya sa? Domin muna baƙin ciki sosai, mai yiwuwa ma mu karaya tsananin damuwa. Za mu ji kamar muna tafiya a inda hazo ya cika koꞌina, kuma mun rasa hanyar da za mu bi. Yadda ꞌyanꞌuwa mata biyu da muka ambata ɗazu suka ji ke nan. Olivia ta ce: “Da na ga cewa guguwar ta rushe gidana, na damu sosai kuma na rasa abin da zan yi.” Monika kuma da maigidanta ya ci amanarta ta ce: “Abin ya ɓata mini rai ba kaɗan ba, na ji kamar wuƙa aka caka min. Yin abubuwan da na saba yi kowace rana ma ya bi ya gagare ni.” Mene ne Jehobah ya ce zai yi mana saꞌad da muke cikin damuwa?

4. Wane alkawari ne Jehobah ya yi mana a Filibiyawa 4:​6, 7?

4 Abin da Jehobah yake yi. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya yi alkawari zai ba mu “salama.” (Karanta Filibiyawa 4:​6, 7.) Wannan salamar tana nufin kwanciyar hankali da kuma natsuwa da muke samu don muna da dangantaka mai kyau da Allah. Wannan salamar ta “wuce dukan ganewar ɗan Adam,” wato tana taimaka mana a hanya mai ban mamaki. Ka taɓa yin adduꞌa ga Jehobah kuma ka ji hankalinka ya kwanta? Mai yiwuwa abin ya ba ka mamaki. ‘Salamar’ da Jehobah ya ba ka ne ya sa ka ji hakan.

5. Ta yaya salamar Allah take kāre zukantanmu da tunaninmu?

5 Filibiyawa 4:7 ta kuma ce salamar Allah “za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku.” Ainihin kalmar da aka yi amfani da ita a nan tana nufin yadda sojoji suke “tsare” birni don kada a kai mata hari. Waɗanda suke zama a irin birnin nan suna barci har da minshari don sun san cewa akwai sojoji da suke kāre su. Hakazalika, idan Allah ya ba mu salama kuma tana tsare zukatanmu da tunaninmu, hankalinmu zai kwanta don mun san ba abin da zai same mu. (Zab. 4:8) Kamar Hannatu, za mu iya samun kwanciyar hankali ko da yanayin da muke ciki bai canja nan-da-nan ba. (1 Sam. 1:​16-18) Idan hankalinmu a kwance yake, zai yi mana sauƙi mu yi tunani da kyau kuma mu yanke shawarar da ta dace.

Ka yi ta yin adduꞌa, har sai Allah ya ba ka “salama” kuma ta tsare zuciyarka da tunaninka (Ka duba sakin layi na 4-6)


6. Mene ne za mu iya yi don mu sami salamar Allah? (Ka kuma duba hoton.)

6 Abin da muke bukatar mu yi. Idan kana cikin wata matsala, ka roƙi Jehobah ya tsare zuciyarka. Ta yaya? Ka yi ta yin adduꞌa har sai Allah ya ba ka salama. (Luk. 11:9; 1 Tas. 5:17) Ɗanꞌuwa Luis da muka ambata ɗazu ya faɗi abin da ya taimaka masa da matarsa mai suna Ana, saꞌad da suka ji cewa zai mutu nan da ꞌyan watanni. Ya ce: “A irin wannan yanayin, yana da wuya sosai mutum ya yanke shawara mai kyau game da jinya da dai sauransu. Amma da yake mun ta yin adduꞌa, mun samu kwanciyar hankali.” Luis da matarsa sun ce sun roƙi Jehobah ya ba su kwanciyar hankali, ya sa su samu natsuwa, kuma ya taimaka musu su iya yanke shawara mai kyau. Abin da Jehobah ya yi musu ke nan. Idan kai ma kana fama da yanayi mai wuya, ka yi ta yin adduꞌa ga Jehobah, kuma za ka ga yadda Jehobah zai ba ka salamar da za ta tsare zuciyarka da tunaninka.—Rom. 12:12.

