Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 1

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

Ka Dogara ga Jehobah Saꞌad da Kake Jin Tsoro

Ka Dogara ga Jehobah Saꞌad da Kake Jin Tsoro

JIGON SHEKARA NA 2024: “Duk lokacin da na ji tsoro, zan dogara gare ka.”ZAB. 56:3.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu koyi yadda za mu ƙara dogara ga Jehobah, da yadda za mu kasance da kwanciyar hankali saꞌad da muke jin tsoro.

1. Mene ne zai iya sa mu ji tsoro a wasu lokuta?

 DUKANMU mukan ji tsoro a wasu lokuta. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa ba ma tsoron waɗanda suka mutu ko kuma abin da zai faru a nan gaba. Amma muna rayuwa ne a lokacin da “abubuwa masu ban tsoro” suke faruwa, kamar yaƙi, da taꞌaddanci da kuma cututtuka. (Luk. 21:11) Ƙari ga haka, muna iya jin tsoron mutane kamar hukumomin gwamnati da suke tsananta mana, ko ꞌyan iyalinmu da ba sa so mu bauta wa Jehobah. Wasu suna jin tsoro cewa ba za su iya jimre matsalolin da suke fuskanta yanzu ba, ko wanda za su fuskanta a nan gaba.

2. Me ya faru da Dauda saꞌad da yake birnin Gat?

2 Akwai lokutan da Dauda ya ji tsoro. Alal misali, saꞌad da Sarki Saul yake so ya kashe shi, Dauda ya gudu ya je wani birni mai suna Gat, kuma wurin birnin Filistiyawa ne. Ba da daɗewa ba, sai sarkin Gat mai suna Akish ya gano cewa Dauda shi ne jarumin da aka yi wa kirari da cewa ya kashe ‘dubun dubban’ Filistiyawa. Hakan ya sa Dauda ya ‘ji tsoro sosai.’ (1 Sam. 21:​10-12) Ya damu da abin da Akish zai iya yi masa. Me ya taimaka wa Dauda ya daina jin tsoro?

3. Bisa ga abin da ke Zabura 56:​1-3, 11, me ya taimaka wa Dauda ya daina jin tsoro?

3 A littafin Zabura sura 56, Dauda ya bayyana yadda yake ji saꞌad da yake birnin Gat. Littafin ya nuna yadda Dauda ya ji tsoro, amma ya kuma nuna abin da ya taimaka masa ya daina jin tsoro. Dauda ya dogara ga Jehobah a duk lokacin da ya ji tsoro. (Karanta Zabura 56:​1-3, 11.) Kuma Jehobah bai yashe shi ba. Da taimakon Jehobah, ya yi wata dabara da ba a saba yi ba kuma dabarar ta taimaka masa sosai. Dauda ya yi kamar ya haukace. Don haka, maimakon Akish ya yi tunanin kashe Dauda, ya ce bai ma kamata a kawo shi wurin sa ba. Yadda aka yi ke nan Dauda ya tsira.—1 Sam. 21:13–22:1.

4. Me zai sa ka ƙara dogara ga Jehobah? Ka ba da misali.

4 Mu ma idan muka dogara ga Jehobah, za mu daina jin tsoro. Amma, ta yaya za mu ƙara dogara ga Jehobah musamman saꞌad da muke jin tsoro? Ga wani misali, idan likita ya gaya maka cewa kana da wata cuta, za ka ji tsoro. Amma idan ka yarda da likitan, hankalinka zai kwanta, musamman idan ya saba yi wa masu irin wannan cutar jinya kuma suna warkewa. Likitan zai saurare ka da kyau, kuma zai tabbatar maka da cewa ya fahimci yadda kake ji. Yana iya gaya maka game da wata jinya da ta taimaka ma wasu su warke. Hakazalika, za mu ƙara dogara ga Jehobah idan muka tuna abin da ya riga ya yi, da abin da yake yi yanzu, da kuma wanda zai yi mana a nan gaba. Abin da ya taimaka wa Dauda ke nan. Yayin da muke bincika abin da Jehobah ya sa Dauda ya rubuta a Zabura sura 56, ka yi tunanin yadda kai ma za ka iya ƙara dogara ga Jehobah kuma ka daina jin tsoro.

