Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 14

Dattawa—Ku Ci-gaba da Yin Koyi da Manzo Bulus

Dattawa—Ku Ci-gaba da Yin Koyi da Manzo Bulus

“Ku bi misalina.”—1 KOR. 11:1.

WAƘA TA 99 Miliyoyin ’Yan’uwa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Ta yaya misalin manzo Bulus zai taimaka ma dattawa a yau?

 MANZO Bulus ya ƙaunaci ’yan’uwansa. Ya yi aiki da ƙwazo a madadin su. (A. M. 20:31) Saboda haka, su ma sun ƙaunaci Bulus sosai. Akwai lokacin da dattawan Afisa “suka fashe da kuka,” domin sun ji cewa ba za su sake ganin manzo Bulus ba. (A. M. 20:37) Haka ma, dattawanmu suna ƙaunar ’yan’uwansu kuma suna yin iya ƙoƙarinsu don su taimaka musu. (Filib. 2:16, 17) Amma a wasu lokuta, dattawanmu suna fuskantar ƙalubale. Mene ne zai taimaka musu su shawo kan ƙalubalen?

2 Dattawanmu masu ƙwazo za su iya yin koyi da Bulus. (1 Kor. 11:1) Manzo Bulus ba mala’ika ba ne. Shi ajizi ne, kuma a wasu lokuta yakan yi masa wuya ya yi abin da ya dace. (Rom. 7:18-20) Ƙari ga haka, ya jimre matsaloli da yawa. Amma Bulus bai daina taimaka ma ’yan’uwansa ba kuma bai daina farin ciki ba. Idan dattawa suka yi koyi da manzo Bulus, za su iya ci gaba da bauta ma Jehobah da farin ciki ko da suna fuskantar matsaloli. Bari mu ga yadda za su iya yin hakan.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin, kuma mene ne talifin zai taimaka mana mu yi?

3 A wannan talifin, za mu tattauna ƙalubale huɗu da dattawa suke fuskanta: (1) yadda za su sami lokacin yin wa’azi da kuma wasu ayyuka, (2) yadda za su riƙa kula da ’yan’uwa, (3) yadda za su kasance da ra’ayi mai kyau game da kasawarsu, (4) yadda za su yi aiki da ’yan’uwansu ajizai. Za mu tattauna yadda Bulus ya shawo kan kowane ɗaya daga cikin ƙalubalen nan da kuma yadda dattawa za su yi koyi da shi.

YADDA ZA KU SAMI LOKACIN YIN WA’AZI DA KUMA WASU AYYUKA

4. Me ya sa a wasu lokuta zai yi ma dattawa wuya su kasance a kan gaba a yin wa’azi?

4 Abin da ya sa hakan zai iya yi musu wuya. Dattawa suna da wasu ayyukan da suke yi ban da ja-goranci da suke ma ’yan’uwa a wa’azi. Alal misali, da yawa daga cikin su sukan gudanar da taron ikilisiya da kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Suna ba da jawabai, suna horar da bayi masu hidima kuma suna ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya a kullum. (1 Bit. 5:2) Wasu dattawa suna aiki a sashen gina Majami’un Mulki da kuma wasu gine-gine da ƙungiyarmu take amfani da su. Duk da haka, kamar yadda yake da kowane mai shela, wa’azin Mulkin Allah ne aiki mafi muhimmanci da dattawa suke yi.—Mat. 28:19, 20.