JEHOBAH ZAI SA KA KAFU

7. Yaya muke ji idan muna cikin yanayi mai wuya?

7 Matsalar. Idan muna cikin wani yanayi mai wuya, yadda muke ji da yadda muke tunani da yadda muke yin abubuwa za su bambanta da yadda muka saba. Kamar yadda guguwa take juya jirgin ruwa nan da can, haka ma yanayi mai wuya zai iya shafan yadda muke ji a ranmu. Ana da muka ambata a baya, ta ce ta yi fama da abubuwa dabam-dabam bayan da maigidanta ya rasu. Ta ce: “Wasu lokuta, nakan soma baƙin ciki sosai har in ji na zama abin tausayi. Wani lokaci kuma nakan yi fushi cewa ya mutu.” Ƙari ga haka, takan ji kaɗaici, kuma yana mata wuya ta yanke shawarwarin da maigidanta ne yake yankewa a dā. A wasu lokuta takan ji kamar a kan teku take, kuma ana guguwa mai ƙarfi. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana idan muna fama da baƙin ciki da yake so ya fi ƙarfinmu?

8. Kamar yadda 1 Bitrus 5:10 ta ce, mene ne Jehobah ya yi alkawari zai yi mana?

8 Abin da Jehobah yake yi. Ya yi alkawari cewa zai sa mu kafu. (Karanta 1 Bitrus 5:10.) Idan ana guguwa, guguwar takan jijjiga jirgin ruwa, har ya yi kamar jirgin zai kife. Don haka, masu ƙera jirgin ruwa sukan saka wani abu da ke kama da fukafukai a gefen dama da hagu na ƙasan jirgin. Waɗannan fukafukan, sukan taimaka wa jirgin kada ya jijjigu da yawa, kuma hakan zai sa hankalin waɗanda suke cikin jirgin ya kwanta don sun san ba abin da zai same su. Amma waɗannan fukafukan sun fi yin aiki da kyau idan jirgin yana tafiya. Mu ma idan muka ci-gaba da bauta ma Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta, Jehobah zai taimaka mana kada mu jijjigu.

Ka yi amfani da kayan bincike da muke da su don su taimaka maka ka kafu (Ka duba sakin layi na 8-9)


9. Ta yaya kayan bincike da muke da su za su taimaka mana mu samu kwanciyar hankali? (Ka kuma duba hoton.)

9 Abin da muke bukatar mu yi. Idan kana cikin wani yanayi mai wuya sosai, ka yi iya ƙoƙarinka ka riƙa yin abubuwan da za su sa ka kusaci Allah. Ba za ka iya yin abubuwa yadda kake yin su a dā ba kam, amma ka san cewa Jehobah ya fahimci yanayinka. (Ka kuma duba Luka 21:​1-4.) Ƙari ga haka, ka nemi lokacin da za ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yin tunani a kan abin da ka karanta. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin Jehobah yana amfani da ƙungiyarsa don ya tanada mana abubuwan da za su taimaka mana saꞌad da muke fama da yanayi mai wuya. Idan kana so ka nemi talifin da ya dace da yanayinka, za ka iya amfani da Littafin Bincike don Shaidun Jehobah, ko kuma manhajar JW Library®. Monika da muka ambata ɗazu ta ce a duk lokacin da take baƙin ciki sosai, takan yi amfani da kayan bincikenmu don ta nemi shawara. Alal misali, ta yi bincike a kan kalmar nan, “fushi.” Akwai kuma lokacin da ta yi bincike a kan “cin amana” da kuma “aminci.” Ta yi ta karatu har sai da ta ji sauƙi. Ta ce: “A cikin damuwa nake saꞌad da na soma binciken, amma da na ci-gaba da karatu sai na ji kamar Jehobah ya zo ya rungume ni. Na ga cewa Jehobah ya fahimci yadda nake ji kuma yana taimaka mini.” Kai ma Jehobah zai iya taimaka maka ka samu kwanciyar hankali ta wannan hanyar.—Zab. 119:​143, 144.