MENE NE JEHOBAH YA RIGA YA YI?

5. A lokacin da Dauda yake jin tsoro, waɗanne abubuwa ne ya yi tunani a kai? (Zabura 56:​12, 13)

5 Ko da yake Dauda yana cikin haɗari, ya mai da hankali a kan abin da Jehobah ya riga ya yi masa. (Karanta Zabura 56:​12, 13.) Abin da Dauda ya riƙa tunanin sa ke nan a dukan rayuwarsa. Alal misali, a wasu lokuta ya yi tunani a kan halittun Jehobah, kuma hakan ya tuna masa da irin ikon da Jehobah yake da shi, da ƙaunar da yake wa ꞌyan Adam. (Zab. 65:​6-9) Ya kuma yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi ma wasu mutane. (Zab. 31:19; 37:​25, 26) Ban da haka, ya yi tunani a kan abin da Jehobah ya riga ya yi masa. Tun lokacin da Dauda yake ƙarami, Jehobah ya yi ta taimaka masa kuma ya kāre shi. (Zab. 22:​9, 10) Hakika, yin tunanin abubuwan nan, sun taimaka wa Dauda ya ƙara dogara ga Jehobah!

Dauda ya ƙara dogara ga Jehobah ta wajen mai da hankali ga abin da Jehobah ya riga ya yi, da waɗanda yake yi, da kuma waɗanda zai yi a nan gaba (Ka duba sakin layi na 5, 8, 12) d


6. Idan muna jin tsoro, mene ne zai taimaka mana mu dogara ga Jehobah?

6 Idan kana jin tsoro, ka tambayi kanka cewa, ‘Mene ne Jehobah ya riga ya yi min?’ Ka yi tunani a kan abubuwan da ya halitta. Alal misali, ba a kamanninsa ne Jehobah ya halicci tsuntsaye da furanni ba, kuma ba za su iya bauta masa ba. Amma idan muka “dubi” yadda yake kula da su, hakan zai sa mu ƙara gaskata cewa mu ma zai kula da mu. (Mat. 6:​25-32) Ƙari ga haka, ka yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi wa bayinsa. Kana iya yin nazari game da wani a Littafi Mai Tsarki da ya nuna bangaskiya, ko ka karanta labaran bayin Jehobah a zamaninmu. a Ban da haka, ka yi tunani a kan yadda Jehobah ya kula da kai. Ta yaya ya taimaka maka ka san game da shi? (Yoh. 6:44) Ta yaya ya amsa adduꞌoꞌinka? (1 Yoh. 5:14) Ta yaya kake amfana daga fansar da Ɗansa ya bayar?—Afis. 1:7; Ibran. 4:​14-16.

Za mu ƙara dogara ga Jehobah idan muna tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi, da waɗanda yake yi yanzu, da waɗanda zai yi a nan gaba (Ka duba sakin layi na 6, 9-10, 13-14) e


7. Ta yaya labarin Daniyel ya taimaka wa Vanessa ta daina jin tsoro?

7 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Vanessa b a ƙasar Haiti, ta shiga wani yanayi mai ban tsoro. Wani mutum a unguwarsu yana kiran ta, kuma yana tura mata saƙonni kowace rana cewa yana so su yi soyayya. Vanessa ba ta yarda masa ba. Sai mutumin ya soma fushi sosai, har da yi mata barazana. Ta ce: “Na ji tsoro sosai.” Me ya taimaka mata ta daina jin tsoro? Vanessa ta ɗauki wasu matakai don ta kāre kanta. Wani dattijo ya taimaka mata ta sanar da ꞌyan sanda. Ban da haka, ta yi tunani sosai a kan yadda Jehobah ya kāre bayinsa a dā. Vanessa ta ce: “Mutum na farko da na yi tunanin sa shi ne annabi Daniyel. Ko da yake bai yi laifi ba, an jefa shi a cikin ramin zakuna da suke jin yunwa. Duk da haka, Jehobah ya kāre shi. Sai na danƙa kome a hannun Jehobah, kuma na gaya masa ya taimaka mini don mutumin ya cire ni daga zuciyarsa. Bayan haka, na daina jin tsoro.”—Dan. 6:​12-22.

MENE NE JEHOBAH YAKE YI YANZU?