5. Wane misali mai kyau ne Bulus ya kafa mana a yin wa’azi?

5 Misalin Bulus. Abin da ke Filibiyawa 1:10 ne ya taimaka ma Bulus ya yi nasara inda ya gaya mana cewa: “Ku san abin da ya fi muhimmanci.” (New World Translation) Bulus ya bi shawararsa. An ba shi aikin yin wa’azi kuma ya yi shekaru da dama yana ɗaukan aikin a matsayin ɗaya daga cikin abubuwa da suka fi muhimmanci. Ya yi wa’azi a “fili, da kuma gida-gida.” (A. M. 20:20) Ya yi wa’azi a kowane lokaci, ba wasu ranaku kawai ba. Alal misali, sa’ad da yake jiran abokan hidimarsa a Atina, ya yi wa’azi ga wasu manyan mutane kuma wasun su sun saurare shi. (A. M. 17:16, 17, 34) Ko a lokacin da yake “kurkuku” ma, Bulus ya yi wa’azi ga waɗanda suka zo wurin sa.—Filib. 1:13, 14; A. M. 28:16-24.

6. Mene ne Bulus ya horar da wasu ’yan’uwa su yi?

6 Manzo Bulus ya yi amfani da lokacinsa da kyau. Yakan gayyaci wasu su bi shi zuwa wa’azi. Alal misali, a karo na farko da ya je wa’azi a ƙasashen waje, ya je tare da Yohanna wanda ake ce da shi Markus. A karo na biyu kuma ya je da Timoti. (A. M. 12:25; 16:1-4) Babu shakka, Bulus ya koya ma ’yan’uwan nan yadda za su tsara ikilisiya, da yadda za su ƙarfafa ’yan’uwa da kuma yadda za su iya yin koyarwa da kyau.—1 Kor. 4:17.

Ku yi koyi da Bulus ta wajen kasancewa a shirye ku yi wa’azi a kullum (Ka duba sakin layi na 7) *

7. Ta yaya dattawa za su bi gargaɗin da Bulus ya bayar a Afisawa 6:14, 15?

7 Darasi. Dattawa za su iya yin koyi da Bulus ta kasancewa a shirye su yi wa’azi a duk lokacin da suka sami dama, ba sai a lokacin da suke wa’azi gida-gida ba. (Karanta Afisawa 6:14, 15.) Alal misali, za su iya yin wa’azi sa’ad da suka je yin sayayya ko kuma sa’ad da suke wurin aiki. Ƙari ga haka, sa’ad da suke taimaka wajen gina wurin ibada, za su iya yin wa’azi ga mutanen da suke yankin ko kuma masu sayar da abubuwa. Kamar yadda manzo Bulus ya yi, dattawa ma za su iya horar da wasu har da bayi masu hidima sa’ad da suke wa’azi tare.

8. A wasu lokuta, mene ne dattijo zai bukaci ya yi?

8 Bai kamata dattawa su mai da hankali wajen yin ayyukan ikilisiya ko na da’ira har su kasa yin wa’azi ba. A wasu lokuta za su bukaci su ƙi karɓan ƙarin ayyuka. Bayan sun yi addu’a kuma sun yi tunani a kan batun, za su iya gano cewa karɓan ƙarin aiki zai hana su yin wasu ayyuka da suka fi muhimmanci. Ayyukan su ne gudanar da ibada ta iyali kowane mako da yin wa’azi da himma ko kuma koyar da yaransu yadda za su yi wa’azi. Yana yi ma wasu wuya su ƙi karɓan ƙarin aiki amma za su iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ya san yadda suke so su kula da dukan ayyukan da aka ba su da kyau.

YADDA ZA KU ZAMA MAKIYAYA MASU ƘAUNA

9. Wane ƙalubale ne dattawa da suke da ayyuka da yawa za su iya fuskanta?

9 Abin da ya sa hakan zai iya yi musu wuya. Bayin Jehobah suna fama da matsaloli da yawa. A waɗannan kwanakin ƙarshe, dukanmu muna bukatar ƙarfafa da taimako. Wasu ’yan’uwanmu za su bukaci taimako don su guji yin abin da bai dace ba. (1 Tas. 5:14) Gaskiyar ita ce, dattawa ba za su iya cire dukan matsaloli da bayin Allah suke fama da su ba. Duk da haka, Jehobah yana so dattawa su yi iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa kuma su kāre tumakinsa. Ta yaya dattawa da suke da ayyuka da yawa za su iya samun lokacin da za su taimaka ma ’yan’uwa?