JEHOBAH ZAI TAIMAKA MAKA

10. Ya muke ji idan wani abu marar kyau ya faru da mu?

10 Matsalar. Bayan wani abu marar kyau ya faru da mu, akwai lokutan da za mu ji kamar ba mu da ƙarfi. Za mu ji kamar ɗan tsere da ya iya gudu sosai, amma yanzu ɗingishi yake yi don ya ji rauni. Za ma mu ga cewa, aikin da muke yi cikin sauƙi a dā yana so ya gagare mu, ko kuma mu ga cewa ba ma marmarin yin abin da muke son yi a dā. Kamar Iliya, ƙila mu ji kamar kada mu tashi daga kan gado, barci kawai muke so mu riƙa yi. (1 Sar. 19:​5-7) Mene ne Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi mana idan ba mu da ƙarfi?

11. A wace hanya ce kuma Jehobah yake taimaka mana? (Zabura 94:18)

11 Abin da Jehobah yake yi. Ya yi alkawari cewa zai tallafa mana. (Karanta Zabura 94:18.) Ɗan tsere da ya ji ciwo, zai bukaci abin da zai taimaka masa ya riƙa tafiya. Mu ma muna bukatar taimako don mu ci-gaba da bauta wa Jehobah. Ga abin da Jehobah ya yi alkawarin zai yi mana saꞌad da muke yanayi mai wuya. Ya ce: “Ni Yahweh Allahnka ne, ina riƙe da hannun damanka. Ni ne kuma nake ce maka, ‘Kada ka ji tsoro, ni ne mai taimakonka.’” (Isha. 41:13) Abin da ya faru da sarki Dauda ke nan. A lokacin da matsaloli suka masa yawa kuma maƙiyansa suna neman su kashe shi, ya ce ‘hannun daman’ Jehobah ya riƙe shi. (Zab. 18:35) Amma ta yaya Jehobah yake tallafa wa bayinsa?

Ka amince da taimakon ꞌyan iyalinku da abokanka da kuma dattawa (Ka duba sakin layi na 11-13)


12. Su wane ne Jehobah zai iya amfani da su don ya taimaka mana saꞌad da muka karaya?

12 Jehobah yana yawan amfani da mutane don ya taimaka mana. Alal misali, akwai lokacin da Dauda ya karaya, sai amininsa Jonathan ya ziyarce shi kuma ya ƙarfafa shi. (1 Sam. 23:​16, 17) Haka ma yake da Iliya, Jehobah ya yi amfani da Elisha don ya taimaka masa. (1 Sar. 19:​16, 21; 2 Sar. 2:2) A yau, Jehobah yana amfani da ꞌyan iyalinmu ko abokanmu ko kuma dattawa don ya taimaka mana. Amma idan muna fama da baƙin ciki, wani lokaci mukan ƙi yin shaꞌani da mutane don muna so mu kasance mu kaɗai. Kowa ma yakan ji hakan. Amma mene ne za mu yi don Jehobah ya taimaka mana?

13. Mene ne muke bukatar mu yi don mu amfana daga yadda Jehobah yake tallafa mana? (Ka kuma duba hoton.)

13 Abin da muke bukatar mu yi. Mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu ware kanmu daga mutane. Idan muka ware kanmu daga mutane, tunanin kanmu da matsalolin da muke fuskanta kawai za mu riƙa yi. Yin irin wannan tunanin kuma zai shafi shawarwarin da muke yankewa. (K. Mag. 18:1) Gaskiyar ita ce, wani lokaci dukanmu muna bukatar a bar mu mu kaɗai musamman ma saꞌad da muke yanayi mai wuya. Amma idan muka ware kanmu daga mutane na dogon lokaci, ba za mu amfana daga mutanen da Jehobah yake amfani da su don ya taimaka mana ba. Don haka, ka yi iya ƙoƙarinka ka amince da taimakon da ꞌyan iyalinku da abokanka da dattawa suke yi maka, ko da yin hakan yana maka wuya. Ka tuna cewa Jehobah ne yake amfani da su don ya taimaka maka.—K. Mag. 17:17; Isha. 32:​1, 2.