8. Wane tabbaci ne Dauda yake da shi? (Zabura 56:8)

8 Ko da yake ran Dauda yana cikin haɗari saꞌad da yake Gat, bai mai da hankali a kan abubuwan da za su sa ya ji tsoro ba. A maimakon haka, ya mai da hankali a kan abubuwan da Jehobah yake masa a lokacin. Dauda ya ga cewa Jehobah yana yi masa ja-goranci, yana kāre shi, kuma ya fahimci yadda yake ji. (Karanta Zabura 56:8.) Ƙari ga haka, Jehobah ya ba wa Dauda abokai masu aminci da suka ƙarfafa shi kuma suka taimaka masa. Wasu daga cikinsu su ne Jonathan da kuma Babban Firist Ahimelek. (1 Sam. 20:​41, 42; 21:​6, 8, 9) Kuma duk da cewa Sarki Saul yana so ya kashe shi, Dauda ya tsira. Ya kasance da tabbacin cewa Jehobah ya san matsalolin da yake fuskanta da irin damuwar da matsalolin suke jawo masa.

9. Mene ne Jehobah ya sani game da kowannenmu?

9 Idan kana fuskantar matsalar da take sa ka ji tsoro, ka tuna cewa Jehobah ya san abin da kake fuskanta da kuma yadda kake ji game da hakan. Alal misali, ba wulaƙancin da aka yi wa Israꞌilawa ne kawai Jehobah ya gani ba, amma ya ce ya “san dukan wahalarsu.” (Fit. 3:7) A wata waƙa da Dauda ya yi, ya ce Jehobah ya ‘ga wahalarsa,’ da ‘damuwar zuciyarsa.’ (Zab. 31:7) Kuma idan mutanensa suna shan wahala, ko da abin da suka yi ne ya jawo musu wahalar, yana ‘damun’ Jehobah. (Isha. 63:9) Don haka, idan kana jin tsoro, Jehobah ya san yadda kake ji kuma yana so ya taimaka maka ka daina jin tsoro.

10. Me ya tabbatar maka da cewa Jehobah ya damu da kai kuma zai taimaka maka ka jimre matsalar da kake fuskanta?

10 Idan ka shiga wani yanayi mai ban tsoro, mai yiwuwa ba za ka ga yadda Jehobah yake taimaka maka ba. Don haka, ka roƙe shi ya sa ka ga yadda yake taimaka maka. (2 Sar. 6:​15-17) Bayan haka, sai ka yi tunani ko akwai kalami ko wani jawabi da aka yi a taro da ya ƙarfafa ka. Akwai wani littafi ko bidiyo ko waƙarmu da ta ƙarfafa ka? Wani ya gaya maka wani abu ko ya nuna maka wani nassi da ya ƙarfafa ka? Idan muna cikin matsala, za mu iya manta da ƙaunar da ꞌyanꞌuwa suke yi mana da kuma yadda ƙarfafar da muke samu daga Kalmar Allah take taimaka mana. Amma waɗannan abubuwa masu daraja ne da Jehobah yake ba mu. (Isha. 65:13; Mar. 10:​29, 30) Suna nuna cewa Jehobah ya damu da kai sosai. (Isha. 49:​14-16) Kuma suna nuna cewa za ka iya dogara gare shi.

11. Me ya taimaka wa Aida ta daina jin tsoro?

11 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Aida da take zama a Sanagal ta lura da yadda Jehobah yake kula da ita saꞌad da take cikin wata matsala. Tun da ita ce ꞌyar fari, iyayenta sun so ta nemi aikin da zai riƙa ba ta kuɗi sosai don ta iya kula da su da kuma kanta. Amma da ta sauƙaƙa rayuwarta kuma ta zama majagaba, Aida ta soma fama da rashin kuɗi. Sai iyayenta sun yi fushi da ita, kuma sun yi mata baƙar magana. Ta ce: “Na ji tsoro don ina ganin ba zan iya kula da iyayena ba, kuma kowa zai tsane ni. Har ma na ɗora wa Jehobah laifi da ya bar abubuwan nan suka faru da ni.” Sai ta ji wani jawabi a taro. Ta ce: “Mai jawabin ya ambata cewa Jehobah ya san abin da yake sa mu ji tsoro ko mu damu. Shawarwarin da na samu daga wurin dattawa da kuma ꞌyanꞌuwa sun sa a-hankali-a-hankali na ga cewa Jehobah yana ƙauna ta. Yanzu idan na yi adduꞌa ga Jehobah, ina da tabbaci cewa zai amsa min, kuma ina samun kwanciyar hankali idan na ga yadda ya amsa adduꞌata.” A-kwana-a-tashi, Aida ta samu aikin da yake taimaka mata ta kula da kanta yayin da take hidimar majagaba da kuma taimaka wa iyayenta har ma da wasu mutane. Aida ta ce: “Na koyi cewa ya kamata in dogara ga Jehobah da dukan zuciyata. Yanzu bayan na yi adduꞌa, ba na jin tsoro kuma.”

