Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Shawara a kan Yin Nazari

Shawara a kan Yin Nazari

Ba sai mun je taro a Majamiꞌar Mulki ko manyan tarurruka ne kawai za mu bauta wa Jehobah ba. Za mu iya bauta masa mu kaɗai ko kuma tare da iyalinmu. Ga wasu abubuwa da za ka iya yi saꞌad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki kai kaɗai ko kuma tare da iyalinka:

  • Za ka iya shirya taro. Za ka kuma iya koyan rera waƙoƙin taron kuma ka taimaki kowa a iyalinka ya shirya abin da zai faɗa.

  • Za ka iya karanta wani labari daga Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, ka zana wani abu da ya faru a labarin da ka karanta ko ka rubuta darasin da ka koya.

  • Ka bincika wata adduꞌa da aka yi a Littafi Mai Tsarki, kuma ka yi tunani a kan yadda za ta taimaka maka ka inganta adduꞌoꞌin da kake yi.

  • Ka kalli ɗaya daga cikin bidiyoyinmu, saꞌan nan ka tattauna da wasu game da bidiyon ko kuma ka rubuta abin da ka koya.

  • Ka shirya yadda za ka yi waꞌazi. Za ka iya gwada yadda za ka yi waꞌazin tare da wani a iyalinka.

  • Ka lura da wani abu da Jehobah ya halitta kuma ka yi bimbini a kai, ko ka tattauna abin da halittar ta koya maka game da Jehobah. a

a Ka duba talifin nan “Ka Daɗa Koya Game da Jehobah ta Abubuwan da Ya Halitta” a Hasumiyar Tsaro ta Maris, 2023.