Ku yaba ma ’yan’uwa kuma ku ƙarfafa su (Ka duba sakin layi na 10, 12) *

10. Bisa ga 1 Tasalonikawa 2:7, ta yaya Bulus ya kula da bayin Allah?

10 Misalin Bulus. Bulus yana shirye a koyaushe ya ƙarfafa da kuma yaba ma ’yan’uwansa. Zai dace dattawa su bi misalinsa ta wajen nuna wa ’yan’uwa ƙauna da alheri. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:7.) Bulus ya gaya ma ’yan’uwa cewa yana ƙaunar su kuma Jehobah ma yana ƙaunar su. (2 Kor. 2:4; Afis. 2:4, 5) Bulus ya ɗauke su a matsayin abokansa kuma ya yi cuɗanya da su. Ya nuna cewa ya yarda da su ta wajen gaya musu damuwoyinsa da kuma kasawarsa. (2 Kor. 7:5; 1 Tim. 1:15) Amma maimakon Bulus ya mai da hankali ga matsalolinsa, ya mai da hankali ga taimaka wa ’yan’uwansa.

11. Me ya sa Bulus ya gargaɗi ’yan’uwansa?

11 Akwai wasu lokuta da Bulus ya bukaci ya yi wa ’yan’uwansa gargaɗi. Amma bai taɓa yin hakan domin yana fushi da su ba. Ya gargaɗe su ne domin yana ƙaunar su kuma ya so ya kāre su daga matsaloli dabam-dabam. Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya sa gargaɗin ya kasance da sauƙin fahimta kuma ya so ’yan’uwan su bi gargaɗin. Alal misali, a wasiƙar da ya rubuta ma Korintiyawa, Bulus ya yi musu gargaɗi sosai. Bayan ya rubuta wasiƙar, sai ya tura Titus wurinsu. Bulus ya so ya san abin da suka yi bayan sun karanta wasiƙarsa. Ya yi farin ciki sosai da ya ji cewa sun bi gargaɗin da ya ba su.—2 Kor. 7:6, 7.

12. Ta yaya dattijo zai iya ƙarfafa ’yan’uwansa?

12 Darasi. Dattawa za su iya yin koyi da Bulus ta wajen yin cuɗanya da ’yan’uwa. Hanya ɗaya da za su iya yin hakan ita ce ta wurin zuwa taro da wuri don su iya tattauna da ’yan’uwa kafin taron. A wasu lokuta, ba sai sun faɗi abu mai yawa ko sun ɗauki lokaci sosai kafin su iya ƙarfafa ’yan’uwa ba. (Rom. 1:12; Afis. 5:16) Dattijo da ke koyi da manzo Bulus zai kuma yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa bangaskiyar ’yan’uwansa kuma ya tabbatar musu cewa Allah yana ƙaunar su. Ƙari ga haka, zai nuna wa ’yan’uwan cewa yana ƙaunar su, zai riƙa tattauna da su a kullum, kuma zai nemi damar yaba musu. Idan yana bukatar ya ba da gargaɗi, zai dace ya yi amfani da Kalmar Allah. Zai gaya musu asalin inda suke bukatar su yi gyara amma zai yi hakan cikin ƙauna.—Gal. 6:1.

YADDA ZA KU KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE GAME DA KASAWARKU

13. Ta yaya ajizancin dattijo zai iya shafansa?

13 Abin da ya sa hakan zai iya yi musu wuya. Dattawa ajizai ne. Su ma suna yin kuskure kamar kowa da kowa. (Rom. 3:23) A wasu lokuta, yana musu wuya su kasance da ra’ayin da ya dace game da kasawarsu. Wasu suna iya mai da hankali a kan kasawarsu sosai har su yi sanyin gwiwa. Wasu kuma sukan yi watsi da nasu kasawar har su ji kamar ba sa bukatar su yi gyara.