MENE NE JEHOBAH ZAI YI MANA A NAN GABA?

12. Bisa ga Zabura 56:​9, wane tabbaci ne Dauda yake da shi?

12 Karanta Zabura 56:9. Wannan ayar ta ambaci wani abu kuma da ya taimaka wa Dauda ya daina jin tsoro. Ko da yake yana cikin haɗari, ya yi tunani a kan abin da Jehobah zai yi masa a nan gaba. Dauda ya san cewa Jehobah zai cece shi a lokacin da ya dace. Balle ma, Jehobah ya riga ya sanar cewa Dauda ne zai zama sarkin Israꞌila. (1 Sam. 16:​1, 13) A gun Dauda, duk abin da Jehobah ya ce zai yi, kamar ya riga ya faru ne.

13. Mene ne muke da tabbaci cewa Jehobah zai yi?

13 Mene ne Jehobah ya ce zai yi maka? Bai kamata mu ɗauka cewa Jehobah zai kāre mu daga dukan matsalolinmu ba. c Amma ko da mene ne kake fama da shi a yanzu, Jehobah zai kawar da shi a sabuwar duniya. (Isha. 25:​7-9) Mahaliccinmu mai iko ne, zai iya ta da matattu, ya warkar da mu kuma ya hallaka dukan masu gāba da mu.—1 Yoh. 4:4.

14. Mene ne za mu iya yin tunani a kai?

14 Idan kana jin tsoro, ka yi tunani a kan abin da Jehobah zai yi a nan gaba. Yaya za ka ji bayan an hallaka Shaiɗan da mugayen mutane, kuma masu adalci ne kawai a duniya? Yaya za ka ji a lokacin da za a kawar mana da ajizanci a-hankali-a-hankali? Wani gwaji da aka yi a taron yanki na 2014 ya nuna yadda za mu iya yin tunani mai zurfi a kan begenmu. A gwajin, wani mahaifi ya bayyana wa iyalinsa yadda kalaman da ke 2 Timoti 3:​1-5 za su kasance idan ana annabci ne game da Aljanna. Ya ce: ‘A sabuwar duniya, za a yi farin ciki sosai. Gama mutane za su zama masu son juna, masu son ibada, masu sanin kasawarsu, masu tawaliꞌu, masu yabon Allah, masu biyayya ga iyayensu, masu godiya, masu tsarki, masu ƙaunar iyalinsu sosai, masu gafartawa, masu yin maganganu masu kyau game da waɗansu. Masu kame kansu, masu tausayi, masu son nagarta, masu riƙon amana, masu hankali, masu sauƙi kai, masu son Allah fiye da jin daɗi, kuma suna da dangantaka mai kyau da Allah. Masu bauta wa Allah da gaske. Ka manne wa irin mutanen nan.’ Kana tattaunawa da iyalinka ko ꞌyanꞌuwa game da yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya?

15. Mene ne ya taimaka wa Tanja ta daina jin tsoro?

15 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tanja da ke zama a Arewacin Masedoniya ta yi tunani a kan abubuwan da za su faru a nan gaba. Da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, iyayenta ba su ji daɗi ba. Ta ce: “Wasu abubuwan da nake jin tsoro cewa za su faru, sun faru da gaske. Mahaifiyata takan yi min dūka bayan na dawo daga taro. Iyayena sun ma ce za su kashe ni idan na zama Mashaidiyar Jehobah.” A ƙarshe, sun kori Tanja daga gida. Mene ne ta yi? Ta ce: “Na mai da hankali a kan farin cikin da zan yi har abada idan na riƙe amincina. Na kuma yi tunani a kan yadda munanan abubuwa za su shuɗe, da yadda Jehobah zai ba ni lada a sabuwar duniya don abubuwan da na rasa a wannan zamani.” Tanja ta riƙe amincinta kuma da taimakon Jehobah ta samu wurin kwana. Yanzu, Tanja ta auri wani ɗanꞌuwa mai aminci kuma su biyun suna hidima ta cikakken lokaci da farin ciki.