JEHOBAH ZAI ƘARFAFA KA

14. Wane yanayi mai ban tsoro ne za mu iya fuskanta?

14 Matsalar. Muna iya samun kanmu a yanayi mai ban tsoro. A Littafi Mai Tsarki, akwai wasu bayin Allah masu aminci da suka faɗi lokutan da suka damu kuma suka ji tsoro don maƙiyansu da dai sauransu. (Zab. 18:4; 55:​1, 5) Mu ma muna iya fuskantar hamayya daga ꞌyan makarantarmu ko ꞌyan iyalinmu ko kuma hukumomin gwamnati. Za mu iya jin tsoro cewa za mu mutu saboda cutar da muke fama da ita. A irin wannan yanayi, mukan zama kamar yaro kuma mu rasa na yi. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana a irin wannan yanayin?

15. Wane tabbaci ne yake littafin Zabura 94:19?

15 Abin da Jehobah yake yi. Yana taꞌazantar da mu kuma ya ƙarfafa mu. (Karanta Zabura 94:19.) Za mu iya kwatanta abin da ayar nan ta ce, da yadda mahaifi yake taimaka wa ꞌyarsa saꞌad da ta kasa yin barci don tana tsoron tsawa da walƙiya. Mahaifin zai shigo ɗakinta, ya rungume ta kuma ya riƙe ta har sai ta yi barci. Ko da an ci-gaba da yin walƙiyar, yadda mahaifinta ya rungume ta zai sa hankalinta ya kwanta. Mu ma idan muna cikin yanayi mai ban tsoro, za mu bukaci Ubanmu na sama ya riƙe mu har sai hankalinmu ya kwanta. Me muke bukatar mu yi don Jehobah ya ƙarfafa mu?

Ka bar Jehobah ya yi amfani da Nassosi ya ƙarfafa ka (Ka duba sakin layi na 15-16)


16. Mene ne muke bukatar mu yi don Jehobah ya ƙarfafa mu? (Ka kuma duba hoton.)

16 Abin da muke bukatar mu yi. Ka riƙa yin adduꞌa ga Jehobah da kuma karanta Kalmarsa. (Zab. 77:​1, 12-14) Hakan zai sa ka yi saurin neman taimakonsa saꞌad da kake cikin matsala. Ka gaya masa damuwarka, da kuma abin da kake jin tsoron sa. Bayan haka, ka saurare shi ta wajen karanta Kalmarsa, saꞌan nan za ka ga yadda zai ƙarfafa ka. (Zab. 119:28) Za ka ga cewa wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki suna ƙarfafa ka musamman ma saꞌad da kake jin tsoro. Za ka iya samun ƙarfafa daga abin da ke cikin littafin Ayuba, da Zabura, da Karin Magana, da kuma kalmomin Yesu a cikin Matiyu sura 6. Idan kana yin adduꞌa ga Jehobah kuma kana karanta Kalmarsa, za ka ga yadda zai ƙarfafa ka.

17. Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?

17 Za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana idan wani abu marar kyau ya faru. Jehobah ba zai taɓa barin mu mu kaɗai ba. (Zab. 23:4; 94:14) Jehobah ya yi alkawarin cewa zai tsare mu, zai sa mu kafu, zai tallafa mana, kuma zai ƙarfafa mu. Littafin Ishaya 26:3 ta gaya mana abin da Jehobah yake yi wa bayinsa. Ta ce: “Ga wanda ya kafa hankalinsa a kanka, kakan ba da cikakkiyar salama. Kakan ba shi salama gama yana dogara a gare ka.” Don haka, ka dogara ga Jehobah kuma ka amince da hanyoyin da yake amfani da su don ya taimaka maka. In ka yi hakan, za ka sami kwanciyar hankali ko a lokacin da kake yanayi mai wuya.

MECE CE AMSARKA?

  • A wane lokaci ne muka fi bukatar taimakon Jehobah?

  • Waɗanne hanyoyi huɗu ne Jehobah yake amfani da su don ya taimaka mana?

  • Mene ne za mu yi don mu samu taimakon Jehobah?

WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko

a An canja wasu sunayen.