14. Bisa ga Filibiyawa 2:13, ta yaya sauƙin kai ya taimaka ma Bulus ya kasance da ra’ayi mai kyau game da kasawarsa?

14 Misalin Bulus. Bulus ya gane cewa ba zai iya shawo kan kasawarsa da kansa ba. Yana bukatar taimakon Jehobah. A dā, Bulus ya tsananta wa Kiristoci da ƙwazo sosai. Amma daga baya, ya gane cewa abin da yake yi bai dace ba, kuma ya yarda ya canja ra’ayinsa da kuma halinsa. (1 Tim. 1:12-16) Jehobah ya taimaka ma Bulus ya zama makiyayi mai ƙauna da sauƙin kai da kuma tausayi. Ya san cewa yana da kasawa sosai amma bai mai da hankali a kan kasawarsa ba. A maimakon haka, ya gaskata cewa Jehobah zai gafarta masa. (Rom. 7:21-25) Bai ɗauka cewa shi kamili ba ne. Amma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kasance da halayen da Jehobah yake so kuma ya dogara ga Jehobah ya taimaka masa ya cim ma hidimarsa.—1 Kor. 9:27; karanta Filibiyawa 2:13.

Ku yi iya ƙoƙarinku don ku iya shawo kan kasawarku (Ka duba sakin layi na 14-15) *

15. Ta yaya dattijo zai kasance da ra’ayin da ya dace game da kasawarsa?

15 Darasi. Dattawa ba kamilai ba ne. Amma Jehobah yana so su san cewa su ma suna da kasawa kuma su yi iya ƙoƙarinsu su kyautata halayensu. (Afis. 4:23, 24) Zai dace dattijo ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya san wurin da yake bukatar gyara. Idan ya yi hakan, Jehobah zai taimaka masa ya yi nasara.—Yak. 1:25.

YADDA ZA KU YI AIKI DA ’YAN’UWANKU AJIZAI

16. Mene ne zai iya faruwa idan dattijo ya riƙa mai da hankali a kan kasawar ’yan’uwansa?

16 Abin da ya sa hakan zai iya yi musu wuya. Dattawa za su iya sanin kasawar ’yan’uwansu a ikilisiya idan suna yawan aiki tare da su. Idan ba su yi hankali ba, za su iya yin fushi ko su daina tausaya ma ’yan’uwa ko kuma su riƙa shari’anta ’yan’uwansu. Bulus ya gargaɗi Kiristoci cewa Shaiɗan zai so su riƙa yin hakan.—2 Kor. 2:10, 11.

17. Yaya Bulus ya ɗauki ’yan’uwansa?

17 Misalin Bulus. Bulus ya kasance da ra’ayin da ya dace game da ’yan’uwansa. A kowane lokaci, yana gaskata cewa ’yan’uwansa suna so su yi abu mai kyau. Ya san kasawarsu domin a wasu lokuta, abubuwan da suka yi yakan sa shi baƙin ciki. Amma Bulus ya san cewa idan mutum ya yi kuskure, hakan ba ya nufin cewa shi mugun mutum ne. Ya ƙaunaci ’yan’uwansa kuma ya mai da hankali ga halayensu masu kyau. Idan ya ga cewa yana yi ma ’yan’uwansa wuya su yi abu mai kyau, yakan gaya wa kansa cewa suna so su yi abu mai kyau amma suna bukatar taimako ne don su yi shi.

18. Wane darasi ne ka koya daga yadda Bulus ya bi da matsalar da ke tsakanin Yudiya da Sintiki? (Filibiyawa 4:1-3)

18 Ka yi la’akari da yadda Bulus ya yi ƙoƙarin sasanta ’yan’uwa mata biyu a ikilisiyar da ke Filibi. (Karanta Filibiyawa 4:1-3.) Da alama Yudiya da Sintiki sun ɗan sami matsala da juna. Bulus bai shari’anta su ba amma ya mai da hankali ga halayensu masu kyau. ’Yan’uwa mata biyun sun daɗe suna bauta ma Jehobah da aminci. Bulus ya san cewa Jehobah yana ƙaunar su. Ya san cewa za su iya sasanta da juna, shi ya sa ya ƙarfafa su su yi hakan. Da yake Bulus yana mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwansa, ya ci gaba da farin ciki kuma ya kasance da dangantaka mai kyau da ’yan’uwa a Filibi.