KA ƘARA DOGARA GA JEHOBAH YANZU

16. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya idan abubuwan da suke Luka 21:​26-28 suka soma faruwa?

16 A lokacin ƙunci mai girma, mutane za su “suma don tsoro.” Amma mutanen Allah ba za su ji tsoro ba. Za mu kasance da ƙarfin zuciya. (Karanta Luka 21:​26-28.) Me ya sa ba za mu ji tsoro ba? Domin a lokacin, mun riga mun koyi yadda za mu dogara ga Jehobah. Tanja da muka ambata ɗazu ta ce abubuwan da suka faru da ita a dā, suna taimaka mata ta iya jimre matsalolin da take fuskanta. Ta ce: “Jehobah zai iya taimaka mana mu jimre kowace irin matsala kuma zai yi mana albarka. A wasu lokuta, muna iya gani kamar ꞌyan Adam suna da iko a kan kome. Amma gaskiyar ita ce, Jehobah ya fi su iko. Kuma ko da matsalar da muke fuskanta tana da wuya sosai, za ta ƙare wata rana.”

17. Ta yaya jigon shekara ta 2024 za ta taimaka mana? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

17 A yau, akwai abubuwa da yawa da za su iya sa mu ji tsoro. Amma kamar Dauda, kada mu bar tsoro ya hana mu yin abin da ya dace. Jigon shekararmu na 2024 ya nuna adduꞌar da Dauda ya yi ga Jehobah. Ya ce: “Duk lokacin da na ji tsoro, zan dogara gare ka.” (Zab. 56:3) Ga abin da wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce game da ayar nan. Mutumin ya ce: “Dauda bai ci-gaba da yin tunani a kan abubuwan da za su sa ya ji tsoro, ko a kan damuwoyinsa ba. A maimakon haka, ya mai da hankali ga Mai Cetonsa.” Ka yi tunani a kan jigon shekararmu a watanni masu zuwa, musamman ma saꞌad da kake cikin yanayi mai ban tsoro. Ka ɗauki lokaci don ka yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi a dā, da waɗanda yake yi yanzu, da waɗanda zai yi a nan gaba. Idan ka yi hakan, za ka zama kamar Dauda kuma ka ce: “Kai Allahna, a kanka nake dogara, ba zan ji tsoro ba.”—Zab. 56:4.

Balaꞌi ya shafi wata ꞌyarꞌuwa kuma tana yin tunani a kan jigon shekarar nan (Ka duba sakin layi na 17)

TA YAYA ZA KA DAINA JIN TSORO IDAN KANA TUNANI A KAN . . .

  • abubuwan da Jehobah ya yi a dā?

  • abubuwan da Jehobah yake yi yanzu?

  • abubuwan da Jehobah zai yi a nan gaba?

WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah

a Za ka iya samun labarai masu ban ƙarfafa a dandalin jw.org/ha. Don ka samu labaran nan, ka rubuta “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” ko kuma “Labarai” a inda aka ce “Bincika.” A manhajar JW Library® kuma, ka duba ƙarƙashin jerin talifofin nan, “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” ko kuma “Tarihin Shaidun Jehobah.”

b An canja wasu sunayen.

d BAYANI A KAN HOTO: Dauda ya yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka masa ya kashe wani beyar, da yadda ya taimaka masa ta wajen Ahimelek, da kuma yadda zai mai da shi sarki.

e BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da aka saka a kurkuku don imaninsa, yana tunanin yadda Jehobah ya taimaka masa ya daina shan sigari, da yadda yake ƙarfafa shi ta wurin saƙonnin da ꞌyanꞌuwa suka aika masa, da kuma yadda zai ba shi rai na har abada a Aljanna.