Ku guji shari’anta ’yan’uwanku (Ka duba sakin layi na 19) *

19. (a) Me zai taimaka ma dattawa su kasance da ra’ayin da ya dace game da ’yan’uwansu? (b) Mene ne ka koya daga hoton dattijon da yake share Majami’ar Mulki?

19 Darasi. Dattawa, ku mai da hankali ga halaye masu kyau da ’yan’uwanku suke da su. Dukansu ajizai ne amma kowannensu yana da halaye masu kyau. (Filib. 2:3) Gaskiya ne cewa a wasu lokuta, dattawa za su bukaci su yi ma wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa gyara. Amma kamar manzo Bulus, ba zai dace dattawa su mai da hankali ga halaye marasa kyau na mutumin ba. A maimakon haka, zai fi dacewa su mai da hankali ga yadda ɗan’uwan yake ƙaunar Jehobah da yadda yake jimrewa da kuma tabbacin da ya nuna cewa zai iya gyara halayensa. Hakan zai sa ’yan’uwansu su san cewa ana ƙaunar su a ikilisiya.

KU CI GABA DA YIN KOYI DA MANZO BULUS

20. Ta yaya dattawa za su iya ci gaba da amfana daga misalin Bulus?

20 Dattawa, za ku amfana idan kun ci gaba da yin nazarin misalin Bulus. Alal misali, a littafin nan Watch Tower Publications Index, za ku iya neman jigon nan “Paul,” a ƙarƙashinsa kuma, za ku ga ƙaramin jigon nan “example for elders.” Yayin da kuke nazarin bayanai da ke wurin, ku tambaye kanku, ‘Ta yaya misalin Bulus zai taimaka mini in ci gaba da yin farin ciki yayin da nake cim ma aikina a matsayin dattijo?’

21. Wane tabbaci ne dattawa za su iya kasancewa da shi?

21 Dattawa, ku tuna cewa Jehobah bai bukace ku ku zama kamiltattu ba, amma yana so ku zama masu aminci. (1 Kor. 4:2) Jehobah ya yi farin ciki domin yadda Bulus ya yi aiki da ƙwazo da kuma aminci. Ku ma za ku iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana farin ciki domin hidimar da kuke yi masa. Jehobah ba zai taɓa manta da “ayyukanku da kuka yi ba, da ƙaunar da kuka nuna masa sa’ad da kuke taimakon tsarkaka ba, kamar yadda kuke yi har yanzu.”—Ibran. 6:10.

WAƘA TA 87 Ku Zo Mu Sami Ƙarfafa!

^ sakin layi na 5 Muna godiya sosai domin yadda dattawa suke aiki da ƙwazo don su taimaka mana. A wannan talifin, za mu tattauna ƙalubale huɗu da dattawa suke fuskanta. Za mu kuma tattauna yadda misalin manzo Bulus zai taimaka wa dattawa su shawo kan waɗannan ƙalubalen. Talifin nan zai taimaka ma dukanmu mu riƙa tausaya ma dattawa. Ƙari ga haka, zai sa mu riƙa ƙaunar su da kuma goya musu baya.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana yin wa’azi ga abokin aikinsa sa’ad da suke barin wurin aiki.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana yawan wāre kansa. Wani dattijo yana ƙarfafa shi ya riƙa yin cuɗanya da mutane.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana ba da shawara ga wani ɗan’uwa da yake ɓata rai don abin da aka yi masa.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa ya ba da kansa don ya taimaka da yin shara, amma waya ta raba hankalinsa. Ko da yake wani dattijo yana ganin sa, bai yi masa magana ba.